Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Kotu Ta Tsare Wanda Ya Kashe Uwar Dakinsa Da Mahaifiyarta A Legas

Published

on

Wata kotun majistire da ke jihar Legas ta garkame wani yaron gida, Joseph Ogbu, wanda ake zarginsa da kashe uwar dakinsa, Oreoluwa John, da mahaifiyarta Adejoke John, yar shekara 89 a gidansu da ke a jihar Legas a ranar Alhamis da ta wuce.

Alkaliyar, Olanike Olagbende ta sa a tasare wanda ake zargin, Ogbu Joseph, a gidan kaso har zuwa lokacin da ma’aikatar shari’ah ta ba da shawarar yadda za a yi da shi, ta kuma dage sauraron karar zuwa 30 ga watan Yuli 2019 don sake bayyana a gabanta. Alkaliyar ta bada umurnin tsare Ogbu bayan da ‘yan sanda su ka roki hakan.

Idan za a iya tunawa, majiyarmu ta ruwaito cewa Joseph Ogbu, wani yaron gida ne dan asalin jihar Binuwai, ya kashe uwar dakinsa da mahaifiyarta bayan kwana daya da daukarsa aiki a gidansu da ke No. 4 layin Ogunlana da ke Surulere jihar Legas.

A lokacin da ‘yan sanda suka kama Joseph, ya bayyana cewa uwar dakin tasa ta bukace shi da ya share gida da dare, shi kuma ya ce mata dare ya yi, ta bari zai share da safe, wanda hakan ya sa rigima ta barke a tsakaninsu, daga bisani shi kuma ya fusata ya dauki wuka ya caka mata. Ya bayyana cewa ba shi ya kashe mahaifiyar uwar dakin tasa ba, ya ce ita da kanta ta hadiyi zuciya ta mutu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: