Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Gobara Ta Kone Wata Tsohuwa ’Yar Shekara 66 A Anambra

Published

on

Wata tsohuwa mai suna Beronica Okwuogu ‘yar shekara 66 da haihuwa, ta rasa ranta a wata gobara wacce ta tashi a Awka da ke cikin Jihar Anambra. Har zuwa lokacin da a ke hada wannan rahoton ba a san musabbabin tashin gobarar ba. Amma wadanda lamarin ya afku a gaban idanunsu sun bayyana wa manema labarai cewa, marigayyar ita daya ce a cikin gidan lokacin da wutar ta tashi da misalin karfe 10.30 na safen ranar Asabar.

Wadanda lamarin ya afku a gaban idanunsu sun ce, “an kasa samun jami’an kashe gobara na jihar lokacin da gobarar ta tashi. Kafin a samu taimako daga wajen mutane, tsohuwar ta kone kurmus, inda hart a kai ga ba a iya gane ta.”

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin. Mohammed ya bayyana cewa, “ da misalin karfe 10.30 na safe ne a ka samu gobara a rukunin gidaje da ke kusa da Mocdons, cikin kauyen Amuda a yankin Awka ta karamar hukumar Awka ta kudu da ke jihar. Tawagar ‘yan sanda masu gudanar da sintiri a yankin Awka, sun ziyarci wurin da lamarin ya afku, domin dakile ayyukan bata-gari wadanda za su iya amfani da wannan damar domin su yi sata a wurin. Mutanen yankin ne su ka samu nasarar kashe wannan gobara.

“Amma duk da haka dai, wuta ta kone wata tsohuwa mai suna Misis Beronica Okwuogu, ‘yar shekara 66 da haihuwa. Ta samu mummunar raunin kona. An garzaya da ita asibitin Regina Celi Hospital, domin yin jinya, a nan ne likita ya tabbatar da mutuwar ta. “An ijiye gawar marigayyar a dakin ijiye gawarwaki da ke asibiti, domin gudanar da yin gwaji.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: