Connect with us

TATTAUNAWA

Fatanmu Mu Ga Manoman Mu Suna Girbi Sau Uku A Watanni 12 – Hon. Aminu Ahmad

Published

on

HON. AMINU AHMAD shi ne zababben dan majalisar Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Makarfi a cikin majalisar. Cikin wannan zantawan da ya yi da LERDERSHIP A YAU bayan rantsar da su ya yi bayani ne a kan wasu daga cikin manufofinsa da ya shigo majalisar da su. wakilinmu Umar A Hunkuyi ne ya zanta da shi. A sha karatu lafiya:

Honorabul da shi ke masu zabe sun zabe ku ne domin neman canji da kuma ci gaba a cikin al’amurran rayuwarsu na yau da kullum, ba mu san wadanne irin manufofi ne kai ka shigo wannan majalisar da su ba, da kuma fatanka na ganin wannan majalisar ta taimaki wannan al’ummar?

To Assalamu alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu, Manufofi su ya kamata a kalla na duk wani wanda yake takaran wata kujera, ko kuma a kalli manufofin jam’iyyarsa, inda za a yi la’akari da su a matsayin dalilin da zai sanya a zabe shi, ba abokin takaransa ba. Domin manufofi su ne kashin bayan tafiyan kowane mutum, ko jam’iyya.

Tabbas jam’iyyarmu ta APC tana da manufofi manya da kanana, cikin manyan manufofin jam’iyyarmu kamar yanda ake ta bayani, akwai batun sha’anin tsaro, akwai kuma batun cin hanci da rashawa, wanda shi ma abu ne da ya gallabi kowa da kowa, akwai maganan rashin aikin yi, wanda shi ma akwai, ga shi nan maza da mata sun kammala karatu ga su nan a jibge babu aikin yi. Sannan sana’o’i sun karanta, ga masana’antu nan duk an rurrufe kila saboda rashin jari, watakila saboda karayar tattalin arziki wanda ya shafi Duniya baki-daya.

Wannan yana daga cikin abin da ya damu duk dan jam’iyyar APC, kamar yanda shugabanmu Buhari da ma gwamnoninmu suke kara nanatawa, wannan abin da suka sanya a gaba kenan na ganin an shawo kansu, an ma fara shawo kan na su. tabbas an sami nasarori masu tarin yawa, amma har yanzun akwai kalubale masu yawa da suke fuskantar mu. Mun kuma sha alwashin ci gaba da fuskantar na su, cikin yardan Allah sai mun shawo kan wadannan masifun, sai mun karya lagonsu, sai mun dawo da zaman lafiya a wannan kasa tamu, sai mun yaki cin hanci da rashawa, mutane za a sama masu sana’o’i da ayyukan yi yanda ya kamata, za a inganta ayyukan gona da duk makamantan su. Wadannan dai su ne kashin bayan ayyukan da muka sanya a gaba tun daga jam’iyyata da ni kaina, wannan shi ne tunani na ga al’ummata da mazabata, su ne kuma abubuwan da za mu mayar da hankali a kansu da fatan samun nasara in Allah Ya so.

To da yake ka kawo maganan aikin noma, kuma sani na ne al’ummar da kake wakilta sama da kashi casa’in duk manoman ne, akwai wani tanadi ne na musamman da kake yi masu na ganin ka bunkasa sana’r noman na su?

Ko mutum ya so, ko ya ki, aikin noma shi ne kashin bayan tattalin arzikinmu, Mai da ake ta fariya da shi, a halin yanzun zamani ya fara nuna mana cewa ba fa abu ne wanda za a iya ci gaba da dogaro da shi ba, sabanin aikin noma abinci, wanda matukar akwai halitta a bayan kasa to abinci kuwa tilas ne. A halin yanzun mafiya yawan mutanan mu sukan noma dan abin da za su ci ne, sai kuma dan abin da ya ragu su sayar su yi wasu bukatun su na yau da kullum.

To ka ga ashe kenan duk wanda ya san abin da yake yi tilas ne ya nemi hanyar da zai bunkasa wannan, don haka, a maimakon noman damina da muke yi kadai, za mu mayar da hankali kan noman rani. Dangane da wannan dole mu je mu tona rijiyoyi mu samar da madatsun ruwa yanda ruwan damina zai rika gangarewa zuwa madatsun nan ta yanda za mu iya yin amfani da shi a lokacin rani wajen noman ranin. Dabbobi su sha ruwan mu kuma yi noman rani da ruwan, a bunkasa aikin noman rani da damina. Ya zamana a ce manomi zai sami daman yin girbi akalla sau uku a cikin watanni 12. In Allah Ya so sai ka ga tattalin arziki ya inganta kasa ta habaka, domin muna ganin bambanci a tsakanin inda suke yin noman rani da kuma inda ba sa yi. Arzikinsu ba daya ne ba, ba za ka iya hada wanda yake yin girbi sau uku cikin shekara da wanda yake yin girbi sau guda a cikin shekarar daya ba.

Yanzun ga taki nan Alhamdulillah an samar da shi, a halin yanzun za ka iya zuwa kasuwa ka saya ba tare da wata matsala ba, dan gwamnati a kan dubu biyar da dan wani abu, wanda za ka amfana da shi. Muna kuma sane da kalubalen da ke fuskantar aikin gonan masu yawa, misali kamar na rashin tsadar kayayyakin amfanin gonan, wannan kuma lamari ne wanda tilas gwamnati za ta shigo ciki, in ya kama a saya ne sai a saya a kan farashin da manomi ba zai fadi ba. Wannan kuma duk kadan ne daga cikin abubuwan da za mu duba tare da shawarwarin kwararru a kan aikin gona domin lalubo hanyoyin da za mu kara inganta sana’ar mutanan mu in Allah Ya so.

A karshe wane kira ka ke da shi ga mutanan da su ka zabo ka zuwa cikin wannan majalisar?

Kamar dai yanda muke fadi har kullum, muna kara godiya a bisa amincewar da suka yi da mu, sun yi imanin cewa za mu yi masu wakilci ne na gaskiya har suka ba mu dama, muna masu godiya a bisa wannan amincewar da su ka yi ma na, mu na kuma neman karin goyon baya ta hanyar gaya mana gaskiya, ta hanayar ba mu shawarwari nagari ta hanyar kira a garemu a duk inda muka nemi mu kauce, ta hanyar janyo hankulanmu domin mu yi masu wakilci nagari ta yanda za mu ci nasara baki-daya, domin nasara ake nema ba faduwa ake nema ba. Domin in mun ci nasara, dukkaninmu ne muka yi nasara, mazabarmu, Jihar mu kasarmu ce ta yi nasara, nasara ba ta mutum daya ba ce. Hakanan in aka fadi kuma tare ne aka fadi, saboda gwamnati ita ce jama’a, jama’a su ne gwamnati, dole a hada kai gabaki-daya domin a sami nasara.

Muna neman irin wannan hadin kan, da goyon baya da shawarwari da kuma addu’a, da fatan Allah Ya yi ma na jagora.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: