Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

27 Sun Rasa Rayukansu A Jirgin Ruwan Da Ya Nutse A Legas

Published

on

A kalla mutum 27 sun rasa rayukansu, lokacin da wani jirgin ruwa ya nutse a Egbin kusa da yankin Ijede cikin karamar hukumar Ikorodu ta Jihar Legas. Wakilinmu ya ruwaito mana cewa, jirgin ruwan ya dauko da fasinjoji daga Lekki, inda ya nutse a garin Egbin. 

Wani wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa mai suna Hogan Bassey, ya bayyana cewa, jami’ai masu bayar da agajin gaggawa ta Jihar Legas, sun tsamo gawarwaki guda biyu. Bassey ya ce, “an samun irin wannan hatsari ne a daran jiya a yankin Egbin. A cewar jami’an, fasinjoji guda 18 ne a cikin jirgin ruwan, amma na ji daga magiya mai tushe shi ne, mutum 27 ne ke cikin wannan jirgin ruwan, gawarwaki guda biyu ne a ka samu nasarar tsamowa daga cikin ruwan. 

“Lamarin ya afku ne da misalin karfe 7.38 na dare, jirgin ya dauko fasinjojin ne daga garin Lekki, inda ya kife a Egbin cikin garin Ijede. Har yanzu ana kokarin ceto mutanen.”

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Legas, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu, ya bayyana cewa, an samu nasarar tsamo gawarwaki guda biyu. Oke-Osanyintolu ya ce, “sama da fasinjoji guda 20 ne su ke cikin jirgin lokacin da ya kife. Har yanzu ana kokarin ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su.”

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Legas, Bala Elkana, ya tabbatar wa wakilinmu da faruwar lamarin, har yanzu ana kokarin ceto mutanen. Elkana ya bayyana cewa, “tawagar jami’ai wadanda suka hada da ‘yan sandar bakin ruwa, su na kokarin ceto mutanen.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: