Connect with us

SIYASA

Tsofaffin ‘ Yan Majalisar Wakilai Da Marigayi Abacha Ya Rusa Sun Koka Kan Hakkokinsu

Published

on

Tsofaffin yan Majalisar da aka zaba a cikin inuwar jam’iyyu daban-daban a  shekarar 1992 a lokacin  Shugaban kasa na mulkin soji na Ibrahim Badamasi Babangida sun koka akan kin biyan su hakokin su.

Mai magana da yawun yan Majalisar su 539 Honorabul Isah Ibn Muhammad a wani gangami da suka gudanar a karkashin inuwar kungiyar su yi na tunawa da 12 ga ranar watan Yuni da Gwamnatin Tarayya mai ci ta mayar a matsayin ranar Dimokiradiyya ya ce, “  Muna murna da wannan ranar domin ranar muce, kuma mun aka yi yi wa wannan bikin ba kowa ba, muna kuma taya Gwamnatin Tarayya da Shugaban kasa Muhammdu Buhari murnar ranar da kuma mayar da sanya ranar a matsayin ranar mulkin dimokiradiyya a kasar nan.”

Ya ci gaba da cewa, a shekarar 1992 al’ummomin sun zabe mu a matsayin yan majalisar wakilai ta tarayya har kuma mun care madafun iko har ta kai ga mun fara yi wa kasa wikilci kafin daga baya gwamnatin mulkin soji ta marigayi Shugaban kasa Sani Abacha ya rusa mu.”

A cewar Isah, “ A waccan shekarar, mun tsaya takara mun kuma lashe zaben kuma shine zaben da ya fi ko wanne zabe sahihanci da aka taba gudanarwa a Nijeriya a lokacin Ibrahim Babangida shine shugaban kasa na mulkin soji daga baya Abacha ya yi juyin mulkin ya rusa mu.”

Ya kara da cewa, “ A wancan lokacin an rantsar damu an kuma bamu takardun sheda na rantsar da mu a matsayin zababbun yan majalisar wakilai na tarayya harta kai ga mun fara kafa kwamitoci a majalisar ta wakilai.”

Isha ya kara da cewa, “ Muna da hakkokin da ya kamata ace an bamu amma ba a ba mu ba har zuwa yau, a karkashin kungiyarmu, muna gudanar da taro duk wata mun kuma gabatar da takardar korafi ga Gwamnati akan hakkokin namu, amma har yanzu ba a ce mana komai ba.”

A cewar Isah, “ Har gaban Kotu mun kai maganar a kan hakkokin namu aka ce mana mu bari za a biya mu hakkokin namu.”

Ya ci gaba da cewa, “Mun kuma kai maganar a ofishin tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, inda ya yi mana alkawarin za a duba koken namu.”

Isah ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari da ya dune su da idon rahama ya bayar da umarnin a biya su hakkokin nasu kamar yadda ya bayar fa umarni aka biya sojojin da suka yi yakin Biafara da kudaden tsofaffin ma’aikatan Hukumar sufurin Jiragen kasa da aka rike masu hakkokin su da kuma tsofaffin ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Nigerian Airways.

A karshe Isah ya ce, “ Mu tsofaffin yan majalisar na wancan lokacin, a halin yanzu mafi yawancin mu muna cikin halin kuncin rayuwa mu da iyalan mu, kuma tuni guda 145 na tsofaffin yan majalisar daga cikin 539 suka rasu a saboda haka, muna kira ga Shugaba Buhari da ya dube mu da idon rahama kamar yadda ya sanya ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar mulkin dimokoradiyya a Nijeriya muma ya tuna da mu.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: