Connect with us

KASUWANCI

An Bukaci ’Yan Nijeriya Su Yi Amfani Da Albarkar Gandun Daji

Published

on

Wani Malamin Jami’a  Farfesa Francis Bissong ya sharwaci yan Nijeriya suyi amfani da albarkatun dake a gandun dazuzzukan kasar nan din ciyar da tattalin arzinin kasar gaba.

Farfesan ya bada shawar ce a  hirar sa da manema labarai a garin Kalaba, jim kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki a kan harkar yanayi da wata kungiyar sa kai ta gwamnatin kasar Kanada, dake gudanar da ayyukan ta a Nijeriya a karkmkashin Jami’ar ta Kanada wato, Cuso ta shirya.

Ya yi nuni da cewa,  Allah ya albarkaci Nijeriya da gandun dazuzzuka masu yawan gaske  wadanda in an basu kularwar da ta kamata zasu, bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Ya ce, dabbobi kamar su irin  Gwaggon Biri da sauran ire-iren Birai zasu iya samar da kudin shiga ga kasar ta hanyar zuwa ganin a yawon buda ido.

Ya kara da cewa itatuwan dake dazuzzukan in an sarrafa su zasu samar da maguna da ban -da-ban.

Ya shawarci mahukunta dasu dauki masana akan harkar gandun daji don binciko ire-iren tsirrai da dabbobi don gano ko irin na tsirrai zasu iya warkar da cututtuka.

Ya kuma shawarci masana yanayin da su tsunduma cikin bincike don samar da hanyar da zata taimaka wajen kare tsirrai mai makon a dinga bari su na lalacewa.

Ya ce, ire-iren Timbar da ake da ita a dazuzzugan kasar nan,  in aka basu kula da ya kamata zasu iya samar wa da Nijeriya  kudin shiga mai yawan gaske.

Ya yi kira ga yan Nijeriya dasu koyi dabi’ar shuka ita tuwa a muhallan nasu daga shiga cikin yanayi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: