Connect with us

LABARAI

Dan Sanda Mai Karban Kudin Beli Ba Shi Da Bambanci Da Barayin Mutane- Kwamishina

Published

on

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Zubairu Mu’azu ya ce ‘yan sandan da ke karbar kudin beli sun fi masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa muni. Kwamishinan ya fadi hakan ne a ranar Talata a garin Legas yayin da yake jawabi wurn taron kaddamar da dakin rubuta shaida a sashen binciken masu aikata manyan Laifuka (SCIID) a Panti.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma ja kunnen jami’ansa da su guji karbar cin hanci daga hannun mutanen da suka kama saboda hakan yana bata wa rundunar suna a idon duniya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: