Connect with us

SIYASA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hana Almajiranci

Published

on

Gwamnatin jihar Nasarawa ta daura damarar kawar da tsarin almajiranci a fadin jihar baki daya. Gwamnatin ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da manema labarai bayan taron da ya shafi bangaren tsaro a shekaran jiya Alhamis.

Gwamnati ta ce  duk da cewa tsarin almajiranci tsarice da ya shafe sama da shekara dari uku ana gudanar da shi a jihar amma yanzu lokaci ya sauya da za a rika barin yara suna gararanba a kan tituna da sunan almajiranci ba.

Saboda haka za ta bada kai da kungiyar Jama’atul nasaru- Islam wajen sauya tsarin almajiranci a jihar.inji Sarkin Keffi Alhaji Cindo Ya Musa.

Da yake jawabi Kwamishinan yan sandan jihar Nasarawa Mista Bola Lange ya ce; wanan zaman ya shafi harkokin tsarone saboda yadda yanzu jihar take fuskantar harkokin Ta’addanci da rigingimun kabilanci masamman na Manoma da makiyaya.

Ya kara da cewa Jami’an tsaro sun hada karfi da karfe wajen kawo zaman lafiya a jihar Nasarawa. Ya ce ; za su hada karfi da karfe tare da masarautun gargajiya wajen magance harkan ta’addanci a jihar.

Saboda jihar tana makwafta da jihohin da ake fama da rigingimu kamar jihar Benuwai da Taraba da Kogi da Filato dama jihar Kaduna.

Shi ma a nasa jawabin Sarkin Lafiya  Alhaji  Sidi Dauda Bage  ya kara da cewa, Sarakunan jihar za su ba da hadin kai ga Jami’an tsaro domin tabbatar da cikaken zaman lafiya a jihar.

Akwai hanyoyin da za mu bi wajen zakulu duk wani mara gaskiya da yardar Allah sai mun tabbatar da an samu zaman lafiya a ko’ina cikin jihar Nasarawa

Shugaban karamar hukumar Lafiya wanda ya yi magana a madadin , Ciyamomin kananan hukumomi jihar. Ya ce, za mu bi hanyar da za a bi wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Ya ce; za su samarwa Makiyaya matsugunai na dindindin saboda su rika gudanar da kiwon dabbobi , suma manoma su tsaya a matsugunanasu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: