Connect with us

KIWON LAFIYA

Hukumar Kula Da Asibitoci Masu Zaman Kansu Ta Rufe 14 A Kalaba

Published

on

Hukumar kulawa da yadda aka tafiyar da asibitoci wadanda suke zaman kansu a jihar Kuros Riba (Kalaba) ta rufe asibitoci 14 a fadin  jihar, saboda basu tafiyar da harkokin su kamar yadda ya kamata, ga shi kuma babu kwararrun ma’aikata, kamar dai yadda wakilin namu ya bayyana.

Shugaban Hukumar Dokta Norbert Mogar shine wanda ya bayyana hakan ranar Litinin a Kalaba.

Ya bayyana cewar an rufe asibitocin tsakanin shekarun 2017 da kuma 2019 ne.

Mogar ya bayyana su asibitocin da aka rufe sun hada da Destiny Medical Consult in Calabar, Holy Trinity Clinic da kuma kulawa da masu haihuwa a karamar Hukumar Bekwarra da kuma Dibine Fabour Clinic  da kuma asibitin haihuwa wanda yake Ugaga a Yala.

Kamar yadda  ya bayyana an yi shi wannan binciken ne babu kama hannun yaro, saboda a samu kawo gyara ta banagren yadda ake tafiyar da asibitoci masu zaman kansu a jihar, musamman ma a wuraren da suke kauyuka.

Ya bayyana cewar an daukin shi matakin ne an ga kuma amfanin yin shi, saboda kuwa an samu raguwar yadda mutane suke mutuwa, saboda kawai yadda akle tafiyar da harkokin basu dace ba.

An dai kaddamar da dokar kulawa da asibitoci masu zaman kan su ne a shekarar 2007.

Lokacin da yake bayyana samun cigaba da Hukumar ta samu cikin shekaru uku, Mogar ya bayyana cewar na dauki shi matakin ne, saboda a samu sauki wajen yadda za a rika kulawa dasu.

Ya bayyana cewar ita Hukumar har ila yau samar da ani tsari na kulawa da su asibitoci masu zaman kansu a jihar.

Hakanan ma ita Hukumar ta gano wasu asibitocin da suke tafiyar da ayyukan su ba tare da gwamnati ta basu lasisi na izinin yin hakan  ba, ya yin da su irin wadannan asibitocin an yi masu rajista suna kuma biyan kudaden haraji ga gwamnati.

Kamar dai yadda ya kara jaddadaw yanzu ita Hukumar ta kulla abokantaka mai karfi da adanda suke da rua da tsaki ta bangaren lafiya  ajihar, da kuma jami’an tsaro saboda a samu yadda za  a rika tilasta amfani da dokoki wanda gwmnati ta kafa.

“Ta hanyar rufe su asibitocin masu zaman kansu wadanda suke tafiyar da harkokin su ba kamar yadda dokoki suk shimfida ba, yanzu an samu damar su al’aumma mazauna jihar sun samu damar amfani da asibitocin gwamnati.

“Bugu da kari kuma kamar yadda ya ci gaba da bayani sun samu damar dawo da tari mai kyau, gas u asibitoci masu zaman kansu, saboda su masu tafiyar da ayyukan yanzu maida hankalin su wajen gudanar da ayyuka kamar yadda ya dace, saboda kwa ana ziyarta su akai-akai saboda a sa idanu wajen sanin yadda suke tafiyar da nasu harkokin.

Mogar ya gode ma gwamna Ben  na jihar saboda nada shi mukamin da ya yi,  da kuma sauran mambobin na Hukumar, saboda su yi aiki a karkashin mulkin shi.

Ya yi kira cewar yayin da shi gamnan zai rushe gwamnatin shi, saboda shirya ma ma yadda za atafiyar da ata sabuwa, ya kamata a sake kafa ita Hukumar saboda ta ci gaba yin ayyukan ta na yaki miyagun mutane, wadanda basu iya tafiyar d ayyukan kulawa da lafiyar al’umma ba, saboda a samu damar ceto rayuwar mutane a jihar,

Dakga karshe kuma ya mika godiyar shi ga ma’aikatar lafiya ta jihar da kuma kungiyar Likitoci ta kasa raehsn jihar ta Kuros Ribas, saboda taimakon da suka ba ita a jihar. Hukumar wajen yadda ta tafiyar da ayyukan ta, inda kuma ya kara cewar hakan ya taimaka masu ba kadan ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: