Connect with us

MAKALAR YAU

Kokarin Hana Bara: Mu Ma Almajirai Ne..!

Published

on

Maganar hana almajiranci da gwamnatin tarayya ta bullo da shi ya ja hankali kwarai da gaske musamman a wannan lokaci da ake kallon gwamnatin na da sa hannu wajan haifar da wannan mummunar dabi’a ta bara a arewacin Najeriya.

Haka kuma wannan batun kowa da yadda yake kallonsa a na shi bangaran wasu na ganin cewa ba hana bara ne abinda ya kamata gwamnati ta yi ba, a’a kamata ya yi ta fara da dalilan da suka haifar da bara sannan  sai a dauki matakin da ya kamata.

Kazalika wasu na ganin bara ta zama ruwan dare gana duniya yana da wahalar gaske a iya hanata a wannan lokaci na siyasa da aka ce kowa yana da ‘yanci kuma ma me yasa tun farko ba a yi wani yunkuri na hana bara ba sai yanzu.?

Sannan kuma akwai wani abu da ake hange game da wannan lamari inda a mafi yawan lokuta za a ga cewa wasu kasashe ne suke da wata manufa game da Najeriya da kuma ‘yan Najeriya sai kawai su bullo da wata manufa ta hanyar gwamnatin Najeriya wanda ta kuma kamar…

Masana sun yi magana gane da sha’anin bara musamman a arewacin Najeriya inda nan abin ya fi kazanta, musamman yadda ake amfani da ita wajan turzarta addini da kuma kabila musamman ta Malam Bahaushe.

Sun bayyana cewa yin bara ga wanda baya da shi ba aibu bane amma wani lokaci mai shi din ne za a ganshi yana bara, sannan idan aka yi bincike za a gano babu dalilin da yasa zai yi bara, ma’ana neman taimaka kamar yadda kowa yasan ana yi.

Yadda Malam Bahaushe ya maida abin wata babbar sana’a ne shi ne ke da ciwo, da kuma yadda suke dagewa sai sun yi bara sai dai ko me zai faru ya faru, sannan rasa kima da mutunci da shiga kaskanci da ake yi wanda bara ce ke haifar da shi, abin ya zama abin kyama a cikin kowace irin al’umma.

Kadda a manta ba wai Bahaushe kadai yake bara ba, kuma bara ba abu ne mai kyau ba a kowane addini amma ana duba daliln da suke sa a yi bara wanda ada ba a yin ta kamar yadda ake yin ta yanzu.

Haka kuma bara a wannan lokaci ta fara zama abinda ta zama domin kowa zai iya zama shaida cewa mutumin da ka san shi ada baya da dabi’ar yin bara yanzu yana iya yi maka bara, kuma da gaske yake baya da shi.

Abinda masana ke cewa shi ne, menene dalilin da yasa mutune suka zabi wannan dabi’a wanda ada yana da wahala ka ga mutanen  kirki cikinta amma yanzu ta koma kowa kana iya gani yana bara.

A nata banagaran gwamnatin tarayya da take barazanar hana bara wannan wani abu ne ta bullo da shi wanda daman ta saba, idan jama’a hankalinsu yafi akan wani abu sai abiyo masu ta bayan gida da wata sabuwa domin su kara shiga hankalinsu.

Ko shakka babu wannan maganar ta hana bara wata boyayyar manufa ce daga gwamnatin tarayya kai tsayre zuwa ga takakawa da gwamnati ta haifar da yanayin da ya jefa su cikin harkar bara kuma yanzu ake son yi masu hisabi da hana ta bayan sun rasa abinda za su sanya a bakin salatinsu saboda matsi irin da wannan gwamnati.

Muna kallon yadda abubuwa suka koma a lokacin wannan gwamnati wanda yanzu talakawa ne kadai suke dandana kunarsu, sune ya kamata ace suna amfana da wannan gwamnati amma akasin haka, yanzu sun koma manyan jami’an mabarata kuma ana kallo sai dai ba hanlin yin magana.

Abinda muke cewa shi ne, ko an ki ko an so wannan gwamntin ta taimaka wajan samar da dabi’ar bara da almajiranci a wannan asa musamman a yankin arewa wanda yake da dadaddan tarihin.

Idan gwamnatin Najeriya zata nemi yadda zata yi maganin matsalar tsarin da ta addabin wannan kasa musamman yankin arewa ta nema amma maganar hana almajirancin ba ita ce hanya da za a yi amfani da ita wajan maganin wannan matsala ba.

Saboda haka matsalar tsaro daban maganar almajirancin daban, magana bara daban, a wannan lokacin duk wanda yasa abinda ake nufi da almajiranci ana nufi karatun allo ko karatun alkur’ani wanda yake da matukar mahimmanci a wannan  lokaci da aka samu karanci mahaddata alkur’ani a yankin arewa.

Yakin da Boko Haram ta yi a yankin Barno ya haifar da karancin mahaddata alkur’ani sannan sauran wadanda suka rage yanzu ake son yi amfani da wata dama wanda za a kara jefa masu san karatu da almajiranci cikin wani mawuyacin haki.

Ina tabbacin kowa yana sani babu wanda ya isa ya hana almajirancin a wanna kasa da maka samun kanmu wai ita Najeriya, sannnan sai dai ayi duk barzanar da za a yi amma dai wanna al’amari yana nan kuma zai cigaba da wakana.

Abinda kawai muke jira shi ne gwamnati ta sake yin tunanin game da wannan batu na hana bara da almajiranci ta yi sabon tunani game da yadda zata yi maganin matsalar tsaro amma ta kiyayi maganar hana almajiranci a wannan kasa.

Al’umma na sane da irin mugun nufin wannan gwamnati akan talakawa ta yadda kullin sai ta bullo masu da wata sabuwa fitina da sunan gyara, an maida su kamar wasu shanu sai dai a kada su yadda ake so a lokaicn da ake so.

Maganar bara, ana iya yin wani tsari da zai magance matsala da halin kunshin da jama’a ke ciki wanda yana daya daga cikin dalilan da ke sa bara a wannan lokaci.

Ana fama da yunwa da fatara da rashin kudi sannan ka ce kadda ayi bara ko kuma tana da alaka da rashin tsaro wannan magana kowa ya gane abinda ake nufi da ita, duk wanda baya san arewa sai kawai ya duba ya ga da me zai jefi arewa ko kuma ya kawo mata matsala ta hanyar shugawabanin da ba su da kishin arewa.

A wannan lokacin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta zama sanadiyar kowa ya zama mabaraci idan baka bara irin ta kaskanci wanda kowa ya baya goyon bayanta to kila kana yin mai tsafta wanda zaka samu wani ya taimaka maka saboda halin da ake ciki da kunci.

Mu ‘yan Najeriya musamman ‘yan arewa almajirai ne, tunda mafiyawan mu ba mu da abinda za mu ci sati guda, kullin sai mun fita nema wanda haka abu ne mai wahala a wannan zamani da aka hana shigowa da shinkafa ta arewa sai ta kudu kuma gashi mun kasa noma wanda za a ci a cikin kasar nan, sannan matsalar  tsaro da gwamnati ta kasa yin maganinta na neman zama wani dalili na kara takurawa talakawan arewa.

Duk wanda ya ce sai cigaba da matsawa talakawa lamba to akwai kyakkyawan misalin a cikin wannan duniya mai cike da abin al’ajabi, masu halin mugunta da keta wajan nunawa dan adam ba a bakin komi yake ba, kuma idan aka saurara za aga abinda zai biyo bayan tozarta almajirai da ake yi.

Babu shakka a wannan lokaci da muka samu kanmu na zama mabaratan zamani, dole ne ‘yan siyasa da masu mulki su tabbatar sun ga bayanmu domin gani suke kamar mune matsalar duniya a wajansu sun manta cewa ba a dade ba suka zo suna barar kuri’armu ba da sunan neman mulki, amma yanzu sun samu nasara shi ne suka juyo kan bayin Allah.

Sannan idan har gwamnatin tarayya bata janye wannan muguwar aniya ta hana almajiranci ba, bayan an karar da manyan alaramumin mu da ke yanki arewa masu gabas inda ake yaki da masu tada kayar baya, to abubuwan jarabawa da iftila’I yanzu aka fara ganinsu a wannan kasa.

Sannan muna bada shawara duk da cewa ba za a dauka, idan ma gwamnati za ta sake karatun ta nutsu game da matsalar tsaro, to wuri bai kure ba, amma wannan magana, idan a ka matsa to karshen wanda ya zo da ita ba zai kyau ba.

Idan Allah Ya kaimu sati mai zuwa zan cigaba da wannan rubutu inda zai maida hankali akan almajiran da suka yi nasara a rayuwa ta dalilin almajiranci da kuma wadanda suka lalace amma ba su ne matsalar tsaron Najeriya ba, duk wanda ya bada wannan shawara kalubalansa a rayuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: