Connect with us

ADABI

Abin Da Ya Fara Ba Ni Tsoro A Babbar Makarantar Da Na Shiga –Na’ema

Published

on

Da zarar mutum ya kammala makarantar sakandare matukar yana da sha’awar cigaba da karatu dokin shiga babbar makaranta zai lullube shi. Sai dai, bakuwarmu ta wannan makon, duk da wannan dokin, akwai abin da ya zo mata a ba-zata kuma ya far aba ta tsoro. Ku karanta hirar har karshe don jin wane abu ne wannan da kuma sauran wasu bayanan.

Masu karatu za su so su ji cikakken sunan ki…

Sunana Ni’ema Dalhat Inuwa

Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitac-cen tarihin ki?

Da farko dai kamar yadda na fada miki sunana a baya Na’ema sannan nayi makarantar Allo ta Malam Tosaro sannan na cigaba da karatu na na Islamiyya nayi makarantar tahfizul kur’an wato Kunti sannan na yi makarantar firamare, sannan na cigaba da karatun sakandare a makarantar sakandare ta Hasiya Bayaro, na yi mikamin monita, sannan na cigaba da karatu a makarantar Legal, yanzu haka ina koyarwa na gwaji (teaching practice) da yake ina NCE 3 ina karantar fannin social studies dama duk wannan bayan na yi saukar Alkur’ani a Islamiyya da kuma allo.

Kafin ki kammala makarantar Sakandare, me kike da burin karanta?

Ina so na karanci economic (fannin tattalin arziki).

Kasan cewar ko wanne dalibi nada nasa burin wajen shiga wata makaranta ta daban, shin bayan kin kammala makarantar Sakandare dinki, wacce makaranta kike da sha’awar cigaba a cikinta?

Legal da kuma Jami’ar Northwest

Mu dan koma baya kadan me yasa kike son karantar economics?

Saboda tun a secondary ina matukar gane shi Sannan ina son subject din

Idan muka koma kan neman ‘admission’ wace irin gwagwarmaya kika sha wajen ganin kin samu, ko kuwa ba ki sha wata wahala ba?

Gaskiya na sha wuya amma ba da yawa ba saboda da akwai wani mijin ‘yar’uwata lecturer ne, ya taimaka min matuka da gaske. Gaskiya ban sha wata wahala ba sabida shi

Na ji a baya kin ce Legal kike, me kike karanta shin kin samu abin da kike so ko kuwa ya abin yake?

Gaskiya ban samu ba saboda English economics na cike

Ya kika ji a zuciyarki lokacin da kika rasa samun cikar burinki?

Wallahi ban ji dadi ba amma sai mamana ta ce shi ne alkhairi, ni daman kuma Allah na bar wa zabin, gashi kuma ya zama alkhairi

Haka ne! Da suwa kika fara haduwa a farkon shigarki makarantar, kuma mece ce silar haduwar taku?

Na hadu da wata kawata Me suna Hafsat, Na hadu da ita tun a gurin JAMB. A lokacin ban santa ba

A farkon da kika fara zuwa aji ko za ki iya tuna kusa da wadda kika fara zama ko kuwa da ita Hafsan kuka zauna?

Da wata memuna

Ya darasin ranar ya kasance?

Wallahi ban wani gane ba sosai. Se da na dawo gida yayata ta sake taimaka min

Me ya fi baki wahala cikin darasin ranar har kika kasa ganewa?

Darasin Psychology (Kimiyyar Sanin Halayyar Dan Adam)

Ya gwagwarmayar zuwa makarantar ta kasance?

Wallahi Alhamdulillahi, saboda mamana tana iya kokarinta haka ma Abbah, ya tsaya tsayin daka a kan karatuna matuka da gaske, babu abin da zan ce musu sai godiya.

Ko akwai wani abu da ya fara baki tsoro a makarantar gaba da sakandare?

Abin da ya fara bani tsoro shi ne a lokacin na shiga da sa’a da kuma farin jinin kawaye, to daga nan kuma daman ina da kokari dai-dai gwargwado gaskiya sabida haka na fara samun matsala gurin abokai da kawaye saboda hassada da ake mun, to gaskiya na ji tsoron lamarin.

Ya batun Jarrabawa fa, shin kin taba fuskantar wata matsala?

Gaskiya a’a, ina samun nasara sosai dan a baya farkon shigata ban samun makin da nake samu a yanzu ba, kin ga kuwa dole na yi godiya ga Allah

Haka ne, wacce daliba ce ko wanne dalibi ne ya fi birge ki kuma me ya sa?

Hafsat tana birge ni sosai, kawata ce ta amana, saboda tana da kokari da sanin ya kamata, da kuma Rukayya

A malamai fa, wanne malami ne ya fi birgeki kuma me ya sa?

Malamin issues and problems (Darasin Nazarin Batutuwa Da Matsaloli) da kuma citizenship (Nazari kan Kasa da ‘Ya’yanta) na SOS, gaskiya suna birge ni, sun iya koyarwa matuka da gaske yadda za ka iya fahimta.

Wadanne sabbin abubuwa kika ci karo da su tun daga lokacin da kika cike form har zuwa kammala rajistar shiga makarantar gaba da sakandare?

Gaskiya sabon abin da na gani ya kuma ba ni wuya wajen yi min signing (sa hannu a takarda) da kuma lokacin da nake lecture ta yamma, ga rana ga wuya haka dai har na saba.

Ya za ki bambanta karatun sakandare da na gaba da sakandare?

Gaskiya akwai bambanci iri-iri daga yanayin girman makarantar da kuma yawan dalibai ga canje-canje courses (kwasa-kwasai) sannan gaskiya rayuwar gaba da sakandare rayuwa ce ta ‘yanci, ba kamar sakandare ba saboda ita sakandare za ki ga rufe gate (kofar shiga da fita ) ake saboda kar wani ya shiga ko ‘student’ su fita, amma Jami’a a bude take ba ma sai an ce ka zauna ba. Sannan karatun jami’a ya fi wuya akan na sakandare gaskiya. Saboda shi cewa ake ka yi,  jami’a kuwa ba sai an ce ba da kanka za ka yi kuma sannan za ki dada ganin rayuwa da iya zama da mutane.

Wasu maza sukan ce ba za su auri macen da ta wuce makarantar gaba da sakandare ba, me za ki ce a kan hakan?

Gaskiya ni a ganina, in suka yi haka to gaskiya suna yiwa jama’a wani irin kallo. Saboda in dai mutum lalatacce ne to ko ba a jama’a ba zai lalace.

Wasu matan ana cewa idan za su je (jami’a) suna tafiya da wata boyayyiyar shiga ta daban da zarar sun bar gidansu sun isa makaranta sai su canja, ya zancen yake shin ana samu ko kuwa kage ne ake yi kawai?

A’a ba na ce ba’a samu ba, amma mu a Legal ba a fiya samu ba saboda in ka shigo da wata shigar ma ba za a barka ka shiga ba sai dai ka shigo ta baya.

Kenan in na fahimce ki kina so ki ce ana samu amma ba sosai ba?

E, ana samu amma kadan gaskiya.

Ya za ki fada wa masu karatu amfanin cigaban karatun ‘ya mace?

Cigaban karatun ‘ya mace yana da matuakar anfani a ko ina ko da ba ta yin aiki za ta taimaki kanta da kuma ‘ya’yanta, sannan kuma za ta bambanta da wanda ya yi karatu iya sakandare. Kuma za ta dada sanin amfanin Ilimi.

Gaskiya ne, idan yau aka ce yarinyarki ta gama sakandare, shin za ki iya barinta ta cigaba?

E, zan barta, saboda na san amfanin shi don ta temaki kanta da kuma al umma.

Da kyau! Mu koma kan sha’anin soyayya, ko akwai wanda ya kwanta miki a zuciya cikin makarantar da har kika Fara soyayya da shi?

Hmmm a’a, sai dai akwai masu cewa suna sona

Kenan duk cikinsu babu wanda kika amsawa?

E.

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga babbar makaran?

Shawarata ita ce su dage da karatu su sa a ransu karatu suka je ba wasa ba.

Haka ne, mene ne burinki na karshe?

Ina so na shiga kungiyar kare hakkin mata, shi ne babban burina kuma Ina fatan hakan

Me ya sa kike son shiga kungiyar?

Saboda yadda ake yi wa mata abin ba na jin dadinsa matuka da gaske.

Allah ya cika miki burinki. Me za ki ce wa makaranta wannan shafi na Duniyar Makarantu?

Amin. Ina godiya, sai dai San barka ga shafin Allah ya dada daukaka.

Amin, me za ki ce wa masu karatun ita kanta jaridar LEADERSHIP A YAU JUMA’A?

Su cigaba da ba ta gudunmawa wajen sayen abun da ta fito da shi.

Muna godiya Malama Ni’ema

Ni ma n agode matuka da gaske.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: