Connect with us

TATTAUNAWA

Rera Wakokin Yabon Manzon Allah (S) Ibada Ne Gare Ni – Malam Habibullahi Lukman

Published

on

A wata zantawar da Wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI Ammar Muhammad ya yi da Malam Habibullahi Lukman fitaccen mawakin Manzon Allah (S) a garin Zariya, ya yi mana bayani dangane da yadda ya fara wake, shawarwarinsa ga mawaka da kuma sauran batutuwa daban-daban masu muhimmanci. Ga dai yadda hirar ta kasance. 

Zamu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu?

Da farko dai suna na Habibullahi Lukman, Sha’iri mai yabon Manzon Allah (S). Ni haifaffen garin Zariya ne. An haife ni a wani Unguwa da ake kira Unguwar karfe.

Zamu so ka bayyana mana irin salon wakokin da kake yi?

Habibullahi Lukman:  ina rubutun wakoki ne amma na yabon Manzon Allah (S) da ahalin gidansa, da wanda duk ya ta’allaka da su. Na kan yi kasida idan Allah ya bani iko ga Manzon Allah (S) da ahalin gidansa. Lallai kasidarmu rubutacciya ce. Domin ni ta tsarin rubutacciyar kasida wata bayyanannen abu ne wanda ake ganewa ta hanyar kafiya da hanyoyin nazami yadda ake rubuta wakokin magabata. Kamar yadda magabatanmu suke rubuta kasidu, to irin wadannan hanyoyin muke bi. Kuma sannan muna buga su, muna rera su, sannan muna yada su ta hanyoyin majalisi, sannan muna yada su a kaset tun daga na ‘audio’ har zuwa na kallo. Lallai haka muke gudanarwa.

Ko zaka iya fadawa masu karatunmu adadin wakokin da ka rera zuwa yanzu?

Mutane da yawa sun sha tambaya ta akan adadin wakokin da na rera, to abin da yasa abin yake zamo min mai wuya, duka wadannan abubuwa da ka tambaya ina yi, na kan rubuta kasida na ba da kamar yadda hadisin Manzon Allah (S) yake cewa; ku tarbiyyantar da ‘ya’yanku abubuwa uku; son Manzon Allah, son Ahlul Baiti, da kuma karatun Alkur’ani, to muna da makarantun Islamiyyu wadanda za a rubuta a ba su, su je su yi, wadansu ma samari ne masu rera wa za a ba su su je su yi, wasu ma za a rubuta ne, ga dai su nan. Saboda haka wadansu ma idan sun tafi ba a garin bane, an riga an ba su, bukata dai a nashshara. Sannan akwai wanda nake rerawa, sannan kuma akwai makarantu a Zariya wanda yake fitattu ne, duk wanda ya ji wakokinmu ya san da cewa muna tare da makaranta kaza da makaranta kaza. Saboda haka ni kaina ba wai sun yi yawan da ba za su kirgu bane, bamu tattara bane, amma dai har yanzu muna kan tattarawa. Saboda ka da ka zo ka fadi abin da bai kai ba, ko ka rage wani abu. Har yanzu dai muna kan hada su.

Shin waken da kake yi, ka ta so ka ga ana yi a gidanku ne ko sha’awa ce yasa ka fara?

Ni abin da nake dauka da waka, kowacce iri ce zaka yi, wani abu ne da idan Allah ta’ala ya ri ga ya yi ka mawaki, zaka iya yin kasida, ko garin da babu kowa ne ba ka taba ganin samfur ba, to idan Allah ya yi za a same ka mai yin wannan abin. Na rayu a Unguwarmu, akwai masu zuwa suna yabon Manzon Allah da Larabci, irin masu Ishiriniyya, masu kaza, na kan bi su, sai mu je mu zauna, na ga suna rerawa, ina kallon irin wannan. Idan sun gama su kan karanta na Hausa, a dan samo irin wakokin irinsu Shaikh Aliyu na Mangi a dan karanta baitoci uku ko hudu sai a yi addu’a. To, wannan abin na burge ni yana shiga cikin raina idan na tafi. Tuna ina karami sai na yi tunanin ya zan yi na rubuta? Sai na fara sa biro da takarda da sauransu ina rubutawa har dai na ta so a hakan. Na fara rubutu, sannan kuma dai na ga ba haka ya kamata na yi ba, ya kamata wadannan Malamai da nake tare da su, wanda suke zuwa wannan Ishiriniyya, na rika karatu a wurinsu, yadda zan gane mene ne shi ka’idojin waka, sai na fara tunanin na karanta Aruli haka, da irin makarantar da na yi baya, sai na ba wannan karatu na bangaren waka din muhimmanci sosai domin na gane ya ya ake yi rubuta waka? Ya ya ka’idoji yake? Wannan hanyar shi na bi har ya zamo cewa na fara wake, dama wakar yabon Manzon Allah ita tafi burge ni a bisa kowacce irin waka. Shiyasa sai na dauke ta, na yi dukkanin binciken abin da zan yi a kan yadda zan yi ilimin waka, tunanina dama a nan ya karkata kuma har gobe muna nan akan wannan tunanin.

Wani irin nasarori ka samu tun bayan tsundumarka harkar waken yabon Manzon Allah (S)?

Babbar nasara ta farko shi ne ka same ka a hanyar, kuma ka samu wadansu lokuta kana kai, kuma zuciyarka a yanzu yadda take bata nuna maka cewa zaka iya bari. Kuma kana da yakinin cewa ka mutu a kai, wannan shi ne nasara ta farko wanda ni ya shafe ni, kuma na tabbatar da ina kan hanya mai kyau. Kuma ina tabbatar da cewa na yadda Allah ya kashe ni a wannan hanyar. Kuma duk wata gwagwarmaya da zan yi a ciki, na tabbatar ina kan hanya ne mai kyau, kuma daidaitacciya, kuma na yi yakini da hakan. Nasara ta biyu kuma da muka samu shi ne har duniya ta gane cewa kana son Manzon Allah kuma kana yabo a gare shi, shi ne wanda jama’a suke bayyana. Kamar shiga ‘album’ dinmu na kallo da ‘audio’ dinmu cikin al’umma, da fadakawarmu yana shiga cikin jama’a, shi ne nasarar da muka samu na biyu. Wadannan sune babban nasara.

Kalubale fa?

Kalubale ba a rasawa. Duk abin da zaka yi akwai kalubale. Ko da Annabawa ma, wanda suka rayu da mutanensu, ba Annabin da aka aiko shi da ba a sa mishi wani kalubale ba. Mu ma mun fuskanci kalubale. Ka san yanayin mai yabon Manzon Allah (S) zai samu kalubale tun daga lokacin da yake son ya mika sako ya zuwa ga mutane, to daga wannan lokacin, wani zai amshi sakonka, wani kuma ba zai amsa ba. Kai kanka wani lokacin zaka sami wadansu matsaloli na game da harkar tafiye-tafiye ko kuma ma yadda zaka gudanar da al’amuran. Tunda mu mun dauke shi ibada ne. Zamu fito mu nema da jikinmu ko mu je mu yi wata sana’a mu nema mu zuba, saboda kokarinmu da niyyarmu da da’awar da muke kira ta kai. To irin wadannan abubuwan sune muke samun tirjiya, wani ya karba wani ma ya soke ku ya ce ba kuna yi don Allah bane, sune irin kalubalen da muka rika fuskanta a cikin harkar yabo.

Kana harkar kasuwancin waken ka ne?

Zamu iya kiran shi kasuwanci, amma ainihin yadda zamu kira abin shi ne; wadansu hanyoyi ne ake bi domin abin ya tabbata? Ya dore, ka yi ka kara? Kuma sannan wadansu hanyoyi ne ake bi na yada lamuran? Kila idan na yi wannan abin Naira biyar ne misali, sai na saka naira biyar dina a ciki, to kokarina naira biyar din nan ba ta haifar min da goma ba, a’a ta rike kanta wanda za ta iya bani dama na yi wancan. To alal akalla a wannan tafiyar muna da wata mahada wanda muka ambaceta da Kamfani ne mai suna Mbaz Multimedia. Ita wannan mun hada guiwa da guiwa da karfi mun tsaya akan cewa yadda zamu yi mu yada yabonmu ta wannan hanyoyin. Akwai abubuwan da bai yiwuwa, da a ce zaka iya bugawan, ka saki, tare da cewa gobe zaka iya ci gaba da lamuran, to da haka din zai iya zama a ce masa kasuwanci. Amma lamuran ba wai zamu kira shi kasuwanci ba, amma idan mun kira shi kasuwanci…. Ma’anar dai da yake badawa, to hanya ce dai ta yadawa.

Kana cikin wata kungiya ne ko kuma kana da naka kungiyar da ka kafa?

Akwai kungiyar da nake jagoranci ita ce Hilikul Madihina. Sannan akwai kungiyar da ni memba ne a cikinta kamar Jama’atu Faidhatul Anwar, kungiya ce gamammiya na Sha’irai na Jihar Kaduna, ina cikin wannan kungiyar. Sannan ina cikin kungiyar mahadar duk wata manufa na yada wani abu da kake yi ta hanyar Sufaye da muke yi, irin su: Majma’u Rijalul Tijjaniyyah, wadannan duk kungiyoyi ne wadanda muke harkoki a cikinsu.

Wani shawarwari kake da shi ga mawaka irin ku?

Shawarar da nake da shi ga mawaka musamman irinmu shi ne duk abin da zamu yi ya zama mun gina shi akan manufa mai kyau. Duk abin da zamu yi mu yi shi akan mizani na Shari’a, mu auna shi tsakanin kurani da hadisi, sannan duk abin da zamu furta cikin soyayyar Manzon Allah da janibinsa ko ahalin gidansa ya zama cewa muna da cikakken kwakkwaran hujjarmu na fadin wannan. Wanda ko da mai kalubale ya zo ya same mu ba shi da yadda zai yi ya ture gininmu saboda mun gina shi ne akan ayar Alkur’ani da Hadisi. Kuma idan muka dauki wannan ya zama cewa muna da magabata masu bamu shawarwari da masu duba mana lamuranmu, ka da mu ce don mun isa zan fadi abin da na ga dama. Mawaki ya sani, an ba shi amanar kwakwalen al’umma ne masu sauraron shi. Duk sha’irin da yake yabo har a zo a tattara a wurinshi, to an ba shi amana ne, to cin amanarsa a wurinsu shi ne ya fadi musu abin da shima ya san ba shi da asali, shi ne a ci amanar kwakwalensu saboda ai yarda da kiran da yake musu suka amsa  saboda Manzon Allah yake kira ne, ka ga ke nan ya yi yaudara da Manzon Allah, ya zo kuma ya mika musu wata manufa wanda ba ita ce ya kamata ba ya mika ba, wannan shi ne shawarar.

Wani sako kake da shi ga masoyanka?

Masoya ina godiya a gare su, kuma ina dadin idan na yi kasida wadansu suna min waya su ce; abu kaza mun ji ka ce kaza, me kake nufi da kaza? Ni kuma abin da na sani a kai sai na ce; to, kaza nake nufi. Idan ko na shawara ne, za su ce; to ka fadi kaza, kana ganin jama’a ba za su ce kaza ba? Sai na ce; eh to gaskiya ne, wanda kuma na yi shi ina da hujja sai na ba da, to ka ga wannan ina jin dadin masoyin nawa a haka, wannan masoyan nawa nagode, Allah ya saka musu da alheri.

A karshe me zaka ce wanda bamu tambaye ka ba?

Alhamdulillahi, wannan dai shi abin da ya fi ci min tuwo a kwarya. Wato wannan maganar da na kawo ta a karshe. Ina maganar lallai-lallai Sha’irai mu mike, kuma duk abin da zamu yi, mu yi shi da ikhlasi, duk wanda yake yi don Allah to wallahi ba zai turu ba, in dai don Allah kake yi, saboda haka mu rika yi don Allah. Na tabbatar da cewa babu wani abin da za a biya Sha’irai wallahi fa ce Allah. Saboda za su kashe lokuta su kashe sana’o’insu, su kashe kaza, su je su daukaka kalmar Allah ba tare da suna tunanin wani abu zai bijiro ko kuma suna yi don wani zai ba su ba. Akwai mawaka wanda bamu ba, wanda yanzun nan mutum zai fara waka, yanzu zaka gan shi da mota da gidaje da duk wani abin mallaka, kuma a ba shi wani madafu na iko wanda zai da fa ya mike ana jin shi a duniya. Kuma muna da fasahar, sannan muna da kalmomin da zamu fada fiye da shi, amma mu muka hakura muka juya wannan abubuwan baya, muka ce mu zamu yi yabo ne saboda Manzon Allah (S) ko da zamu tafi rigunanmu suna kecewa. Ko da zamu yi tafiya ana dukanmu, ko da za a hana mu zamu yi a daki, ko kuma zamu yi mubaraza ne da kowaye a ciki, mun yadda mu yi. Kuma mu mutu akan harkar da muke yi, wallahi idan ko Sha’iri ya riki haka, to wallahi tallahi shi abin a jinjinawa Sha’iri ne akan inda ya tsaya. “wa amma man kafa makama Rabbihi wanahan nafsa anil hawa….” “Fa’innal Jannata hiyal ma’awa.” Wannan busharar kawai zan iyawa sha’iri idan ya ji irin wannan.

Mun gode.

Habibullahi Lukman: nagode.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: