Connect with us

ADABI

Tarin Kurakurai A Littafin Halayyar Zamani (1)

Published

on

Littafin ‘Halayyar Zamani’ daya ne daga cikin jerin littafan Adabin Kasuwar Kano, mai dauke da shafuka 148, wanda su ka hadu su ka ja zaren labarin. Fa’iza S. Muhammad ce ta kaga labarin, inda madaba’ar Megacraft wadda ba a bayyana adireshinta ba ita ta wallafa shi, farashin da a ke fansar shi a kasuwar littafai naira dari uku ne kacal.

Bayan fansar wannan littafin a kasuwa abin da zai biyo baya kuwa ai sharhin bayan karatu ne, a yunkurin ya Allah ko dai yabo ko suka mai ma’ana a kan yadda manazarci ya ga littafin, ya kuma kalle shi, ko ba komai domin marubuciyar ta san ko wace irin alkibla za ta dosa a rubutunta na gaba. Don haka ba luguden littafin wannan marubucin zai yi ba, kamar yadda kuma ba baje shi zai yi a faifai ba, domin fitar da tsaki da tsakuwa tare da cin tsutsa. A’a, ba kuma manufar wannan sharhin ba ne a yi wa littafin nazarin kokwanto.

Dalili kuwa  wannan shi ne littafin ta na farko da ta wallafa, don haka tana bukatar uzuri. Sai dai ta lura ba ta makara ba duk da kasancewar ta sabuwar yankan rake ce a duniyar rubutu da marubuta.

A kan wannan mai sharhin zai dai yi kokarin fahimtar da ita cewar Borno gabas ta ke. Bari mu yi tattaki mu leka mu gani mene ne na ci, da na zubarwa da za a tsinta a ciki!

Halayyar Zamani, labari ne mai fuska daya, inda marubuciyar ta ke kokarin bayar da labarin wata mata mai suna Fatima wadda ita ce babbar jarumar labarin, wacce ta fuskanci kalubalen rayuwa tun kafin ta fado duniya har zuwa haihuwarta, wato ta fuskanci tsangwama da mummunar kiyayya da tsana wurin kishiyar mahaifiyarta  wato Inna Jummai. Babban kalubalen da Fatima ta fuskanta a rayuwarta shi ne yadda Danliti ya ci zarafinta ta hanyar yi mata fyade.

A sakamakon haka ne kuma Fatima ta samu damar yin kyakkyawar rayuwa daga baya, har ta kai ga ta samu ingantaccen ilimi da murza sitiyarin manyan motoci sakamakon haduwarta da wani bawan Allah da ya zama da ita tamkar diyar shi a Kaduna, haka Fatima ta zama jinin wannan bawan Allah, duk abinda ya yi wa ‘ya’yan shi su Zainab da Fatima da Rukayya ita ma an yi mata.

Da karshe dai Fatima wacce ta mori miji mai kyautata mata da sauke hakkin iyali, ya gina mata babban asibiti da kuma bata goyon baya na kafa kungiyar mata masu rajin kare hakkin matan da ake yi wa fyade.

Bari mu tsaya a nan sai mu tsakuro tarin kura-kuran da sabuwar marubuciyar ta yi zubar-gadon su wanda zamu iya cewa sun zarce lissafin Ras-Kwana.

Tun da farko marubuciyar littafin ba ta yi amfani da salon sarrafa harshe ba yayin rubuta littafin musamman wajen yin karin magana ko tagwayen kalmomi ko amfani da siffatau kai tsaye (Personification) ko siffatau mai-kama (simile) ta saki rubutun sakaka, babu gishiri bare magi, haka ya ke a salamce.

Kwata-kwata marubuciyar ba ta yi amfani da dokar bin ka’idojin rubutu ba, babu alamar wakafi ko tsayawa ko alamar tambaya bare kuma uwa uba alamar motsin rai, duk da akwai wurare da dama da ya kamata marubuciyar littafin ta yi amfani da su. Wani abin lura kuma, tun daga farkon littafin har zuwa karshe babu inda marubuciyar ta yi amfani da alamar nuna maganar wani.

Marubuciyar littafin ba ta yi amfani da dabarun jan ra’ayin mai karatu da wasa kwakwalwarsa ba wajen yin waiwaye (Flash back ko Foreshadowing) don rike mai karatu ya ji littafin bai gundurarwa.

Duk da marubuciyar ta yi amfani da jigo daya ne tal, amma ta kasa dora tsinin alkalami ta gina labari mai sarkakiya da kawo maslaha a karshe kamar dai yadda ta kama kame-kame sai dai a ce wane dan gidan wane ya yi wa wance fyade ko an ji labarin an kama Ilan mai unguwa ko mun dawo gaisar da ‘yar ajinmu an yi mata fyade shi ke nan.

Jigon da marubuciyar ta dauka jigo ne mai matukar muhimmanci, amma kuma alkalamin marubuciyar ya yi gardamar rubuta abubuwan da za su gamsar da mai karatu ya tabbatar da littafi ne ya ke karantawa ba jagwalgolo ba. Haka nan idan za a auna littafin a sikeli ne ko kusa ba zai samu ko kashi biyar cikin dari ba. Ni dai da na karanta wannan littafi ciki da wajensa, zan iya kiran wannan aikin da aikin baban giwa, saboda tamkar bata itace ne don dahuwar kaho.

A shafi na 13 Marubuciyar ta rubuta Makarfi karamar hukumar Kaduna, sai kuma a shafi na 14 marubuciyar ta ce Ilan mai unguwa ya yi wa yara fyade har wasu sun mutu. A haka marubuciyar ta kasa kawo hobbasar da mutanen unguwa suke yi tare da hukuma don ganin an hukunta shi amma yana ta yawon shi yana shan iskar Subhana duk a cikin garin Makarfi da suka kwankwadi ilimin zamani da kuma wayewa.

A shafi na 16 da 17 da 18 marubuciyar ta yi tashin goron zabi ko tsallen-badake wajen zura labarin iyayenta da kuma na inna Jummai da yaron ta Danliti, sannan ta saki labarin ta koma fadakar da mai karatu ba wacce ake bai wa labarin ba.

Allah Sarki rubutaccen  Adabin Hausawa yana cikin tsaka-mai-wuya! Idan dai har marubuciyar littafin Halayyar Zamani za ta kasa rubuta farkon sunan Fatima da Maryam da Rukayya da Zariya da Makarfi da Kaduna da Zainab da Mustafa tare da Yasmin da babban baki, ai ya kamata sunan Mai Duka a rubuta shi da babban baki, haka marubuciyar ta dinga rubuta sunan Allah tun daga farkon littafin har zuwa karshen shi.

Haka kuma a shafi na 41 marubuciyar ta nuna cewa Fatima ‘yar shekara bakwai ba ta san mece ce mutuwa ba, shin a wane karni? A shafi na 51 marubuciyar ta ce “A ka yi assembly aka fito da hedimasta daga shi sai gajeren wando yana sussunkuyar da kai….”  A wane gari ko a wace kasa hakan ke faruwa? Sannan a shafi na 52 ma ta bada labarin cewa jarumar littafin wadda ba a cika bayyana sunanta ba, ta ce hedimastansu ya yi niyyar yi mata fyade amma ta janyo kwalba ta buga mishi. Anya irin biyayya da girmamawa zai sa karamar yarinya ‘yar shekara sha biyu ta yi dubarar hakan? Tambaya ce ga marubuciya.

Duk dai bamu bar shafi na 52 ba, inda marubuciyar ta ce “Idan kuma mutuwa ki ka yi sai ya dauki gawar ya kai ki kogi….”  Ma’ana idan ya gama amfani da karamar yarinya har ta kai ga mutuwa sai ya dauki gawar ya kai kogi. To wace hanya yake bi wajen fita da gawar daga ofishin shi ba tare da an gan shi ba? Gaskiya da sake wai an bai wa mai kaza kai, sannan kuma duk a cikin birnin Zazzau mai dadadden tarihi wajen ilimi da wayewar kai hakan ta faru.

A shafi na 56 marubuciyar ta yi tuya ta manta da albasa, domin har iyayen Fatima da Rukayya wadanda suka samu cikakkiyar tarbiyya suka gama ja musu kunne da nasiha lokacin da aka kai su makarantar kwana mai karatu bai ji inda aka musu hudubar cewa su kula da addini sosai ba a matsayinsu musulmai.

A shafi na 63 marubuciyar ta nuna yadda Inna Jummai take dora yaronta Danliti kan dabi’ar ya illata Fatima diyar mijinta, ya gurbata rayuwarta ta hanyar yi mata fyade. Wannan manazarcin zai mika tambayar shi ga sabuwar marubuciyar Halayyar Zamani, shin wannan Adabin Malam Bahaushe ne ko adabin Yahudawa? A kasar Hausa uwa da kanta ta ingiza yaronta ya aikata fyade?

A shafi na 71 kuma cikin littafi na biyu marubuciyar ta kasa yin amfani da hukuma ko jami’an tsaro wajen dasa zargi da bincikar Danliti da Rukayya kawar Fatima don a rikitar da kwakwalwar mai karatu, kawai sai ta bar su salin-alin suka kama harkokinsu a gari ba wanda ke zargin su.

Bugu da kari a cikin shafi na 83 mawallafiyar ta yi kememe ta kasa nuna kuskure da sakacin iyayen da har za su bayar da diyarsu ‘yar shekara uku kacal wani tsoho mai shekara fiye da hamsin ya tafi da ita har gidan shi sannan ya yi mata fyade har  ta bakunci kiyama.

Duk a cikin littafi na biyu shafi na 84 marubuciyar ta bayyana cewa tsohon da ya yi wa ‘yar shekara uku fyade da yake kora bayani a gaban alkali dalilin da ya sa ya aikata hakan sai ya ce sharrin shedan ne, har wani dan sanda yana buga mai kulki. Tambaya ga mawallafiya, da ma dan sanda ko wani jami’i yana da hurumin yin wani hukunci lokacin da alkali ke shari’a?

Wani kuskure da mawallafiyar ta tafka a shafi na 92 shi ne yadda ta ke bayar da labarin lokacin da Fatima za ta rubuta jarabawar shiga jami’a wato JAMB, zabinta na farko ABU inda take son karatun lauya, sai zabi na biyu kuma jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto inda a nan kuma take son karantar fannin likitanci, sa’ilin da ta samu sakamakon jarabawa har kusan dari biyu da talatin, hakan ya sa ta samu jami’ar Danfodiyo.

Tambaya ga marubuciyar ita ce shin wane fanni jarumar littafin ta karanta lokacin da take makarantar Sakandaren kwana da ke Soba, kuma yaushe hukumar JAMB ta fara amincewa da wannan tsari irin na Fatima?

Saboda ya haramta duk jami’o’in kasar nan su bata takardar shiga jami’a a dokar hukumar JAMB. Idan kuma muka waiwaya baya cikin shafi na  62 an bayyana Rukayya kawar Fatima ta karanta fannin kasuwanci ne da masana’antu a sakandare din ta, me ya sa a cikin littafi na biyu marubuciyar ta dora ta a matsayin malamar asibiti?

Zan ci gaba in sha Allah.

Sani Ahmad Giwa,

[email protected]

www.mysanigiwa.blogspot.com

08169701410
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: