Connect with us

RA'AYINMU

Jawabin Shugaban Kasa Buhari Na Ranar Rantsarwa

Published

on

’Yan adawa sun yi zaton ko Buhari zai yi jawabin ranar rantsuwa a ranar da a ka rantsar da shi 29 ga watan Mayu, ta yiwu kila saboda su na jin kamar bai dace ba mayar da Ranar Dimokradiya ranar 12 ga Yuni. To, sai dai sun sake shan kunya ma wannan karon. Buhari da mataimakinsa Farfesa Osinbajo an rantsar da su ne kurum a ranar 29 ga wata, to amma dukkanin sauran bukukuwan sai ranar 12 ga Yuni kamar yadda shugaban kasar ya fada.

Lallai ko shakka babu, jawabin na shugaban kasa da ya gudanar a wurin bikin 12 Yuni na cigaba da jan hankulan jama’a, wadansu da su ka damu a baya, to da sauraron jawabin kuma sun dan samu nutsuwa, domin jawabin ya karfafa iyaka yadda ya kamata. A cikin jawabin, shugaban kasar ya fadi abubuwan da wani shugaban kasa kafin sa bai fada ba.

Cewar da ya yi zai tsamar da ‘yan Najeriya miliyan 10 daga kangin talauci, abin jin dadi ne kuma abin a yaba ne. Kai, ko wannan jawabin ma kadai ai ya isa ya gamsar. A duk lokacin da wani shugaban kasa ya yi irin wannan maganar, to dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan yunkura ne don ganin tabbatar da hakan.Wannan kalaman nasa, sun yi kama da irin shahararren jawabin shugaban kasar Amurka, John Kennedy, inda ya ce, Amurka za ta tafi duniyar wata kafin shekara 10.

Mu na ji a ranmu cewar, wannan kudurin na tsamar da mutum miliyan 10 da shugaban kasa ya ce zai yi; wato rabin ‘yan Najeriya kenan, to abu ne mai yiyuwa. A ganin an cimma hakan, shugaban kasar na da darasi da dama da zai koya daga kasar Sin. A cikin shekara daya, kasar Sin ta fitar da mutanen kasarta miliyan 13 daga talauci. Wanda a cikin jawabin shugaban kasar, za mu ga yanda ya maida hankali sosai kan mutanen karkara, wanda har ya yi kira ga gwamnatin jihohi da su bi sawun sa wurin yin hakan.

Wannan abun jin dadi ne da farin ciki ga wadanda su ka fahimci abun. Daga shekarar 1978 da kasar Sin ta fara dagowa, ta tsamar da mutanen ta miliyan 850 daga yanayin mugun talauci. Kasar Indiya ma, ta tsamar da ‘yan kasarta miliyan 270 a cikin shekara 10 daga 2005. Saboda haka, shugaban kasar Najeriya zai iya koyar darasi daga kasashen. Dukkanin kasashen sun dogara ne da fadada tattalin arizkin su ne wurin samun wannan nasarar.

Bayan wannan ma, shugaban kasar zai iya daukar darasi daga shugaban kasar Amurka Lyndon Johnson na yakin sa da fatara da talauci. Shugaban kasar, wanda ya gaji Kennedy bayan kashe shi, ya yi mulkins aa tsakanin 1963 zuwa 1969. Ana lissafa sa a cikin manyan shuwagabannin kasar Amurka, to amman bah aka kawai ya zama hakan ba, ya yi anfani da ‘yan majalisa da yin dokoki. Jawbinsa wanda ya gabatar a 1964, kamar shigen na Buhari, shi ya jaza wa majalisar kasar yin dokokin inganta tattalin arziki tare da samar da wani ofishin samar da abubuwan yi ga ‘yan kasa. A ganin samar da hakan, shugaban kasa Johnson ya gina kasar ta hanyar ware makudan kudi ga fannin ilimi da lafiya a matsayin hanyoyin magance talauci.

Kasar Jafan ma, wacce ta kashe makudan kudi wurin gina yara ma su tasowa ta fannin samar da ilimi bayan rugurguzar da kasar ta samu a yakin duniya na biyu, kasa ce da Buhari zai iya daukar darasi daga gare ta ita ma.

A duk tarihin duniya, kasar Jafan ce kadai kasar da aka taba anfani da makamin nukiliya kanta inji kasar Amurka a shekarar 1945. Shuwagabannin kasar, bayan ganin abunda ya faru da su da jin tozarci, sai su ka yanke matsayar ware kusan dukkanin arzikin kasar wurin samar da ilimi ga yara ma su tasow. Wannan yunkurin kuwa, shi ya sanya kasar ta zama kasa ta biyu a azriki a duniya bayan Amurka. Jafan ta dade sosai tana ta biyu a ariki kafin kasar Sin ta doke ta ta mayar da ita ta uku.

Bayan wadannan duka, shugaban kasar zai iya dauko darasi daga kasar Koriya ta kudu, waton kasar da ta shahara da kere-kere da kuma manyan mai kanfanonin nan na ‘Samsung’, ‘LG’, ‘Kia’, ‘Hyundai’, ‘Daewooo’ d asauran wadansu kanfanonin. Gwamnatin kasar ta bayar da kulawa sosai ga kanfanoni ma su zaman kansu da harkar kere-kere.

Girmama ranar 12 Yuni da Buhari ya yi har abada zai zama cikin tarihi kuma abun a yaba, shi ne kuma abunda ya dace. Tsohon shugaban kasa, Cif Oleseguin Obasanjo, wanda shi ne ya anfana da abunda ya faru na 12 ga Yuni, domin da ba dan hakan ta faru ba da bai samu zama shugaban kasa ba, to amman ta ya zai yi haka alhalin yana hassadar MKO Abiola din, wanda ya ke dan kabilarsa kuma abokin karatunsa (a sakandare). Shuwagabannin PDP ma da su ka gaje shi (Umaru Musa Yar’adua da Gooluck Jonathan) ma duk ba su yi ba. wannan shi ya mayar da sukar da PDP key i na ce wa Buhari na siyasa ne da 12 ga Yuni kawai shafci fadi. To shin ma, mai nene illar siyasantar da 12 ga Yuni ma? Laifi ne ‘yan siyasa su yi siyasa? Shin mai ya hana Obasanjo, Yar’adua, da Jonathan yin siyasar da suma da 12 Yuni din?

Ba nan kadai ba, shugaban kasa Buhari kuma ya kara da canza wa babban filin wasa na kasa suna wacce Obasanjo ya gina zuwa ‘Moshood Abiola National Stadium’. Wannan ba ma kawai daidai ba ne, a’a ya kuma nuna irin halin dattako da sanin ya kamata na Buhari.

A bayyana yake cewar Shugaban kasa Buhari na son bariin tarihi mai kyau, kuma hakan shi ne burin kowane shugaban kasa. Da zaman sa shugaban kasa, abu na farko da ya fara yi shi ne kawar da cinhanci da rashawa. Yanzu a Najeriya, ba wani wanda ya isa ya zauna da shugaban ko mataimakinsa a tattauna yanda za a saci kudi, ko kuma ya yi mai dadin baki don ya bashi wasu kwangiloli.

Haka kuma, bai yi wata-wata ba da hawansa mulki, ya fatattaki kungiyar Boko Haram tare da anso wasu kananan hukumomi da a da su ke hannun ‘yan kungiyar. Sannan ya ci gaba da yin wasu ayukkan da ya gada daga wadanda su ka gabace shi kamar aikin hanyar jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna, tashar jirgin sama, hanyoyi, wutar lantarki da kuma dabbaka asusun kasa na bai-daya. Ya kuma sauya harkar noma, ta yanda har matasa na noma yanzu a kasar da sauran ayukkan jin dadi, walwala da inganta rayuwar al’aumma wanda yake ba a taba wanda ya kai nasa ba a baya.

Tun bayan da Buhari ya zama shugaban kasa, ba mu sake jin an kashe shuwagabanni ba kamar irin yanda ta taba faruwa ga Bola Ige, Marshal Harry, Aminosari Dikibo da sauran su ba. Har yanzu wannan abun bai gushe a kwakwalen ‘yan Najeriya ba. Maganar wai kuma a ce ‘yan majalisa hudu sun tsige gwamna, wannan kam ba yanzu ba sai da a da. Sanann da a ce zaben 2019 da aka yi lokacin mulkin gwamnatocin baya ne, to da an murda sakamakon zaben jihohin Adamawa, Bauchi da Oyo domin jam’iya mai ci. Da kuma jihohin Kuros riba da Akwa’ibom sun zama jihohin APC ko ta halin kaka.

A kokarin shugaban kasa Buhari na sauya Najeriya da barin kyakyywan tarihi a karshen mulkinsa, ya kamata ya yi nazarin ta natsu ga wani abu da ke addabar kasar wato matsalar tsaro ciki har da matsalar barayin shanu da garkuwa da mutane. Akwai bukatar ya dauki matakan da ya dauka wurin maganin Boko Haram a kan matsalar tsaron da ke addabar kasar a yanzu. Lalle yanzu ne shugaban kasar ya kamata ya yi wannan ba tare da wani bata lokaci ba, lalle da bukatar Buhari ya kawo karshen matsalar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: