Connect with us

KASUWANCI

Badakalar Naira Miliyan 20: Gwamanti Na Nazarin Soke Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Kamfanin Kasar Cyprus

Published

on

Sakamakon zargin bakalar cin hanci da rashawa ta naira miliyan ashirin da akan samu hannun wasu  jiga-jigan na’aikatan hukumar Tashar Jiragen Ruwa ta kasa, Gwamnatin Tarayya tana yin nazarin soke  yarjejeniyar da hukumar ta  kulla da wani kamfani na kasar Cyprus.     

Wannan  matakin ya faru ne bayan wata uku da ofishin lauyan kasar Swiss a watan  Mayun shekarar 2017 ya saki rahoto sa, inda rahoton ya tina zargin badakalar ta  cin hancin da ake zargin wasu jami’an hukumar sun karba a 2007 zuwa  2011.

Kimanin dala  miliyan  sha takwas aka zargin kamfanin ya turo zuwa  Nijeriya.

Bugu da kari rohoton ya ci gaba da cewa, kamfanin anci tarar sa na miliyan daya na kudin kasar ta Swiss kuma aka umarce shi da ya dawo da miliyan talatin da shida na kudin kasar ta Swiss, kuma aka danganta ribar da kamfanin ya samu a matsayin haramtacciya.

Sakamakon bayar da wannan rahoton da mahukuntan kasar ta  Swiss suka yi, Darajta Janar ta  Hukumar tashoshin jaragen ruwa ta Nijeriya, Hadiza Bala-Usman, kwanan baya ta sanar da cewa,  kamfanin, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) zata hukunta kamfanin.

A cewar, Hadiza hukumar ta samu izinin hakan ne daga koton kasar ta Swis, inda ta kuma turawa hukumar ta EFCC don gudanar da binciken, tare da bincikar jami’an da ake zargin sun amfana da cin hancin.

Ta kara da cewa, Hukumar ta kuma turawa ofishin Akawu na kasa takardun kotun kasar  ta Swiss ta turo akan zargin badakalar.

LEADERSHIP A YAU ta ruwaito sake yin nazari akan kwangilar ko kuma soke ta gaba baki daya,   idan aka yi la’akari da binciken da ofishin Akawun gwamnatin tarayya ya gudanar.

Wasu daga cikin abubuwan da gwmanatin tarayya  tayi la’kari dasu akan kamfanin, sun hada da, sake yin nazarin akan kwangilar da aka baiwa kamfanin wadda ta hada da sanya wa kamfanin takun kumi da kuma hana shi duk wata harkar kasuwanci da Hukumar ta jiragen Ruwa ta kasa da kuma sanya masa sababbin hukunce-hukunce da duk wani kamfani da zai yi harkar kasuwanci a kasar nan, tare da hukunta jami’an Hukumar ta tashar jiragen ruwan na kasar nan da kuma tsofaffin ma’aikatar hukumar.

An kuma bayya cewa, Ofishin Akawun gwamnatin tarayya a bisa binciken da ya gudanar, ya gano cewa, kamfanin yana daya daga cikin kamfanonin da aka kulla yarjejeniya dashi, inda kuma ya gudanar da aikin kwangilar ga Hukumar ta Tashoshin jaragen Ruwa ta kasa har ta samu sama da naira biliyan bakwai a wasu shekaru da suka shige.

Har ila yau, an bankado tsofaffin  jami’an Hukumar ta tashashen jiragen ruwan, suna daga cikin wadan da suka amfana da badakalar. Sai dai, rahoton kasar  bai ambato sunayen wadanda ake zargi da aikata badakalar ba.

Kamfanin dai, ya shiga yarjejeniya da hukumar ce, a  2005, don kafa yadda za a kawo saukin yin fito ga dukkan masu amfani da jiragen ruwa dake tsibirin yammacin Bonny Onne, da Okrika da   kuma Fatakwal.

Hukumar ta jiragen ruwa ta kasa tana da kashi sittin bisa dari, inda kuma hukumar Bonny Channel zata dauki kashi arba’in bisa dari.

Wata majiya a hukumar ta jiragen ruwan  da bata so a bayyana sunan ta ba, ta shedawa jaridar LEADERSHIP cewa, kamfanin da ake zargin ya amsa zargin da ake masa na bada cin hancin ga wasu jami’an hukumar sai dai, sun bada cin hancin ne saboda jami’an sun ki basu rasidan su.

A bangaren kamfanin a wata takarda da ya gabatar wa da Hukumar jiragen ruwan ta kasa yace, ya shinfida wasu matakai don magance irin hakan nan gaba, duk da cewa kamfanin ya kuma biya tarar da mahukunta kasar Swiss taci tarar.

Wata majiya ta shedawa jaridar LEADERSHIP cewa, kudurin gwamnatin tarayya na soke yarjejeniya yana daga cikin yunkurin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na rage cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Majiyar ta kara da cewa, uzurin da kamfanin ya bayar na dalin bada cin hancin bai da wata madafa. Hukumar ta bayyana cewa, ta nemi shawarar lauyoyin ta da sauran masu ruwa da tsaki akan maganar. Tuni dai, hukumomin yaki da cin hanci da ban-da -ban, suka fara bincike akan badakalar.

An ruwaito wata majiya ta ce, za a sanar da ‘yan kasa, akan samakon binciken zargin badakalar. Bugu da kari, an ruwaito wata majiyar ta ce, hukumar a tsaye take don kawo karshen cin hanci da rashawa a hukumar ta hanyar gwamnatin tarayya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: