Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 15 A Zamfara

Published

on

Rundunar sojojin “Operation Hadarin Daji” sun samu nasarar halaka ‘ya bindiga goma sha biyar da suka addabi al’umma a gundumar Dansadau da ke jihar Zamfara. Wannan nasarar da sojojin suka samu ta halaka ‘yan bindigar bayan rundunar sojojin ta sanar da cewa ta kashe ‘yan bindiga ashirin da tara a wata arangama da suka yi da ‘yan bindigar a Moriki ranar Alhamis din da ta gabata.

Rundunar sojin ta shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a jiya Juma’a, a wata takarda wadda ke dauke da sa hannun mukaddashin jami’in yada labarai na rindinar, Laftanar Ayobami Oni-Orisan.

Ya ce, rundunar sajan ta dirarwa ‘yan bindigar a sansaninsu da ke dajin Madada da ke gundumar Dansadau kauyen Magami da ke karamar hukumar  Maru cikin jihar ta Zamfara.

Maimagana da yawun rundunar sojin ya ce, sojojin sun kutsa cikin dajin, ina suka yi wa ‘yan bindigar dirar mikiya, inda suak ci karfinsu wasu kuma suka gudu da raunuka a jikinsu. Lokacin wannan gumurzun sojojin sun kashe ‘yan bindiga goma sha biyar, inda suka tarwatsa  maboyarsu.

Duk da haka sun ce, rundunar sojan sun rasa mutum daya daga cikinsu da kuma dan sa-kai mutum daya wanda aka ji masa mummunan rauni. Oni-Orisan ya ce, sojojin za su ci gaba kokarin yakar ‘yan bindigar har sai sun kawo karshensu. Ya ce dajin Madada, daji ne day a shahara wajen samun mafakar ‘yan ta’adda. Ya ce, ranar 26 Yuni, 2019, rundunar ta kama wasu mutum biyu a Bagega da ke kai wa ‘yan bindigar labarin shirin da rundunar ke yi na kai wa ‘yan bindigar hari.  Ha kuma ya ci gaba da cewa, sojojin sun kwato shanu dari da ‘yan bindagar suka sace a kauyen Wanke da Kanoma da ke karamar hukumar Maru . Haka kuma rundunar da aka kai Farun sun gano shanu goma sha hudu a dajin Tungar Hako wadanda ‘yan bindigar suka gudu suka bar su. Saboda haka sai kwamandan rundunar sojojin, Manjo Janar Jide Ogunlade ya bukaci al’ummar yankin das u taimakawa rundunar wajen sanar musu da muhimman bayanan da za su taimaka wajen samun nasarar yakar ‘yan bindigar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: