Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Ana Farautar ‘Yan Hidimar Kasar Da Suka Tsere Da Bashin Miliyan 22

Published

on

Gidauniyar masu kula da ‘yar bautar kasa wanda a ka fi sani da ‘National Youth Corps Foundation’ a turance, ta na neman a kalla masu yi wa kasa hidiya guda 75, wadanda su ka amshi bashin kudi a kalla naira 300,000 zuwa naira 400,000, domin su fara kanan sana’o’in hannu da kasuwanci, da sharadin za su biya bayan shekara hudu. ‘Yan bautan kasar da a ke nema ruwa a jallo, sun riga sun gama aikin nasu na yi wa kasa hidima, sun yi amfani da takardar shaidar bautar kasar wajen amsar bashin, wanda wannan takardar shaidar ce, kadai hanyar da zai ba su damar amsar wannan bashin.An bayyana cewa, ‘yan bautar kasar da a ke nema ruwa a jallo, sun bar takardar shaidan nasu na kammala bautar kasa a hannun gidauniyar, kimanin shekara hudu Kenan.

Babban Jami’in gudanarwa ta gidauniyar NYSC Foundation, Bako Bentim, ya tabbatar wa manema labarai cewa, a lokacin da a ka bude gidauniyyar koyar da sa’anar hannu da kasuwanci ta sassanin ‘yan bautar kasa da ke yankin Kubwa a cikin garin Abuja. Gidauniyar ta NYSC Foundation ta ce, ana horar da ‘yan bautar kasar a sassanin ta Kubwa cikin garin Abuja ne, inda ya hada da bayar da tallafin kekunan dinki guda goma, domin koyan san’o’in hannu.

Daraktan sassanin ya bayyana cewa, suna samar wa da matasa ‘yan bautar kasa bashi a kan kudin ruwa kalilan, su na bada bashin ne kadai ta nasadiyar takardar shaidar kammala yi wa kasa hidima da kuma masu tsaya musu mutum biyu. Ya kara da cewa, sun sanya hanyoyin amsar da bashin ne, domin ya zama mai sauki ga duk wani dan bautar kasa.

“Mu na fuskartar matsaloli, saboda wasu ‘yan bautar kasar sun ki su biya bashin da suka amsa, mu na da akalla ‘yan bautar kasa 100 da su ka amsa bashin, inda har yanzu ba su biya ba kuma har yanzu takardar shaidarsu na kammala bautar kasar  ta na hannunmu. Har izuwa yanzu ba su zo sun amsa ba na tsawon shekaru”

Mu na bayar da bashin ne tsakanin naira 300,000 da naira 400,000, ya danganta da yanayin kasuwancin da dan bautar kasar ya kawo zai yi. A cikin binciken da mu ka yi, an gano cewa har yanzu akwai a kalla sama da ‘yan bautar kasa da ba su biya bashin ba kuma har yanzu mu na neman su ruwa a jallo,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: