Connect with us

Uncategorized

Yadda Kwankwaso Ya Siyasantar Da Harkar Ilimi A Kano

Published

on

Harkar Ilimi ta gamu da tasgaro daga Tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso saboda rikitacciyar siyasarsa kan gurguntaccen tsarin ilimi kyauta wanda ya gabatar a karshen mulkinsa zango na biyu. Tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2015,  wanda ya kirikira kawai domin ya barwa sabuwar Gwamnatin Dakta Abullahi Umar Ganduje jangwangwama.

Ya yinda da ya bar daruruwan abubuwan amfani a bangaren ilimi cikin mummunan yanayi a lungu da sakon  Jihar Kano, bayan da ya yiwa wasu ‘yan Kadan Kwaskwarima wanda suke bakin hanya, ta hanyar yi masu fantin Kwankwasiyya domin masu wucewa su gani ta hanyar  tsarin tallafin karatun kasashen waje wanda ya kirkira a matsayin Gwamnan Kano. Kwankwaso ya ci gaba da amfani da tsarin domin amfanin kansa a siyasance.

Ko shakka babu Kwankwaso na cikin fitattun ‘yan siyasa a Nijeriya wanda har yanzu suke mafarkin kayen da suka sha a zaben da ya gudana na shekara ta 2019. Bawai asarar kujerar Sanata ka dai Kwankwaso ya yi ba wanda Malam Ibrahim Shekara ya rangada da kasa ba, har da kayen da dan gaban goshinsa ya sha a hannun Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje  wanda aka zaba da rinjayen kuri’u masu yawan gaske a zangonsa na biyu wanda al’ummar Kano suka yi masa domin nuna godiyarsu bisa ayyukan cigaban da aka samu ta fuskar jagoranci wanda ya hada da  ilimi alokacin zangonsa na farko.

Duk da kasancewar Kwankwaso a matsayin Sanata, Ganduje ya samu gagarumar nasara kan dan gaban goshin  yaronsa kuma surukinsa  Abba Yusif wanda sakamakon haka  aka rufe shafin mafarkin Kwankwaso  na sake komawa zango na uku zuwa fadar Gwammnatin Kano.

Bayan da ya sha kaye kuma aka kaishi kasa, har yanzu Kwankwaso na na tunanin sake dawo da kimar da a baya yake mafarkinta, amma saboda iya harkalla sai ya aje asusun Kwankwasiyya wanda a halin yanzu ya  kaddamar  da wani tsarin neman tallafi domin wasu zababbun dalibai da ya ware.

Babbar manufarsa bata wuce yin amfani da wannan sabon abinda ya kaddamar ba domin amfanin kansa domin sake samun wani haske a siyasance, Kafin haka, sakamakon matsuwar da ya yi don burge wadanda suka amfana da tallafin karatun tare da iyayensu, a shekarar data gabata Kwankwaso ya shirya wani asusun tallafi domin wadancan daibai da ya yaudara.

‘Yan Kwankwasiyya ne kadai Zasu iya fadar hakikanin abinda akayi da wadancan kudaden da aka tara. Wani zai yi zaton mutane masu muhimmanci, musamman manyan jagororin Kwankwasiyya ne Zsu Halarci gurguntaccen taron da aka gudanar a ranar asabar data gabata domin tattara gudunmawa ga kungiyar. Wannan tasa ‘Yan kungiyar da ake yaudara kuma Kwankwaso ke amfani dasu suka kauracewa taron  sakamakon haka taron bai yi armashi ba.

Abin dariya, babban mai kaddamarwa a lokacin taron wanda ya bayyana gagarumar gudunmawar Naira Miliyon 30 wanda aka hakikance da cewa  na cikin matsaikatan al’umma a Nijeriya wanda har yanzu ke fafutakar neman abin sawa a baka, an bayyana  cikakken sirri  da kuma dalilan  kafa wancan asusu na Kwankwasiyya.

Baki daya, wadanda suka shirya sun bayyana cewar an tara abinda ya kai  Naira  Miliyon 87,727.000.00 a lokacin taron, amma tambayar anan itace, ina wadannan kudade suke kuma ya akayi amfani da su ga wadanda aka shirya abin dominsu? Wannan itace amsar da har yanzu na kasa suka kasa samun amsarta. Kamata ya yi Kwankwaso ya sayar da guda daga cikin gidajensa dake Abuja, Kano,  Dubai,  Egypt ko wanda ke Marocco  domin biyan wadancan daibai ba wai shirya neman tallafi ba.

Kamar yadda wani mai suna Haroun Muhammad wanda ya bayyana kansa amatsayin dan Kwankwasiyya mazaunin Pout-Harcourt wanda ya yi wani  rubutu wanda aka buga a dandalin sadarwa na zamani  Potal  mai taken  Kwankwaso “ The Sage Of Ours And A Legend Of His  Own Time”

A cikin wannan rubutu, Haroun Muhammad ya bada mamaki kwarai da gaske musamman yadda ya kwatantan Kwankwaso da shugabanni irinsu   Marigayi Obafemi Awolowo, Winstom Churchill, Liond Geoge, Kwame Nkruma, Jerry Rawlings, Mahattara Gandhi, Lea Kwan, Kenal Ataturk da sauran wasu masu yawa cikin dogon jerin sunayen da ya lissafto.

Amma dai, Muhammad ya yi rubutun kamar wanda yafi kowa fahimtar karatu wanda kwankwasawan sun makance suna fakamniyyaa kamar wadanda ruwa ya ci, wannan dai shi ne Kwankwason da ake dauka amatsayin uba ga tsarin ilimi Kyauta. Wanda yake gudanar da jami’a mai zaman kanta a Abuja inda dalibai ke biyan abinda ya kai Naira Miliyon 1.5.

A wannan Makaranta babu wani dalibi dan asalin Jihar Kano da yake amfanar ilimi kyauta ko kuma suke samun rangwame kudin makaranta ko tallafin karatun ko da kuwa masu baiwar karatu ne ‘Yan asalin Jihar Kano kowa wani bangare na kasar nan, wannan wa ake yaudara kenan?

Wannan mutumin ne fa ya tabbatar da yadda ya amfana da tsarin ilimi kyauta tu daga matakin firamare  har zuwa Jami’a, amma kawai yana amfani da tallafin karatu zuwa kasashen waje wanda ya kaddamar a lokacin da ya ke matsayin Gwamnan Jihar Kano domin arzurta kansa da makusantansa da sunan daliban da aka tura karatu zuwa kasashen waje, amma sai da wadannan dalibai suka yi nadamar kasancewa cikin wadanda akace sun amfana da wannan tallafi da ake ta yamadidi dasu da niyyar sauya rayuwarsu.

Sakamakon kyakkyawar manufar Gwamna Ganduje  na ci gaba da ayyukan da ya gada, wanda baya ga tulin bashin daliban dake kaaratu a makarantun kasashen waje da aka gadarwa gwamnatinsa, sai da gwamna Ganduje ya tabbatar da ganin ya inganta rayuwar wadannan dalibai  domin ci gaba da karatunsu.

Amfanin ilimin bai daya a matakin kowane karatu bai misaltuwa  idan akayi la’akari da kalubalen da ke tattare da wannan bangare wanda Kwankwaso ya yiwa dibar karan mahaukaciya ta hanyar karkatar da hankulan al’umma kan batun tallafin karatu zuwa kasashen waje. Saboda haka ne Kwankwaso da magoya bayansa suke amfani dashi amatsayin wani bututu da suke zuke lalitar jama’a.

Wannan shi yasa Gwamna Ganduje aka gadar masa da manyan ayyuka a bangaren ilimi, tare da durkusar da sashin ilimi wanda hakan tasa ake samar da gibin wajen rashin samun kyakkyawan sakamako ta fuskar karatu. Wannan tasa kusan dukkan hukumomin ilimi, kama daga firamare, sakandire zuwa Jamai’a dukkan ajujuwansu sun lalace, Babu abubuwan da ake bukata na yau da kullum sun yi karanci.

Daga ranar 29 ga watan mayu  shekara 2015, akwai ajujuwa 25,000 daga cikin 30,000 wanda ake dasu, ya yinda abinda ake bukata a makarantun gwamnati shi ne 3,000,000 wanda ake da ajujuwan 45,000.

Haka kuma akwai ban dakuna 18,000 daga cikin jimlar abinda ake bukata guda 35,000 ya yinda ake da abubuwan zama guda 198,832 daga cikin abinda ake bukata guda 914,000.

Bugu da kari akan haka,  kayan koyo da koyarwa basu wadata ba ya yinda kayan bukatar malamai ya yi karanci kwarai da gaske, haka kuma kusan kaso 50% na malamai ba suda takardar shaidar kwarewa.

Gwamnatin Dakta Abudllahi Umar Ganduje ta yi fice kwarai da gaske ta fusakar samar da ingantattu hanyoyin inganta harkar ilimi domin kawar da irin wancan mummunar hange da ake yiwa harkar. Gwamantin Jihar Kano ta tuntubi gwamnatin tarayya domin samar da tallafin sama da Naira Biliyon 2, wanda Kwankwaso ya ki baiwa muhimmaci.

Wannan ya bada damar gyara  ajujuwa tare da maye gurbin wanda babu su ko suka zama wuraren kiwon dabbobi, an gina dakuna Karatu,  samar da rijiyoyin burtsatse samar da abubuwan zama da kayan karatau na sama da dalibai15,000 da sauransu.

Gwamna Ganduje ya tabbatar da bukatar da akeda ita na shigar da al’umma cikin harkokin ilimi, haka kuma ya samar da hukumar cigaban harkokin ilimi (EPC) a matakin Jiha  da kuma kananan Hukumomin Jihar Kano 44, wanda aka samar masu da kudin somin tabi na Naira Miliyon 440, wanda ya kama Naira Miliyon 10 ga kowacce karamar Hukuma.

Kwamitin  ya yi amfani asusun ta hanyar sake fasalin  Block 490 wanda ya Kunshi ajujuwa 981, samar da abubuwan zama guda 7,915 da teburin zama mai daukar dalibai 3 da sauran kayan koyarwa. Baya ga manyan ayyuka a sassan ilimi daban daban, Gwamantin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta tabbatar da ci gaba da mayar da hankali wajen inganta rayuwar malamai ta hanyar  biyansu albashi da kuma samar da horo akai akai.

Sama da malamai 30,000 aka baiwa damar ci gaba da karatu suna karbar albashi a wasu tsare tsare guda uku, wanda suka hada da NCE, PDE da kuma B.sd duk sun kammala ko suna gaf da kammalawa wannan na cikin  kokarin Gwamna Ganduje na tabbatar da ingantattun malamai ne kadai suke koyarwa a makarantun Jihar Kano. Kafin wannan tagomashi, Jihar Kano ce keda yawan adadin malaman da ba suda shaidar kwarewa a fadin Nijeriya,

Wannan kari ne  kan sauran tallafin Gwamantin Jihar Kano kamar irin tsarin karatun  mata wanda aka horar da sama da mata 10,000 wanda dukkan su yanzu sun cin jarrabawar shiga makarantun sakandire, wanda hakan ya tabbatar da gagarumar nasara, sauran tallafin ya hada da  yiwa Malamai karin girma wanda suka jima basu samu ba.

Babu wata nadama cikin fadar irin gagarumin nasarar da Gwamna Ganduje ya smau wajen ciyar da harakar ilimi gaba wanda ya haifar da gagarumar nasara shigar da yara makarantu tare da samun gagarumin ci gaba.

Illar yaudarar da Kwankwaso da magoya bayansa ke yiwa Jama’ar Kano kamar yadda aka sani shike tabbatar da son zuciyar kwankwaso da magoya bayansa, saboda  lokacin da yake yaudarar  al’ummar Kano,  bai san cewa akwai ranar sakamako ba, lokacin da jama’ar Kano zasu yi masa hisabi kan abinda ya aikata a Jihar Kano.

Gaskiya ta bayyana yadda Kwankwaso da abokan tafiyarsa suka salwantar da tallafin kudaden karatu zuwa kasashen waje domin zaluntar Kano da Kanawa, Baya ga barin tulin bashin da ya haura Naira Biliyon 4  na tallafin karatun dalibai, kwanan nan  wani bincike ya nuna  yadda  miliyoyin daloli  suka shiga asusun ajiyar wani ta hanyar amfani da bututun da ake zuke tallafin karatun dalibai.

A ciki akwai guda daga cikin jami’o’in  kasashen waje, da ake zargin sama da Dala Miliyon 1 an fitar dasu da sunan wasu dalibai wadanda ba’a tura su karatun ba. Kudin an ta nade su domin karkatar dasu ne kawai, Gwamnatin Ganduje ta damu kwarai wajen ci gaba da wannan shiri, kawai saboda tsarin gwamnatin na ci gaba da ayyukan data gada.     

Za’a ci gaba da tambayar cewa,  ya ya Kwankwaso ko kwankwasiyya ke hada ire iren wadancan bayanai, Yau a kasar Marocco Kwankwaso na cikin manyan masu zuba hannun jari  a kasar, Katafaren gidansa dake waccan kasar na cikin gidajen da suka fi sauran a yankin  Highbrow, ta ya zaka kwatanta wanda ya jefa tattalin arzikin Jihar Kano cikin mawuycin hali kafin barinsa gwamnati, ya wawashe baitulmali tare barin tulin bashi na sama da Naira biliyon 400 ciki harda ayyukan da ba’a kammala ba masu yawa, wanda da yawa daga cikin dodorudo ne kawai. Lokaci ya yi da Kwankwaso ya kamata ya daina siyasantar da harkar ilimi a Jihar Kano.

Wannan wace irin yaudara ce lokacin yana ofis da gangan ya kasa samar da abubuwan da ake bukata a bangaren ilimin ‘Ya’Yanmu ta hanyar sanya ingantaccen harsashin ilimi tun daga matakin firamare zuwa karamar sakandire, sannan kuma sai yanzu da yabar ofis zai ci gaba da tattara kudade domin tura yara zuwa kasashen waje karatu kawai domin ci gaba da yaudarar yaran da iyayensu. Ya kamata Kwankwaso ya sani  ba dole sai yaudari al’umma ba domin jan ra’ayinsu.

Al’ummar Jihar Kano, kwankwaso zai iya ci gaba da yaudarar wasu tsirari daga cikin mabiyansa ‘yan Kwankwsiyya amma ba kokarin yin zagon kasa ga hanya da aka dauka na ciyar da ilimi gaba ba a Jihar Kano ba.

Abubakar mai yawan fashin baki ne kan harkokin Yau Da Kullum
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: