Connect with us

ADABI

Asadul Muluuk (49)

Published

on

Muna ba wa masu karatun wannan littafi hakurin kuskuren da muka yi na maimata shafi da a makon da ya gabata, da fatan za a gafarce mu, yanzu kuma za mu ci ga daga in da muka tsaya kamar haka.

Bayan da sarki ya sallame su, sun fito ke nan suna sanya takalmansu sai ga waziri shi kuma zai shiga wurin Sarki, abin da ko a mafarki ma ba su taba zato ba, ta kalle shi shi ma ya yi mata kallon kaskanci, za ta wuce ta ce; “ Kai ne mafi sharrin al’umma da mummunar makoma, ka taba ji ko ganin wazirin da yake shiga turakar sarki wurin da sai iyalinsa kadai aka amince su shiga, Wallahi kana daga cikin kaskantattu karshenka ba zai kyawu ba, kuma idan har ba a kawo karshen numfashinka a wannan masarauta ba ba za a samu nutsuwa ba.’’ Suka wuce suka bar shi a nan, ya shiga suka yi abin da suka yi da sarki ya fito ya koma gida.

Kashe garin faruwar abin Badee’atulkhairi ta kunshe rigar da je ta kashe Mal’unu da ita zuwa dakin da Asadulmuluuk ke jinya, ta shiga jikinta a sanyaye, ya tambaye ta abin da ta zo da shi.

Sai ta warware rigar, da ya gani ya ce, wannan jinin na menene,? Ta ce, jinin Mal’uunu ne, bakin bawan da ya yi sanadiyyar saka cikin wannan halin, daya daga cikin alkawarin da dauka na ganin bayan duk wanda ya sanya kafa a gurbin da taka, matukar ba ni na yi masa izni ba.

“ Ya Badee’atulkhairi, kada ki rika kashe rai ba da hakki ba, yin haka zunubi ne mai dauke da la’anar Allah da fushi, haka Allah ya fada,” wannan nasiha ce Asadulmuluuk ke yi mata, yayin da hawaye ke zuba daga idanunta, ta amsa cewa.

“ Allah ya yi gaskiya, kuma manzonsa ya isar da sakon gaskiya, amma Allah ya yi magana ne a kan mumini, ni kuwa na san da Mal’uunu da wanda ya sanya shi aikata wannan ta’addanci dukkansu ba muminai ba ne, kawai dai ka bar su a matsayin Musulmai kamar mu, mumini ba dai aika babban zunubi ba. Ka sani tun da ka zo Kasar nan suke alwashin ganin bayan bayan ranka, ni kuma na tanadi kaifin takobi ga duk wanda ya hau hanyar waziri.

An shafe makonni biyu da samun tsautsayin Asdulmuluuk, lamari sai kara gaba yake kullum kafa sai kara hawa take yi a madadin samun sauki, amma sai sake lalacewa take yi, ita kuma Gimbiya Badee’atulkhairi tana kara shiga cikin damuwa.

A ranar sabar din watan Almuharram tana zaune a wurinsa sai ta ji kamshin turaren Fahriyyah wanda hakan ya alamta mata cewa ta iso wurin, sai ta ji sallama ta amsa a kan dole, cikin wata murya mai kama da kuka Fahriyyah ta yi magana “

Ina gaisuwa gareki, kuma ina mai jajanta mana game da abin da ya same mu na wannan tsautsayi.’’ Tana rufe bakinta Badee’atulkhairi ta waigo cikin fushi ta ce; ‘’ Allah wadai da wannan jaje irin na karnukan aljanu irin ki, da ke da mai hali irin na ki Allah wadai da shi, kin san da faruwar abin ba ki kawo mana dauki ba sai yanzu za ki zo ki yi mana jaje bayan abin da zai faru ya faru?’’

Fahriyyah ta ce; “ Ba na kusa mahaifina ya wakilta ni kan wata tawaga ta sulhu tsakanin wasu ‘yan biyu masarauta, kuma ai ni ban san gaibu ba ballantana in san abin da zai faru, amma dai na yi alkawarin yin bincike a kan abin da ya faru. kin manta cewa na yi alkawrin duk wanda zai taba hankalinki ko lafiyarki sai na ga bayansa?

Wannan lamari ya faru bayan tafiya ta, amma dai ki yi min uziri zuwa gobe idan Allah ya kai mu zan zo miki da cikakken bayani a kai.’’

Gimbiya Badee’atulkhairi ta ce; “ Ai mun gaya miki ba ma bukatar wani taimako ko agaji daga gareki.’’ Fahriyyah ta ce; ‘’ Neman taimako ko agaji ga abokin halitta wajibi ne domin shi ke zama sila, Allah ba a ganinsa kuma duk bawan da nemi taimako daga Allah yana samun taimakon ta hanyar wani dan sako daga Ubangijin talikai, ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan samun lafiya gare shi, zan tafi amma sai bayan mako guda zan dawo na barki lafiya.’’

A cikin mako na ukuk daga makonnin jinyarsa, ya zamto tun Asadulmuluuk yana iya magana ya kai mtsayin baya iya magana, idan an yi masa magana sai dai ya yi ishara da kansa ko ya yi ishara da hannu. Saboda tausayi ya zamto mahaifinsa ba ya iya zuwa duba shi, don a duk sa’adda ya zo duba shi sai dai ya koma da yana kuka.

Gimbiya Fahriya ta dawo daga tafiyar da ta yi sai ta zo bayani mai tsoratarwa, ya yin da ta iske Badee’atulkhairi cewa, “Asadulmuluuk fa ba zai ta shi daga wannan ciwo ba, sai bayan kamar wattani akalla takwas, idan kuma ba a yi sa’a ba watannin za su iya kai wa ga watannin shekara, a sannan ko dai an fidda rai da shi ko kuma ya amsa kira ga Allah.

Saboda maganin da a ka yi amfani da shi wajen gyaran da kuma wanda ake shafawa yau da gobe, an karbo shi ne daga wurin wani boka da ke zaune a Gaarul’ahmari, wani bokan aljani da yake zaune cikin bakin kogon yamma da gabar kogin Bahrul’ahmari mai tsananin kunci, a can ne za a samu makarin maganin, amma kuma a iya sani na, wannan maganin ba za a rasa shi a wurin wazirin babanki ba, in kuma ba a same shi ba sai an je an yaki wancananka boka an kashe shi, sannan a bude wani sunduki da ke kasan wani dutsen nika da yake zaune a kai a dauko maganin.

Dama yanki uku suke da irin wannan maganin daga shi sai wasu sarakunan bokaye da suke zaune Birnin Makka, Shikku da kuma Sakeebu, amma dai na wurin wancan bokan sai ya fi zama sahihi tunda shi ya ba da maganin.

Badee’atulkhairi ta fusata ta mike tsaye, saboda bakin ciki ma ta kasa cewa komai sai dai hawaye kadai ne ke fita daga idanunta, shi kuwa Asadulmuluuk yana son tambayarta amma kuma babu baki, don haka shi ma kawai sai hawaye ne ke zuba daga idanunsa. ko da juyowarta ta ga yana zubar da hawaye hankalinta ya sake tashi, Fahriyyah ta ce; “ Har yanzu dai a shirye nake da ba ku ko wacce irin gudunmawa a kan samun lafiyarsa, zan iya zuwa in yaki ko wace irin halitta komai karfinta, da karfina da na dakaruna.’’

Gimbiya ta waigo saboda jin kalamanta, kamar dai ta ce na baki dama, sai ta ji daga bayanta Asadulmuluuk ya daure ya buda baki ya ce; ‘’Ya Badee’ah kada ki ba ta dama idan kika ba ta damar haka za mu wayi gari wata rana na samu lafiya amma ba ma tare da ke, yanzu haka shi ne mafi soyuwa agareki, koko zamana a haka muna ganin juna?

Ina son ci gaba da rayuwa cikin wannan jinyar har Allah ya dauki raina, amma na fi son idan na koma ga Allah ki zauna ki gina sabuwar rayuwa da wani wanda Allah zai kawo miki, in kuma auren dan gidan waziri shi zai zama maslaha a gareki to ina mai baki shawarar aurensa don samun zaman lafiya da rayuwa mai dorewa a rayuwarki.

Tun da wuri da na san zuwana kasar nan zai zama silar afkawarki halin da kike ciki a yanzu, da na roki alfarmar barina a gida, zuwa na Kasarku ne ya yi sanadiyyar jefa ki halin da kike ciki a yanzu. Ina neman gafara daga gareki, amma dai ba na neman komai daga Fahriyyah don ita ce silar afkawar mu wannan hali. ’’
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!