Connect with us

TATTAUNAWA

Dokar Wa’azi: Gwamnatin Kaduna Ta Sa Kur’ani Da Baibil A Gaba – Rabaran G. Badiron

Published

on

Tun lokacin da gwamnatin jihar Kaduna ta motsa domin samo mafita ga matsaloli ga matsalolin tsaro da suke addabar jihar, ta kuduri samar da dokokin da sai an bi su, duk wani mai wa’azi a na Musulunci da kuma na Kirista za su bi, kafin su fara yin wa’azi, a duk inda aka sa ba.

Kan haka wakilinmu, BALARABE ABDULLAHI, ya sami damar tattaunawa da RABARAN ISAAC G. BADIRO, Fasto na First Baftist Cgurch, a Sabon garin Zariya da ke jihar Kaduna, inda ya sami damar tattaunawa da shi, kan wannan yunkuri da gwamnatin jihar Kaduna ke kan yi a halin yanzu, Ga yadda tattaunawar ta kasance da Rebaran Isaac.

Ya ka dubi yunkurin da gwamnatin jihar Kaduna ke yin a samar da dokokin da za a gindiya wa ma su wa’azi a fadin jihar?

Wannan dokar zan ce ba sabuwa ba ce,domin a shekara ta 2016, mun tattaunawa da kai inda na ba gwamnan jihar KadunaMalam Nasir Ahmed El-Rufai shawarar da lallai ya cire hannunsa a duk wani abu da ya shafi addini, na Musulunci ko kuma day a shafi addinin Kirista. Na kuma shawarce da ya fuskanci siyasa da kuma ayyukan da za su zama silar cigaban jihar Kaduna, a kuma gina mutane, a wancan lokaci, na ce ma sa batun addini ba na sa ba ne,domin a karkashin addini ne aka zabe shi matsayin gwamna ba.

To, su wanene ya kamata su yi Magana kan addini?

Duk wani batu da ya shafi addini, wannan bangare na malamai ne gabadaya, ba na ‘yan siyasa ba ne, mu ne (malaman Kirista da malaman Musulunci) Allah ya ba mu dama tare da umurni da mu yi wak addini aiki, bisa tsare – tsare da kuma dokokin da suke a littafi mai tsarki, wato Bayibul da kuma littafi mai tsarki, Alkur’ani mai girma, kuma su ne Allah ya kira ya ce su lura da siyasa mu kuma mu lura da addini, kamar yadda mu ke yi dare da kuma rana.

Amma tun da su an zabe su ne a karkashin siyasa, to sais u tsaya matsayin da Allah ya ajiye su, ka da su yi shisshigi ga wani bangare na rayuwa da ba su san komi a wannan sashi ba.Domin in malamai suka gaza ko kuma suka sa son rai wajen sauke nauyin da aka dora ma su, Allah ba zai tambaye su ba.

Kuma da malamai na Kirista da na Musulunci, sun rike aikin da Allah ya ba su da hannu biyu, babu wani dan siyasa da zai sami damar yi ma su katsalandan ko kuma shisshigi a cikin ayyukan da suka shafi addinin Kirista ko kuma addinin Musulunci, a nan sai mu fahimci, bangon fa ya tsage, shi ya sa kadangare ya sami inda ya labe.

A lokacin da gwamnati ta yunkura domin wannan batu na dokar, wasunku daga malaman Kirista da na Musulunci, sun yaba, me za ka ce?

Ai rayuwa ken an, duk abin da aka yi wasu komi bacinsa, za su yaba, kuma komi kyawunsa, za su yi suka, amma, abin tambaya shi ne, sun yi yabon ko kuma sukan domin Allah ba, sun yabo ne domin wasu dalilai na su da bai shafi addini ba.Amma sai muyi tambaya daya, ayyukan addini na ‘yan siyasa ne ko kuma na masana addini ne? A nan ka san amsar a bayyane ta ke, na masana addini ne, ba na ‘yan siyasa ba.

Wasu na ganin ya dace gwamnatin jihar Kaduna ta kafa kwamitin da zai samar da wadannan dokoki da ta ke son samar wa, amma a sa masana addinin Musulunci da masana addinin Kirista da kuma masana shari’a a cikin kwamitin, sais u su samar da dokokin da gwamnati ke bukata, ka yadda da wannan shawarar?

Ba ma kafa wasu sabbin dokoki ba, ko kuma kafa wani kwamiti, dokokin da mu ke da su a Nijeriya kan addini ya fi dubu daya, sun sami kwanciyar hankali a tsakaninmu? Maimako a kara samar da wasu dokoikin, sai a yi karatun baya, domin a gane karatu na gaba. Kuma wadanda ka ce a sa su a cikin kwamitin, sun san Allah? suna yin ayyukansu domin Allah ne? sun a tsoron Allah? sun manta da manyan litattafanmu biyu ne  wato Bayibul da Alkur’ani?

A matsayin ka na babban mai yada bishara a cikin addinin Kirista, ina mafitar matsalolin da gwamnatin da gwamnatin jihar Kaduna ke son samu, na kawo karshen matsalolin da ake kira na addininko ko kuma na kabilanci a wasu sassan jihar?

A mafitar daya, gwamnati na sa Bayibul da Alkur’ani a gabanta, domin duk wasu dokoki da suka shafi mabiya addinin Kirista, ya na cikin littafi mai tsarki, wato Bayibul, in kuma dokokin day a shafi mabiya addinin Musulunci ne, ya na cikin Alkur’ani mai girma, in gwamnatin jihar Kaduna ta sa wadannan litattafai biyu a gabanta ta kuma sami malamai daga addinan biyu, da suka san Allah, suke aiki kuma domin Allah kuma suke tsoron Allah, za a sami mafita ga matsalolin da suka gwamnatin jihar Kaduna ta yunkura, domin samar da wadannan dokoki ga ma su wa’azi a fadin jiha.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: