Connect with us

ADABI

Tasirin Wakokin Mata Ga Wadanda Aka Yi Ma Su Na Dakta Mamman Shata Katsina (4)

Published

on

Mata Masu Alaka Da Zaman Kai

Muna sa ran son duk wani abu mai kyau ta sa ya yi ma ma fi yawancin mata masu zaman kan su waka (Indo, 1998; Salisu, 2005; Titi, 1999; Danbaki, 2003) (Jeni, 2011; Ture, 2011; Dilla, 2011; Tambai; 2011; ‘Yar masaka, 2013)

Misali, asalin haduwar sa da Indo Musawa a Musawa, ta gudo daga gidan aure ta yi ta zo wurin kanen mahaifiyar ta, a tsakanin 1956, wanda kuma shi me Galadiman Musawa a lokacin. Da ya gan ta, shi bai san tana da aure ba, sai ya aiki makadin sa, Musa Dan Amare ya ce mata yana son ta da aure. Da ya je, ashe kanen mahaifin na ta ya gan shi, sai ya sa aka kama shi aka daure, sabili da ya yi magana da matar aure. Sai da aka ci shi tarar fam biyu. Shi kuma Shata, jin haka, sai ya gudu daga Musawa. To karshe Shata da Indo ba su kara yin ido hudu ba sai cikin Oktobar 1959 lokacin ma ta kashe aure har ta zo Katsina ta kama daki a Republic Otel, shi kuma yana wasa a unguwar ‘Yar’aduwa Katsina. Ita da kawayen ta suka ji labara suka zo kallon sa. To, yana ganin ta cikin mutane, a take ya yi mata waka.

A wannan ajin akwai su Ajeje da Assibin Danmusa, har da Indo Musawa. Itama.  Kuma a wannan ajin, akwai matan da ba su yi siyasa ba, don haka ba su kasaita ba, ba su kuma fito sarari ba, amma dalilin wakar da makadin ya yi masu, ta ba su damar hawa bisa wannan mataki, na samun suna a Duniya. Kafin ya yi mata waka cikin 1959, Duniya ba ta san Indo Musawa ba. Kowacce mace da ake kira uwar burgwui (uwar kusa) mai zaman kanta tana hankoron ta ga Shata ya yi mata waka domin ta kara tallata kan ta, domin ta ida fitowa sarari kowa ya san ta don inganta sana’ar ta (Munari, 1990128; Awwali, 2006; Rabi, 2011, 2012) Wakar makadin ta kara masu daukaka a cikin sana’ar su ta karuwanci. Ka ga manema za su karu, daga nan kudi da farashi suma su kasu. Ba’ada bayan haka, sunan su kuma ya tafi har inda bas u zato, saboda kwarjinin wanda ya yi masu wakar.

Irin abin da ya faru ga ‘Yar Nabala Yamai ke nan cikin 1974. Ko wakar zambo wani mawaki ya yi ma karuwa, to makarin sa shi ne ta nemo Shata ya yi mata wakar yabo don ya shafe wancan tabo na baya (Doka, 1998) Nana (2011) ta yi nuni da cewa domin hakane kowace mace da ta shahara a ko’ina cikin Arewacin Najeriya ta ke son makadin ya yi mata waka (Jumeme, 2014)

A wakokin su ya kan bayyana surorin su da halayyar su ko dabi’o’in su (Mati, 2011; Maikudi, 2011). Kamar misali ya ce mace mai kirki, mai kyauta, da sauran su. To wannan kalaman na kara jan hankalin su. A cikin sunduki, cikin akwati na karfe, ran juma’a ana azahwar Indo tassafko…’ Indo ta nuna cewa an ba Shata labarin ran Juma’a aka haife ta, shi ya sa ya fadi haka, don ya nuna darajar ta.

Nana-Dankwara (2000) da Maitama (2003) sun bayyana cewa nasarar da Alhaji Mamman Shata ya samu wajen ruruta mata da sana’o’insu shi ne na ratsowa cikin zamanin kakar karuwanci ko zaman kai da mata su ka yi. Wannan ya ba su matan ‘yancin a yi masu waka. A wancan zamani, karuwanci wata babbar hanya ce ta kasaita da nuna alfaharia tsakanin mata. Karuwancin ma mataki-mataki ne, don wasu sun fi wasu aji da kima (Amina-Rugar-Idi, 2003). Domin al’amarin kasaitar ta su ta kai, sai a wuci-wuci su ka rika neman Shata da ya kara nuna su a Duniya domin su ida fitowa sarari (Sambo, 2001; Dan’asabe, 2011; Sa’I, 1998; 2014)

A waje daya, shi kan sa Alhaji Shata, harkar zaman kai na mata ya kara tallata shi don ta nan ya kara nuna basirar sa. Yawancin manyan matan da su ka shahara a Kasar nan, da ma na ketare ya yi masu wakoki (Ghana, 2004; Nana-Daku, 2009) Wadanda aka tattauna da su sun hada da: Hajiya Indo Musawa (1959), Hajiya A’isha Yalwar Yakubi Shandam (1970) da Hajiya Lami Shagamu (1983) Lami ta nuna cewa Shata y agama yi mata komi a Duniya, tunda duk inda bahaushe ya ke, ba inda wakarta ba ta kai ba. Komi na Duniya, tana samun sa da sauki ta dalilin waka.

Mata Ma’aikatan Gwamnati

Hajiya Binta ‘Yar Masaka Kakumi (1957) malamar tsabta ce a Dutsin-Ma a tsakanin 1957. Wakar da makadin ya yi mata a West End Hotel Dutsin-Ma. Duk da yake Bakandamiya wakar ‘mazan jiya’ ce, kamar yanda Shatan ya yi hasashe, amma an dauki amshin ta an yi ma Binta waka. Yana cewa a ciki: Malam ‘Yar Masaka, idan uban ki ke saka, to sako man bullan.  Wakar ta kara jawo mata kwarjini da soyayyar jama’a a ko’ina. Wasu abubuwa da dama da a da kafin Shatan ya yi mata kirari sun fi karfin ta, bayan ya yi mata waka sai su ka kasance ma ta da sauki. Shata ya wake malaman tsabta da ‘yan doka, don dai zancen sub a ya cikin wannan takardar (Kankara, 2010a; 2010b; Gundawa, 2011; Maifada, 2007).
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: