Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Bindiga Su Kashe Wani Mafarauci A Ekiti

Published

on

A daran Juma’a ce, wasu danda a ke kyautata zaton makiyaya ne, su ka harbe Emmanuel Ilori, a wata gona da ke yankin Orin Ekiti cikin karamar hukumar Ido/Osi ta Jihar Ekiti. An bayyana cewa, Ilori ya na cikin yin fararautar dabbobin tare da abokinsa a daji, lokacin da lamarin ya afku a tsakiyar daren ranar Juma’a.

Wani mafarauci wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa mai suna Mista Adeniyi Ajayi, ya bayyana cewa, mafarautar sun hadu da makiyaya wanda yawan su ya kai guda 30, a tsohuwar gonad a ke bayan garin. Ya kara da cewa, “lokacin da mu ka yi yunkurin bayyana musu abinda mu ke yi a wannan gona, sai makiyayen su ka fara harbin mu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Ilo. “Su dai makiyayen masu garkuwa da mutane ne, wadanda su ka mayar da dajin a matsayin maboyarsu.”

Ya kara da cewa, jami’an tsaro sun zo sun dauki gawar mafaraucin, domin gudanar da bincike.

Zanga-zanya ya barke a yankin Orin Ekiti ranar Asabar lokacin da a ka samu labarin mutuwar mamacin. Masu zanga-zangar sun gudanar da kone-kone a cikin garin, sun bukaci gwamnatin Jihar Ekiti da ta gudanar da bincike kan wannan kisa tare da zakolo masu hannu a cikin, domin a hukunta su.

Basaraken garin, Cif Francis Falua, ya bayyana cewa, a shekarar ta da ta gabata, wadansu wadanda a ke kyautata zaton makiyaya wne, sun kashe wata mata mai guna biyu, ya bukaci gwamnan jihar Kayode Fayemi, da ya dauki matakin gaggawa a kan lamarin, kafin lamarin ya turzura. Falua ya kara da cewa, “Makiyaya sun dade su na farmakin mamoma a yankin, inda su ke tura dabbobinsu cikin gonar mutane tare da cinye musu amfanin gona.”

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Ekiti, DSP Caleb Ikechukwu, ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya bayyana cewa, ‘yan sanda sun kaddamar da farautar duk wadanda ke da hannu a cikin lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: