Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Cafke ’Yan Fashi Biyu A Kalaba

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Kuros Ribas, ta samu nasarar cafke wasu mutum biyu, wadanda a ke zargin ‘yan fashi da makami ne a garin Kalaba ta kudu, lokacin su ka kai wani samame a ranar Juma’a. Da ta ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a wayar salula, kakakin rundunar ‘yan sanda DSP Irene Ugbo, ta tabbatar da wannan kame. Ta bayyana cewa, ‘yar sanda daga yankin Efut ne, su ka samu nasarar cafke wadanda a ke zargin. Ugbo ba ta bai bayyana sunayen wadanda a ke zargin ba, ta kara da cewa, an mika lamarin ga shalkwatar ‘yan sanda ta jaihar, domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Ta ce, rundunar ‘yan sandar jihar ta dauki kwararan matakai a kan masu aikata ta’addanci a cikin jihar, rundunar za ta gurfanar da duk wanda a ka cafke da laifin ta’addanci a cikin jihar. “Mun fara gudanar da irin wannan lamari a yankin Kalaba ta kudu. Tawagar ‘yan sanda daga yankin Efut ta samu nasarar cafke mutum biyu wadanda a ke zargi, lokacin da su ke gudanar da sintiri  a yankin. An samu nasarar kwato karamar bindiga kirar gida daga hannun wadanda a ke zargi, sannan an mika lamarin ga shalkwatan ‘yan sandar jihar, domin gudanar da cikakken bincike,” in ji ta.

Irene ta bukaci mazauna jihar da su dunga taimaka wa ‘yan sanda da bayanai wadanda zai kai ga cafke masu laifi.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: