Connect with us

JAKAR MAGORI

Kotu Ta Yanke Wa Kukun Da Ya Kashe Maigidansa Hukuncin Daurin Rai-Da-Rai

Published

on

A ranar Talata ce, babbar kotun Jihar Legas wacce ta ke da zama a Igbosere, ta yanke wa kuku Sunday Anani, hukuncin daurin rai da rai a gidan yari, bisa laifin kashe mai gidansa shugaban kamfanin Credit Switch Ltd, Cif Opeyemi Bademosi.

Alkali mai shari’a Mobolanle Okikiolu-Ighile, ya samu Anani da laifin da a ke tuhumar sa da shi na kisan kai, bayan da ya samu kwararan hujjoji. Gwanatin Jihar Legas ta gurfanar da Anani dan shekara 22, a gaban kotu ne, bisa laifin da a ke tuhumar sa guda 2 na laifin kisan kai da kuma na fashi da makami.

Da farko dai, Anani ya musanta laifin da a ke tuhumar sa da shi, amma daga baya ya amsa laifin sa. Ya amsa laifin sa ne ta bakin lauyarsa mai suna, Misis Aderenra Adeyemi. Don haka, ya amsa laifin kashe Cif Bademosi, a gidansa da ke Ikoyi cikin Jihar Legas, lokacin da ya yi yunkurin yi masa fashi. Ya tabbatar da cewa, shi ya kulle na’urar talabijin, domin ya samu nasarar tsare wa daga wurin da ya aikata laifin. Ya roki kotu a kan kar a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar ratayewa idan an same shi da laifi.

Kafin a yanke masa hukuncin dai, sai da kotu ta tambayi lauyansa a kan ya na da wata hujja wanda zai iya kare kansa.

Adeyemi ta ce, “wanda a ke tuhuma matashi ne, kuma ya yi ladamar a kan abinda ya aikata. Wannan shi ne karo na farko da a ka samu hujjan ya taba aikata irin wannan laifi. “Babbar abinda mu ke rokon alkali dai shi ne, ya yanke masa hukuncin zama a gidan yari na wasu shekaru. “Idan alkali mai shari’a ya amince da hujjojin da mu ka bai wa kotu, to za mu amince da duk wani hukunci da ya yanke.”

Kwamishinan shari’a ta Jihar Legas, Misis Titilayo Shitta-Bey, ta yi hamayya da bukatar lauya mai kare wanda a ke tuhuma. Shitta-Bey ta ce, “mu na kira da kotu ta yanke masa hukunci mai tsauri a kan laifin da a ke tuhumar sa da shi na kisan kai.”

Ta bayyana cewa, akwai abubuwan da su ka mamaye wannan shari’a, kamar na rashin yarda. “Wanda a ke tuhuma an dauke shi aiki a gidan mai gidansa a matsayin kuku, inda a ka yarda da shi dari bisa dari. “Kwai bayan kwanaki uku da daukar sa aiki a gidan mai gidansa, sai wanda a ke tuhumaya ya kashe mai gidansa wanda ya ba shi sabon rayuwa, ya yanke masa duk wani jin dade nasa da na matarsa da kuma na yaransa. “A yanke masa hukunci mai tsauri, domin ya zama izina ga wadanda su ke sha’awar kashe masu gidansu.”

Bayan da Okikiolu-Ighile ta kammala bayar da shawarwari ga shari’ar Anani.

Alkali mai shari’a ya ce, “abun takaici ne matashi irin wannan ya aikata wannan laifi. Mene za ka samu riba a kan aikata wannan laifi? ina tambayan ka. “Abun takaici ne wannan matashi da iyalan Bademosi su ka dauke shi aiki a matsayin mai dafa abinci, kuma ya aikata irin wannan mummunar aika-aika. “Karin takaici shi ne, yadda wanda a ke tuhuma ya je gidan bada niyyar aika ba, ya shiga gidan ne da niyyar sata da kuma na kisan kai.

“Wanda a ke tuhuma ya amsa laifin sa na kisan kai, wanda iyalan mamacin ba su yi tsammanin hakan ba. Bayan hujjoji da a ka gabatar a gaban kotu, ni alkalin wannan kotu, “na yanke wa Sunday Adefonou Anani hukuncin daurin rai da rai a gidan yari. “Wannan hukunci zai fara aiki ne tun daga yau, 25 ga watan Yunin shekarar 2019.”

Tun da farko dai, lauya mai gabatar da kara ya bayyana wa kotu cewa, wanda a ke zargi ya aikata wannan laifin na kisan kai ne, a ranar 31 ga watan Oktobar shekarar 2018, a rukunin gidajen Park Biew Estate da ke Ikoyi cikin Jihar Legas. Ya kara da cewa, wanda a ke tuhuma ya caka wa mamacin mai shekaru 67 da haihuwa, wuka tare da sace masa wasu kayayyaki, wannan laifi dai ya saba wa sashe na 223 da 297 na dokar manyan laifuka ta Jihar Legas na shekarar 2015. Haka kuma, lauyan ya gabatar da shaidu, ciki har da matar mamacin Ebunola Bademosi, wanda ta bayyana yadda ta dawo ta sami mai gidanta kwance cikin jini.

Lokacin da a ke gudanar da shari’ar, wanda a ke tuhuma ya amince da laifin sa ne cikin wata wasika wanda ta fito daga hannun lauyansa a ranar 20 ga watan Mayu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: