Connect with us

LABARAI

Sojoji Sun Samu Nasarar Kama ‘Yan Bindiga A Sakkwato

Published

on

Rundunar sojin Nijeriya sun samu nasarar kama mutum uku wadanda ake zargi da hatsabiban ‘yan bindiga ne. Kakakin rundunar sojin, Kanal Sagir Musa shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana daya da suna Malam Ibrahim.

Ya ce; wadanda aka kama din sun yi fice ne wajen yiwa ‘yan bindigar leken asiri, kuma suna karbar kudaden fansa a madadin ‘yan bindigar.

Ya kara da cewa; shi kuwa dayan mai suna Ashiru Goni, yak ware ne a kai wa ‘yan bindigar kayayyakin bukatun da suka so, inda yake kai musu a duk inda suke a cikin Sakkwato da wajen Sakkwato.
Kanal Musa ya ce na ukun mai suna Mamman Taratse,  ya kware ne wajen siyarwa da ‘yan bindigar dabbobin da suke sato wa a kasuwanni daban-daban na ciki da wajen jihar.

Sannan ya kara da cewa har wala yau, sojojin sun yi nasarar kai wani samame a kauyen Magira inda suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar inda suka kashe da dama, yayin da wadansu suka gudu da raunuka a jikinsu, sai dai ya ce; soja daya ya rasa ransa a wannan samamen da suka kai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: