Connect with us

LABARAI

Yaki Da ‘Yan Bindiga A Zamfara: Gwamna Matawalle Ya Nemi Hadin Kan Kafafen Watsa Labarai

Published

on

Gwanma Bello Matawalle na Zamfara ya nemi hadin kan kafafen watsa labarai wajen salon rahotannin da suke kawo wa dangane da yakin da ake yi da ‘yan bindiga a jihar. Inda ya bukaci da su rika kawo rahotannin nasarorin da jami’an tsaro ke samu ne domin karfafa jami’an.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Alhaji Zailani Bappa, mashawarci na musamman ga gwamnan kan harkokin kafafen watsa labarai da bangaren sadarwa, inda ya tabbatar da cewa gwamnan ya ce irin wadannan rahotanni ne kawai za su karfafa jami’an tsaron.

Ya kara da cewa; rahotanni dangane da nasarorin ne kawai zai kara wa al’umma fatan musamman wadanda suke fuskantar matsalar tsaron a jihar.

Gwamnan ya jinjinawa irin kokarin da jami’an tsaro ke yi wajen yaki da ‘yan bindigar a jihar, inda ya tabbatarwa da al’umma cewa ba zai gajiya ba wajen ganin ya samar da zaman lafiya a jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: