Connect with us

LABARAI

Al’ummar Karamar Hukumar Makarfin Jihar Kaduna Sun Yaba Wa Shugabansu

Published

on

 

Al’ummar Karamar Hukumar Makarfi su sun yi nisa da fara shaidawa da romon damukuradiyya karkashin mulkin shugaban karamar hukumar tasu wato Injiniya Kabiru Mu’azu Mayare..
Bincike da wannan Wakilinmu ya yi a wannan lokacin ya fara ne da tabo abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a kai tsaye.
Tarihi ya nuna cewa babu wani cigaban rayuwa da zaka kirashi da sunan ci gaba ba face ka sako harkar Ilmi ba.
Sai abu na biyu shi ne harkar kiwon lafiya. Sai abu na uku shine kula da rayuka da dukiyukin jama’a to in har al’uma ta sami wadannan abu guda uku to sauran sukan zama masu sauki.
Hakan ya sa wakilinmu ya binciki harkar ilmi a wannan karamar hukumar ta Makarfi inda aka sami tabbacin gine gine da gyare gyare da zuba kujeru da kwakwkwafa matsalolin malaman makaranta da daukar nauyin dalubai zuwa maiyan makarantu lamarin sai wanda yaje ya gani don jama’ar karamar hukumar yabo kaiwai suke da fatan gamawa lafiya ga shugaban nasu.
Harkar lafiya kuwa tuni kananan asibitoci suka amfana da abubuwa da dama don takaita wahalhalu da ake samu a baya wajan haihuwa da bayar da tallafi ga marasa lafiya.
Maganar tsaro kuwa mai girama shugaban karamar hukumar ta Makarfi har ya sayo motoci don baiwa jami’an tsaro don karfafa har kar kula da rayuka da dukiyoyin jama’ar sa.
Harkar ci gaban gari kuwa da yawa daga cikin yankuna da ke karkashin shugaban an ja masu wutar lantarki.
Bugu da kari akwai aiyukan da suka hada da gina kwalbatoci a wasu yankuna.
Ya zuwa yanzu dai biciken ya nuna cewa jama’ar karamar hukumar Makarfi fatan alkairi ga shugaban karamar hukumar bisa namijin kokarin da yake yi a bangarorin da suka dane suna kuka a kansa.
Hakan ya sa Wakilinmu ya zanta da daya daga cikin jama’ar karamar hukumar kuma fitaccen matashi a garin makarfi mai suna Abdullahi Ibrahim game da ci gaban da aka samu a yankin nasu da kuma kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu.
Malam Abullahi ya fara da godiya da Allah ya masu shugaba mai kishin jama’arsa gida da waje.
Kuma matashin ya yi yabo akan dukan bangarorin da shugaban ya taba kamar harkar ilmi da lafiya da tsaro yace, a gaskiya sai godiya ga Allah.
Matashin ya karkare da janyo hankalin shugaban da cewa Wajibi ya kara dagewa akan aikin da yasa a gaba don hakan shi zai kaisa samun nasara a nan gaba da ikon Allah.
Kuma ya ce kada ya damu da sukar ‘yan adawa mai gaskiya yana tare da Allah.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar ta makarfin honorabul Injiniya Kabiru Mu’azu Mayare akan ko me ya janyo hankalinsa ga dukufa wajan cikawa jama’arsa alkawarin da ya yi masu?
Sai Injiniya ya kada baki ya ce,” Cika alkawsri ga jama’arsa ya zama Wajibi a gareni don sun cikamin wanda suka daukar min shiyasa nima nake cika masu wanda na daukar masu nima kuma wannan aikin da aka fara somin tabi ne damar zasuba jambiyar APC goyon baya”.
Shugaban ya jinjinawa mai girma gwamnan jihar Kaduna Malam Ahmed Nasiru El Rufai bisa gudummawar da yake basu na tabbatar da sun gudanar da shugabanci na gari.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!