Connect with us

MAKALAR YAU

Yadda Dalibi Zai Magance Kasala A Lokacin Daukar Karatu A Makaranta

Published

on

Ganin cewa al`umma a wannan zamanin walau a karkara take ko a birni, tana ba da muhimmanci ga neman ilimi, daidai iya karfinta, yana da matukar muhimmancin gaske yaran da ake turawa makaranta ya zamo suna da kyakkyawan jagoranci kan yadda za su samu ilimi mai inganci kuma ya amfane su tare da al`ummar da suke rayuwa a cikinta.

A bisa haka ne, muka yi wa dalibai tsaraba da hanyoyin da za su bi domin kawar da kasala lokacin daukar karatu, wadda kowa ya san cewa kasala tana daya daga cikin abubuwan da suke rusa wad alibi tubalinsa na samun ilimi.

Abu ne mai matukar muhimmanci ga dalibi ya tattaro hankalinsa a lokacin da yake sauraren malami a aji, wanda hakan ne zai taimaka wa dalibi samun kyakkyawan sakamako a karshen kowane zangon karatu. Domin samun nasarar mayar da hankali zuwa ga abin da dalibi ya kamata ya yi a makaranta, akwai bukatar lalle ya yi tunani tare da shagaltuwa da abin da malamai ke kokarin koya masa a aji.

Duk da ba aiki ne mai sauki ba, a wajen wasu dalibai su mayar da hankalinsu ga darussan da ake  koyar musu, musamman a lokacin kosawa, duk da kuma ya saba wa dabi`a malami/malama ya/ta kosa da darasin da zai/za ta koyar- balle kuma ya/ta yi tangadi a lokacin da yake/take bayar da darasin.

Abokina dalibi, kunnen ka nawa! Shin ko kana fuskantar matsalar hallarto da tunaninka a ajin daukar karatu? To karkade kunnuwanka don ka sha labarin yadda za ka shawo kan wannan matsalar taka.

Na farko, ka tabbata ka samu wurin zama daf da malami a aji: Zama a gaban malami a aji; kuna kallon juna, wannan wata hanya ce da za ta saukaka maka wajen tattara hankali da shamaki tsakanin ka da mamayar bacci a aji, wanda kuma ko ba komai kana tsoron ya kalli kana lumsashe ido. Wannan mataki zai taimaka wajen magance maka kasala a lokacin daukar darasi.

Na biyu, ka rinka tambaya tare da bayar da amsoshin wasu tambayoyin da malami ke yi wa dalibai: A wasu lokuta, da zarar an fara darasi a aji, abu ne mai sauki ka fara jin wasu abubuwa masu daukar hankali ko bacci yana neman shiga tsakanin ka da darasin da malamin ku yake koyar da ku. Amma da zaran ka kutsa kai wajen bayar da amsoshin wasu tambayoyin da malam ke wurgowa tare da mika naka, zai taimake ka wajen tattara hankali dangane da yanda darasin ke gudana. Sannan kuma yi kokari wajen rubuta wasu daga cikin muhimman batutuwan da malamin ke magana a kai, kuma ka guji yin surutu ko yin abin da zai dauke maka hankali.

Na uku, idan ka gaji, ba laifi ka dan mike don motsa jininka a cikin ajin: Dogon lokaci dalibi yana sauraron  darasi wani zubin yana kawo gajiya da kosawa. To idan hakan ta faru, ba laifi ka dan mike tsaye tare da dan ware jini, sannan kuma da ace malami zai tambaye ka: me ke faruwa? Za ka iya yi masa/mata bayani a tsanake, kan cewa gabobin ka ne suka dan kage. Malamin zai fahimci cewa kana son ka dan ware ne don samun zarafin ci gaba da daukar karatu.

Na hudu, aiki da dabarun warware gajiya a cikin aji:

Motsa gabobinka a sa’ilin da kake zaune a aji, irin su lankwasa wa ko danna kafar ka a kasa- a hankali, zai taimaki gabban jikin ka wajen ci gaba da aiki tare da samun kariya daga sharrin bacci. Sannan ana son idan za ka yi hakan, ka yi a hankali don kar ka dauki hankalin sauran daliban ajin baki daya.

Na biyar, ka zauna kusa da taga, ko wurin da iska ke shigowa aji: Aji mai karancin magarar iska yana taimaka wa dalibi ya fara jin kasala mai dauke da bacci. Saboda haka yana da kyau ka zauna kusa da taga ko fanka, wanda hakan zai sa ka mori kai-komon iska mai sanyi da rage barazanar kasala da kosawa a lokacin da kake daukar darasi.

Na shida, yi kokari ka samu isasshen bacci da dare- kafin nan: Daya daga cikin matakan da zasu tallafi tunanin ka zuwa abin da ake son ya karkata da shi a aji, shi ne samun isasshen bacci kafin ka shiga aji- saboda masana sun bayyana cewa jikin dan Adam yana bukatar baccin awanni bakwai (7) a kowane daren Allah. Kuma wannan shi ne zai bai wa jiki damar aiwatar da aikin da ya dace da shi. Sannan kuma samun isasshen bacci da dare, kafin tafiya aji daukar darasi, ka ga ka samu hutu tare da saita tunanin ka wajen gudanar da aikin da ya dace; a cikin sauki, wanda zai dakile kutsen baccin aji, a lokacin da malami ke bayar da darasin.

Na bakwai, ka rinka samun isasshen lokacin motsa jiki: Motsa jiki yana taimakawa wajen rage wadansu damuwa, bai wa kafofin jini aiki kamar yadda ya dace, tare da bunkasa aikin kwayoyin halittar kwakwalwa. Gudun safe tare da sassarfa, doguwar tafiya da kafa, gudu na dogon zango da makamantan su, zai taimaka wajen lafiyar jiki a kowane lokaci.

Na takwas, cin abinci mai lafiya tare da shan isasshen ruwa masu tsabta: Yi kokarin samar da hanyoyin da za su kai ga samun abinci mai inganci. Ka nisanci hadidiyar nau’in abinci mai nauyi (Carbohydrates) ko maiko a lokacin da kake shirin shiga ajin karatu, ka al’adanci nau’in abinci mai amfani a jiki (proteins, minerals) kuma masu bunkasa kaifin kwakwalwa da jiki. Kuma kana iya guzurin goran ruwa, a lokacin dogon darasi, sabida gudun mamayar kishirwa.

Abokina, ina tsammanin wadannan shawarwari za su taimake ka wajen magance kasala a aji.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: