Connect with us

ADABI

Tarin Kurakurai A Littafin Halayyar Zamani (2)

Published

on

A ci gaba da zakulo kura-kuran da suke jibge a littafin ‘Halayyar Zamani’ za a ga inda marubuciyar ta bayyana a shafi na 95 cewa Anti Zainab da mijinta sun kawo mata ziyara a makaranta har ta na shiga da su cikin hostel din su, shin a jami’ar Danfodiyo maza suna shiga hostel din mata? Wannan mai karatu zai so karin bayani.

Sannan haka kawai a shafi na 96 marubuciyar ta nemi yin wasa da hankalin mai karatu inda ta ce an yi wa wata mai suna Maryam fyade lokacin da ta fita an so hand-out cikin dare wani hostel, abin tambaya a nan shi ne; a ina aka yi fyaden, shin Maryam hostel din maza ta je ko na mata, sannan ina jami’an tsaron jami’ar Danfodiyon su ke?

A shafi na 103 marubuciyar ta yi gugar zanar bayyana jami’ar karatu a matsayin farfajiyar zama kara zube babu doka, inda ta ce wasu gungun matasa sun yi wa wata yarinya fyade a cikin Jami’ar kuma har da hura usur don sauran su bayyana, ko ina mawallafiyar ta boye masu gadin jami’ar har suka kasa bayar da cikakken tsaro ga dalibai?

Idan mu ka shiga cikin shafi na 110 kuwa muka dan tsakuro nan wurin: “Bayan an sa ta a makara na dauko kur’ani  izufi sittin na durkusa a gabanta na fara daga Bakara sanda na kai Suratul Maryam sannan na fara jero addu’o’i….” Kokwanton da wannan manazarcin ya ke yi anya marubuciyar ta san hizifi nawa ne daga Bakara zuwa suratul Maryam kuwa? Ko tana nufin sai an jira Fatima ta yi wa gawar takwararta tilawa sannan za a sallace ta? Ko kuwa karatun yaya Mustafa masu jiran a fito da gawa za su tsaya saurara?

Kafin in ci gaba da lulawa cikin littafi na biyu, ya kamata makarancin wannan sharhin ya fahimci cewa ba luguden littafin ake yi ba kamar yadda na bayyana tun a farko, a’a hasalima marubucin ya yi alimbon fitar da wake a cikin garin masara, sannan bugu da kari manufar wannan sharhi don a samu gyara a wallafe-wallafen marubuciyar nan gaba, wannan ke nan.

Tun daga farkon littafi na daya har zuwa karshen na biyu, manazarcin littafin zai kasa fahimtar irin Hausar da marubuciyar ta yi amfani da ita, domin sun yi hannun riga nesa ba kusa ba da daidaitacciyar Hausa, kuma ba ta yi kama da Hausar Kano, Katsina, Sokoto ko Zariya ba, sannan ba za a kira ta da Hausar Zamfarawa ko Hadejawa ba, ba kuma za a kira ta da Hausar gidan asharalle ba.  Kodayake ilimi kogi ne ba mu sani ba ko wata karbabbiyar Hausar ta bayyana!

A cikin shafi na 114 sabuwar marubuciyar ta ce bayan bikin kawarta Rukayya wadda aka kai unguwar Rimi cikin birnin Kaduna, da wata biyu sakamakon jarabawarsu ya fito, aka sa ranar da za a yaye su a jami’a, sannan za a rarraba kyautuka ga wadanda suka yi kokari, sannan a fadi inda aka tura su zuwa bautar kasa. Shin da ma haka ake yi da sakamakon jarabawa ya fito sai makaranta ta tura mutum bautar kasa?

A shafi na 115 kuwa marubuciyar ta yi kokarin saka jarumar yin kida bashi, ko wuce makadi da rawa, inda ta ce wa Anti Zee lokacin da ta ke amsa wayar ta cewa su yi wa tsohon hukunci daidai da shi, ka da su rage mishi. A matsayin Anti Zee lauya shin ita ce ke da alhakin yanke hukunci ko alkali?

Duk a cikin tarin kura-kuran da suke jibge a cikin sabon littafin, za a ga wuraren da marubuciyar ta yawaita maimaita wannan maganar a cikin shafuka mabanbanta: “Wa’inda suke cewa sai da hadin kan mace ake mata fyade, su kuma kananan yara da ake musu su ma da hadin kansu ne?

A cikin shafi na 117 marubuciyar ta kasa bayyana kwanakin da su Fatima da yaya Mustafa suka yi a Zariya da Makarfi sai dai kawai mai karatu ya ji cewa za ta koma wurin aikin bautar kasar ta can Adamawa.

A shafi na 123 kuwa marubuciyar ta bayyana Fatima ta na off, ma’ana ta na jinin al’ada, kusan har tsawon wata biyu kamar yadda ta nunawa sabon angonta. Kawai sai marubuciyar ta kasa nunawa mai karatu yadda angon nata ya nuna damuwarsa a cikin kwanaki sittin suna kwana gida daya, kuma Mustafa ya kasa nusar da ita zuwa ga asibiti don duba lafiyarta.

Fa’iza S. Muhammad a cikin littafin nata ta  yawaita nuna Yaya Mustafa zai zo Najeriya akan dalilin da bai taka kara ya karya ba a cikin ‘yan awannin da aka sanar da shi wani al’amari ba tare da bayar da uzurin kwana daya zuwa biyu ba.

Mawallafiyar ta ce matasa suka yi wa Danliti dukan tsiya cikin dare kuma suka yanke gaban shi a shafi na 131, can a shafi na 147 kuma marubuciyar ta nuna cewa wasu matasa sun kama Danliti a cikin wani kango suka yi mishi duka sannan suka kwakule mishi idanuwa da kuma wasu sassa na jikin sa. Shin marubuciyar ta na nufin duk lokacin da Danliti ya dauka ba tare da gaba ba, ya ci gaba jinyar kansa a haka ba tare da ya mutu ba?

Tun daga farkon labarin da Fatima ta ke ba Maryam har zuwa karshe babu inda marubuciyar ta yi kokarin nunawa mai karatu yadda Maryam ke ji yayin da ake ba ta labarin, musamman halin tausayi, mamaki, jin haushi ko razana bare kuma har a nuna Maryam ta yi wa Fatima tambaya.

Idan muka leka shafi na 140 zamu ga yadda marubuciyar ta yi riga malam shiga masallaci, inda ta yi saurin bayyanawa mai karatu dalilin da ya sa Mustafa mijin Fatima ke fushi da ita bayan bai fada mata dalilin ba.

A shafi na 146 kuwa mawallafiyar ta ce Inna Jummai ta samu hatsari wanda hakan ne ya yi sanadiyyar yanke kafafuwanta, daga bisani kuma mijin ya yi mata saki uku. To mai karatu zai so sanin wurin da Fatima suka hadu da ita a karshe har take yi mata alheri?

Nazartar littafin tun daga farko har zuwa karshen sa, mai karatu zai ga babu inda marubuciyar ta ambaci sunan kasar da Mustafa mijin Fatima ya ke aiki.

Kurun-gus ma kawai!  A gaskiyar zance littafin Halayyar Zamani da marubuciyar ta radawa suna ko kadan bai ci sunan shi ba, littafin ya saki linzamin shi tun farkon farawa.

Da karshen wannan sharhi, nake son in yi amfani da wannan dama don godiya da nuna farin ciki ga wannan marubuciyar, musamman yadda ta nuna kishin ta ga kungiyar marubuta Alkalam ta jihar Kaduna, wajen kin sanya tambarin kungiyar da kuma ambaton sunan kungiyar tun daga bangon littafin har zuwa karshen sa, (kamar yadda yawancin ‘ya’yan kungiyar suke yi) wala’alla ta yi hakan ne don kar a dora alhakin kwamacalar da ke cikin littafin ga mahukunta da manyan marubutan da suka dade suna yi wa adabin Hausa hidima irin su Halima K/Mashi, Asma’u Lamido mai ‘Ya’yan Safara da su Hajiya Fatima Yusuf Muhammad wadda a sani na ta na da kwarewa wajen shirya rubutun azanci mai cike da ilimi da balaga tare da tsantsar nahawun Hausa.

Har zan rufe sharhi na ban mika tambaya ta ga wannan marubuciyar ba, shin tarin takardun da suke kasuwa da sunan a sayarwa masu karatu za a dawo da su gida ne a yi gyara ko kuwa haka masu karatu za su kama kwasa, daga bisani su koma yin da-na-sanin fansar su akan naira dari uku? Ko kuwa marubuciyar za ta kalli matsayin ta ne a daya daga cikin mambobin kungiyar Alkalam da mutane suke yi wa kallon shahararru a fagen tsara labarin hikaya don fitar da kungiyar kunyar kishiya ko kuwa?

Sani Ahmad Giwa

[email protected]

www.mysanigiwa.blogspot.com

08169701410
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: