Connect with us

ADABI

Sha’awar Karatu Da Rubutu Ya Sa Ni Tsunduma Cikin Rubuta Littattafan Hausa – Zainab Chibado

Published

on

Gabatarwa

Assalamu Alaikum waraha matullah, muna wa bakuwarmu maraba da ziyartarmu a wannan shafi na duniyar marubuta

Wa’alaikumussalam’warahmatullah,

Da farko za mu so masu karatu su ji sunanki da kuma takaitaccen tarihin bakuwar tamu?

Da farko dai sunana Zainab Muhammad wadda aka fi sani da Chubado Muhammad a bangaren rubutu, ni haifaffiyar jihar kaduna ce amma kuma girman garin kano,

A kano na yi karatun islamiyya  da firamare har zuwa sakandire dina.

Ya aka yi kika tsinci kanki a harkan rubuce-rubuce?

Na kasance mai matukar sha’awar rubuce-rubuce da kuma karatun littattafan Hausa,  shi ya sa na samu kaina a cikin harkar rubutu.

Za ki kai shekara nawa da fara rubutu?

Kimanin shekara hudu ke nan da farawa ta.

Daga fara rubutun ki zuwa yanzu kin rubuta littafai kamar guda nawa?

Littattafai hudu na rubuta a tsawon wadannan shekarun, akwai

1 A’ISHATU (CHIBADO)

2 AMINTACCIYA CE

3 KADDARATA

4 KI YARDA DA NI

Sai kuma, BAFULATANA wanda nake rubutawa a yanzu.

Wane littafi kika fara rubutuwa a cikin wadannan littattafan?

A’ISHATU (CHUBADO) shi ne littafin da na fara rubutawa.

A dankule wane sako wannan littafi ke dauke da shi?

Labari ne da yake nuni da illar cin amana da kuma yaudara.

A cikin littattafanki wane ya fi burge ki, ma’ana wanne ne bakandamiyarki? Kuma wanne ya fi ba ki wahala yayin rubuta shi kuma me ya fi ba ki wahala?

Gaskiya a cikinsu na fi son Chubado, kuma na fi jinsa a raina fiye da sauran.

Sannan kuma na sha wahala sosai wurin rubuta shi saboda ban saba yin rubutu ba a lokacin.

Wadanne irin nasarori kika samu ta hanyar rubutu, haka wasu kalubalen kika taba fuskanta wanda ba za ki taba mantawa da shi ba, daga wajen marubuta har ma da masu karatu?

Nasarori kam Alhamdulillahi, na same su ba kadan ba, musamman a lokacin da nake rubuta Amintacciya ce, sai dai kawai in ce Alhamdulillahi kawai. Su ma kalubale kam akwai su ba za a rasa ba, tunda komai mutum zai yi baya rasa irin wadan nan abubuwan musamman ma harka ta jama’a irin tamu, wasu lokutan kam dole ne ka fuskanci kalubale ta kowane fanni.

Mene ne burinki a nan gaba dangane da rubutunki?

Burina shi ne in zama marubuciyar da duk duniya za a santa, sannan kuma a yi alfahari da ita, a bangaren ci gaban addini da kuma rayuwar al’umma da dai sauransu.

Ko za ki iya tuna littafin da kika fara karantawa a rayuwarki? Da Kuma sunan marubuciyar?

Littafin da na fara karantawa a rayuwata shi ne, Rintsi da tsanani mallakar Abdul’azeez madakin gini

Wane/wace marubuciya ce ta fi burge ki, har kike so kike burin kwaikwayon irin rayuwar shi/ta?

Marubuciyar  da ta fi burge ni ita ce Halima Kurminmashi.

Marubuciyar kuma da nake kwaikwayon rayuwarta kuma ita ce Chubado Muhammad

Me kika fi kauna a rayuwa, ko in ce mai ya fi burge ki?

Abin da na fi kauna a rayuwata shi ne Muhammadur rasulillah(S.A.W)

Sai kuma mamana da babana.

Me kika fi tsana?

Karya da kuma yaudara a rayuwa.

Wane kalar abinci kika fi so? Abin sha da kuma kaya?

Ina son tuwon shinkafa da miyar taushe da kuma zogale.

Abin sha kuma na fi son zobo. Kayan sa wa kuma na fi son jallabiya baka.

Da wane lokaci kika fi jin dadin yin rubutu?

Na fi jin dadin rubutu a lokacin da na tashi daga bacci.

Wane kira za ki yi wa marubuta har ma da masu karatu?

Kiran da zan yi ga marubuta shi ne mu ji tsoron Allah mu dinga rubuta abin da ya dace a cikin littattafan mu. Domin mu sani ilimin da Allah ya ba mu na rubutu, amana ce, wadda za a tambaye mu rana-gobe, saboda haka idan ka yi da kyau za ka ga da kyau, idan kuma ba ka yi da kyau ban an ma mutum zai gani, don haka ne ma masu hikimar magana ke cewa, “Abin da ka shuka shi za ka girba” domin haka nake kira ga marubutanmu su shuka alheri, domin su girbi alheri. Kuma ya kamata marubuta su sani abin da ka rubuta fa yana nan tsawon lokaci, duk lokacin da aka dauko shi za a ganshi ko bayan ba ka. Sannan kuma mu sani cewa, duk abin ka raubuta za ka bar tarihi ga na baya, saboda haka yana da kyau mu bar kyakkyawan tarihi ga na bayanmu, yadda za su yi alfahari da mu a matsayin iyayensu ko kuma yayyaunsu.     

Ga masu karatu su ma su ji tsoron Allah  su dinga amfani da fadakarwar da ke cikin littafi, sabda ba wai don nishadi kawai ake karanta lttafi ba, akwai darusssa masu yawa da ke kunshe a cikin littafin, saboda haka ya kamata makaranta su lura da wadannan darassa kuma su ci moriyarsu ta hanyar amfani da su.

Me za ki iya cewa game da maida littafai na kudi da wasu marubutan online ke yi?

Eh, to a gaskiya ni a ganina kuma a nawa ra’ayin sai nake gani duk abin da za ka fadakar da al’umma bai kamata a ce an mai da shi na kudi ba, amma suna da damar yin hakan tunda basirarsu ce, kuma rubutun su ne, amma kuma sai nake ganin da za su yi hakuri da batun kudin tabbas Allah zai biya su da sakamako na Alheri, wanda kuam ya fi kudi.

Wace ce Tauraruwarki cikin marubuta, mawallafa ko na online?

Taurarona shi ne Abdul’azeez sani madakin gini. A duniyar marubuta online kuma tauraruwata ita ce  Sadiya sidi Sa’id, ita ce tauraruwata. Alhamdu lillahi

Bakuwar mu muna godiya da kika samu lokacin amsa goron gayyatarmu. Allah ya kara daukaka da basira.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: