Connect with us

LABARAI

Kullum Ina Ganawa Da Mutane 100 Zuwa 200 – Malam Chindo

Published

on

Wani Malami Mai suna Malam Umaru Chindo da ke zaune a kauyen Kwararo a cikin gundumar Tiggi da ke karamar hukumar mulki ta Augie a jihar Kebbi ya bayyana cewa a kullum yana ganawa da mutane dari zuwa dari biyu wadand ke zuwa wajensa neman waraka.

Malam Umaru Chindo ya yi wannan bayanin ne ranar Labara a gidansa da ke kauyen na Kwararo lokacinda wakilin LEADERSHIP A YAU ya ziyarce shi.

Ya bayyana cewa daman can shi ba wannan sana’a ce sana’ar sa ba, shi manomi ne, Ya hadu da wadannan iskokin ne kimanin shekara daya da rabi ne sanadiyyar kamunsa da mayu suka yi.

Wadannan iskokin suka zo suka shiga jikinsa suka kori mayun kuma suka yi masa isharar cewa za su taimaka masa wajen warkarda mutanen da Jinnu suka shafa, daga nan ne sai ya soma bayarda maganin Jinnu kuma ya ce daga wancan lokacin zuwa yau ba zai iya tuna adadin mutanen da yi wa magani ba saboda tun lokacin da wannan lamarin ya bayyana a kullum mutane sai kwararowa suke yi daga ko Ina kusa da nesa.

Malam Umaru Chindo ya kuma kara da cewa shi baya jinga da kowa illa dai duk abinda aka ba shi zai karba saboda wannan shine sharadinda suka gindaya masa kuma ya amince da haka saboda su dai wadannan Jinnu dai musulmi ne da suka yi zamani da Annabi Suleman saboda haka sun tabbatar masa da kada ya yi jinga da kowa su kuma za su taimaka masa har na wani lokaci mai tsawo.

Ya ce a farkon wannan lamarin duk abinda baiwa mutum zai iya zama magani a wajensa saboda sau da yawa ya kan debo kasa ya saka a kwarya ua zuba ruwa ya yi addu’a ya baiwa mutum ya sha a take zai warke amma ya zuwa yanzu mutum ko da a kwance ya ke idan dai matsalar Jinnu ce ko kuma wani rashin lafiya mai alaka da Jinnu to ya kan dafa jikin marashi lafiyar sai ya kira Jinnun kuma zai zo.

Malam Umaru Chindo ce daga cikin abubuwan al’ajabinda suka faru da shi sun hada da daukarsa da Jinnu din suka yi zuwa wadansu sassa na cikin Nijeriya da kuma wadansu kasashe da suka hada da Saudiyya inda ya ce har ya taba Sallar Asuba a Masallacin Madina kuma suka zagaya da shi cikin Birnin Madina sannan suka mayarda shi gida kuma a cikin dare daya, bayan wannan kuma sun Sha daukarsa zuwa garuruwan Jinnu na musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Wata Hajiya da ba ta so a ambaci sunanta ba da wakilinmu ya ci karo da ita kan hanyar kauyen ta bayyana cewa itama ta zo ne daga jihar Zamfara a sanadiyyar samun labarinsa wajen wani mutum da ya yi wa magani a Sakwkwato.

Wannan Malamin dai a gidansa mutane ba su tsinkewa saboda ala-kulli-halin wadansu suna shiga wadansu kuma suna fita daya nesa da kusa don neman waraka dangane da matsalolin su dabam-daban.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: