Connect with us

LABARAI

NDLEA Ta Cafke ‘Yan Kwaya 186 A Jigawa

Published

on

Hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Jigawa tace ta yi nasarar cafke masu ta’ammali da miyagun kwayoyi 186 cikin watanni shida a jihar.

Shugabar hukumar ta NDLEA reshen jihar Jigawa Barrister Obi Josephine Ruth ce ta bayyana haka ga manema labarai a jiya a ofishinsu dake birnin Dutse.

‎Ruth ta ce cikin ‘yan kwar su kimanin 186 mutum 182 sun kasance maza da kuma mata guda hudu.

‎Ta karada cewa, ‘yankwayan an kama bisa aikata laifin amfani da miyagun kwayoyi daban-daban, tabar wiwi, magungunan Kodin, Tiramadol da dai sauran miyagun kwayoyi.

Shugabar ta kuma ce, hukumar tasu ta NDLEA ta yi nasarar kama‎ miyagun kwayoyi wadanda yawansu ya kai nauyin 61.24 kgm daga watan na Janairun 2019 zuwa yanzu.

Sannan ta karada cewa, hukumar zata cigaba da yin iya bakin kokarinta wajen dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar ta Jigawa.

Zuwa yanzu dai tace an tabbatar da laifukan mutane 22 yadda kuma sauran mutane 108 suka dukufa yi musu nasiha kan hadarin dake tattare da mu’amula da miyagun kwayoyin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: