Connect with us

MAKALAR YAU

Allah Sarki Talaka!

Published

on

Kai! gaskiya a na fama da wani abu wai shi kirkirarren talauci a wannan kasar ta mu mai wadataccen albarkan man fetur da sauran albarkatun ma’adinai irinsu tantalaye, gwala-gwalai, dadin dadawa kuma manoma na samun yadda su ke so (ga ruwan sama).

Dukkan ni’imomi Allah ya sauke su a wannan kasa mai suna Nijeriya amma duk da haka, mafiya rinjayen mutanen kasar ba su dandanon wannan ni’ima saboda wasu daidaiku sun yi babakere sai handamewa su ke yi, tamkar mallakin uwayensu.

Kaima na san, ka san akwai bakin kirkirarren talauci a wannan kasar, kuma ka san akwai arziki sosai a kasar. Komi na rayuwa sun bambanta tsakanin masu kudi da talakawa, wanda da gangan ne su masu kudin su ka ja layi tsakanin hidindimunsu da na talaka.

Arzikin Nijeriya tuntuni ya zama na gado, daga wadanda su ke sarrafa shi sai iyalinsu da abokansu makusanta. Duk wanda bai cikinsu sai dai hancinshi ya sunsuno kamshi daga nesa.

Na jima da ra’ayin cewa talaucin mutanen Nijeriya kirkirarre ne ‘Artificial Poberty’, kuma da gangan a ka damfarawa jama’a shi don a mulke su. Wannan shi ne bakin muguntar wanda ya tattara dukiya ta hanyar zalunci, ba zai so wani ya samu arziki ba, saboda kar a yi kafada da kafada da shi.

Mutane sun yi zaton shi kirkirarren talauci (musamman na ‘yan Nijeriya) gazawa ne wanda talaka ya yi, amma shi kuma mai kudi tsabar hazaka da kwazo ne. Sam! ba haka ba ne.

A kasa wacce gwamnatinta da masu tafiyar da al’amuran gwamnatin komi na tafiya dai dai kuma masana’antu da ma’aikatu sun wadatu sosai, shi ne za a iya jefa ayar tambaya ga wadanda a ka samu da wani abu makamancin talauci.

Saboda a irin wadancan kasashe da na fadi, akwai ayyuka har ma wasu kananan ayyukan sai an rika nemo bakin haure su na yi. a irin wannan hali idan ka ga talaka ka na iya jefa shi cikin jerin ma su matacciyar zuciya.

Amma Nijeriya sam ba haka ba ne, masana’antu tuntuni an kashe su murus, sun daina aiki ballantana ‘yan kwadago su samu aiki. Ba a maganar ma’aikatu, saboda yawancin ma’aikatun da a ke da su masu daurewa na gwamnati ne.

Su kuma ma’aikatun gwamnati da yawansu su na la’akari ne da kwalin shaidar karatun mutum, wanda tun daga nan damuwar ta ke farawa.

Makarantu sun sauya sun za ma na kudi, daukar dawainiyar karatu daga firamare har zuwa kammala Jami’a ba kowanne magidanci ba ne ke iyawa. Saboda da kyar ma a ke samun abin da za a ci ballantana kuma a samu wanda za a adana don dawainiyar makarantar yara.

Ga iyayen da ke aiki tukuru ba dare ba rana don ganin ‘ya ‘yansu sun yi karatu kuma, matsalar na farawa ne yayin da ‘ya ‘yan su ka kammala makarantar lafiya lau, a wasu lokutan ma da sakamako mai kyawun gaske.

Samun aiki shi ne babban kalubalen, saboda ma’aikatun da su ke na gwamnati ne sun dade da komawa kasuwanni, sai da gumin goshi za a saurare ka. Idan su ka saurare ka, kai ne wanda za ka yi aiki ga takardunka komi tsaf – tsaf, amma kuma sai ka biya cin hanci.

Ko ka biya cin hanci, ko kuma ya kasance ka san wani babban mutum wanda zai rubuta maka takarda mai dauke da sa hannunshi. Saboda irin wannan bahaguwar dabi’a ne ya sa a ma’aikatun gwamnatin daga ‘ya ‘yan manya, sai wadanda su ka san manya, sai wadanda a ke cire wani kaso daga albashinsu, sai kuma wadanda su ka siyi gurbin aikin da kudi mai tsada.

Yayin da mutum ba ya jin yunwa, kwakwalwarshi za ta rika sawwala ma shi cewa kowa ma a koshe ya ke, haka nan yayin da mutum ke fama da matsananciyar yunwa, zai rika gani kamar kowa ma na jin yunwa ne.

Wannan bakin kirkirarren talauci da mutanenmu ke fama da shi al’amari ne da ke bukatar mafita tun kafin ya sauya ya zama wani abu na daban, tunda ya jima da fara sauya kamanni. Idan kai ka na samun abinci sau uku a rana, wani sau biyu ya ke samu, sannan akwai wanda sau daya ya ke samu, kai da yawa haka nan su ke kwanciya cikinsu sai dai ruwan famfo.

Barayin gwamnati wadanda su ke tsilla – tsilla da rashin gaskiya a ofisoshinsu, su ka tara makudan dukiya (ba su koshi kamar wuta) sun fi raina talaka fiye da kowa. Sai dai, su na manta cewa kudin da su ke tinkaho da shi su ke wani huhhura katon hanci da girman kai, hakkin wannan talakan da su ke yiwa kallon banza ne su ka hana shi.

Sun sace dukiyar talakawa, amma ba a nan abin ya tsaya ba sai kuma su ka sa karar tsana da kyama ga duk talaka. Makarantun ‘ya ‘yansu daban da na ‘ya ‘yan talakawa, asibitocinsu daban da na talakawa, kasuwanninsu daban da na talakawa, abincinsu daban da na talakawa, yanzu ma sunayen ‘ya ‘yansu daban da na talakawa; su ke da Ameerah, talakawa kuma na da su Kande.

Idan wannan bakin kirkirarren talauci ya ci gaba da wanzuwa tare kuma da nuna tsana na masu sace dukiyoyin ga talakawa babu makawa watan watarana abubuwan da ba a so su faru za su auku. Ko Mage idan ka bi ta a guje ta kai bangon da ba ta iya tsallakewa, juyowa za ta yi ta nufo ka a yi ta ta-kare.

Ku yi ta sheke ayarku, watarana fa idan talaka ya ji radadin talaucin nan dole ne ya kwala ihu, kai har ma ya dawo hayyacinshi ya nemi mafita. Bari dai na yi shiru. Mu hadu mako mai zuwa!
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: