Connect with us

TATTAUNAWA

Mu Na Goyon Bayan Shirin Buhari Na Samar Da Rugar Fulani – Dr. Bature Abdul’azeez

Published

on

Wannan wata tattaunawa ce da MUHAMMAD ABUBAKAR ya yi da shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar Nijeriya, DR. BATURE ABDUL’AZEEZ dangane da batun shirin gwamnati na samar da Rugar Fulani a tarayyar Nijeriya. Shugaban na ‘yan kasuwa ya tabo batutuwa masu muhimmancin gaske, ga yadda hirar ta kasance:

Me za ka ce dangane da shirin Buhari na samar da Rugar Fulani?

A madadin ‘yan kasuwar Nijeriya a karkashin kungiyar ‘National Harmonies traders union’ muna goyon bayan kudurin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan shirin samar da Rugar Fulani a jihohi 36 na tarayyar Nijeriya. Wannan shiri ya yi kyau, ya yi daidai. Kuma duk wani dan kishin kasa, mai son zaman lafiyan Nijeriya, ina ga wannan shawarar ta yi daidai da a yi wurin kiwo na Fulani makiyaya a Nijeriya.

Nijeriya kasa ce ta mu, wacce take Allah ya hada zamanmu da dukkan kabilu daban-daban, da dukkan addinai daban-daban, da sana’o’I daban daban, ga dai su nan. Allah ya hada mu wuri daya, saboda haka babu yadda za mu yi da junanmu illa yin hakuri da juna, mu yi kyakkyawan tunani da kyakkyawan zato.

Shin Rugar Fulanin na da amfani ne ga sauran jama’a banda makiyaya?

Su Fulani da a ke tunanin za a samar musu da ruga, wannan zai takaita fada a tsakaninsu da ainihin manoma, domin wannan sabani ya kunno kai ne a tsakaninsu, shi ne a hankali yake girma har ya zama cewa yana neman ya haddasa fadan kabilanci a wannan kasa tamu mai albarka. Toh alhamdulillahi, tunda Allah ya sa za a makiyaya a kowacce jiha, toh ni ina ganin su ba Shugaban kasa hadin kai, domin shanun nan ai ba gwamnati ce kadai take cin shanu ba, ba arewa kadai ta ke cin shanu ba. Shanun nan ai duk abincinmu ne gabadaya ‘yan Nijeriya, ai mu mun fi murna da a ci Shanu kan a cinye mana Jakai.

Ya za a yi a ce Bafulatani duk inda ya dafa a wadansu jihohin za a fito a na nuna ko Shugaban kasa ya yarda za a yi Rugar Fulani su ba za su aminta ba. Ba za a yi musu wurin kiwo a jiharsu ba. Wadannan mutane suna bamu mamaki, wadannan mutane muna ganinsu ba su da tunani. Idan ma suna da tunani toh tunanin kawunansu kawai da bukatarsu suke yi.

Yin Makiyaya, wurin kiwo ai ba za ta cutar da kowa komai ba, kuma wani arziki ne a ka kusanto da shi, kusa-kusa da jama’a, kuma fadace-fadace da a ke yin a samun sabani tunda ance, Fulani suna cinye abincin gonakin mutane, idan a ka kebe su ai za su yi abin da a ke so, kuma za su tsaya a inda suke, kuma za a kafa dokoki masu karfi muddin za a yi wurin kiwo na kirki, inda shanu za su ci ciyawa, su sha ruwa ba zai yanke ba. Inda zai zama gwamnatin tarayya a kowacce rugar Fulani za ta tanadar musu tiractoci da iri na ciyawa kamar yadda a ke a Turai.

A raba fili uku, ciyawa ta fito, su fara cin ta farko, kafin su cinye wata ta sake fitowa a ta biyu, haka har ta uku. Saboda haka a nan gwamnatin tarayya ta yi daidai, wannan shi ke nuna tana adalci ga ‘yan Nijeriya, kuma shi ke nuna tana adalci madaidaici tsakanin wannan bangare da wancan bangare. Tsakanin wannan kabila da wannan kabila. Kuma ba shakka gwamnati ta damu kwarai da fadace-fadacen da a ke yi.

Wannan ya sa wasu daga cikin gwamnoni sai suke fitowa suna nuna kyamarsu zahiri a kan wannan, kuma ba su da wata hujja sai siyasa, saboda siyasa suke son kunna fitintinu iri daban-daban wanda zai shafi ainihin manoma da Fulani, wanda wannan yak an janyowa kasar tamu koma baya. Ni ina ganin wannan zai kawo karshen fadace-fadace.

Kuma shugaban kasa ya fito fili ya nuna da gaske yake yi, duk wani gwamna da yake nuna cewa shi bai yarda ba, toh ya san fa Nijeriya fa, ai zaman hakuri a ke yi, idan ba a zaman hakuri ai wadansu ba za su zo su mamaye harkokin wasu ba. Idan za kai lissafi, wadanda duk suke maganganu kan wai su ba su yarda ba, za ka gansu mutane ne na Jihar gabashin kasar nan, jihar gabashin kasar nan, idan za mu duba irin yadda suka mamaye harkokin kasuwanci a gabakidaya kasar nan, za mu duba ai ‘yan kasuwa za mu yi kukan cewa, mu a bangaren yamma da bangaren arewacin Nijeriya gabadaya mun zama ‘yan kallo, domin idan da za ka kula, wuraren da suka mamaye harkokin kasuwanci, musamman daga inda Fulanin nan suka fito wato Arewa, idan ka kula, za ka ga kaso 70% na kasuwanci za ka ga sune.

Kuma batun cewa mutanenmu na fama da talauci, ai mamaye harkokin kasuwanci da wadancan mutanen suka yi shi ne ya kara tabbatar da batun talaucin mutanenmu. Amma duk da wannan, su mutanen kudancin kasar nan da suke zaune a jihohin da Fulani suka fito ai ba a wani tunanin a tada hankalinsu, ko a nuna su ba ‘yan jiha bane, domin ‘yan kasa ne, su ‘yan Nijeriya ne, saboda dokar kasa ta aminta ga dukkan dan kasa da ya zagaye ko ina ya je ya yi sana’a muddin halastacciya ce. Ko ina gida ne.

Kuma babu shakka wadanda suke ‘yan asalin gabar mazauna inda Fulanin nan suka fito, su za su bayar da cikakkiyar shaidar cewar a nan babu tsana, babu kyara, babu tsangwama, suna zaune lafiya fiye da garuruwansu. Amma sai ga shi wasu daga cikinsu da basu da kishin kasa, daga shugabanninsu da sauransu kullum basu da wani abu illa cewar su basu yarda da wani abu daga arewa ba, ko ba su yarda da wani abu na Musulmi ba, sun manta a arewa muna zaune lafiya da kiristoci da sauransu. Amma tunda dan atrewa ya yarda cewa kasa daya ce, babu wata kyama, babu wata tsangwama.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: