Connect with us

KASUWANCI

Gidauniyar GH Da Kamfanin Digital Agro-Connect Sun Yiwa Mata Bita Kan Noma

Published

on

Sananniyar Gidaniyar kasuwanci ta G H dake a jihar Kaduna tare da hadin gwaiwa da kamfanin aikin noma na  Digital Agro- Connect sun yiwa mata, matasa da juma zawara sama da dari bita a kan fannin aikin noma a Kaduna.

Taron ya gudana ne a dakin taron Gidauniyar kuma taron ya samu halarcin mata, matasa, zawarawa harda na wasu da suka jima suna yin aikin noma a jihar.

A hirar sa da jaridar Leadership Hausa Ayau jim kadan da tashi daga taron bitar na kwana daya, Shugaban Gidauniyar ta GH Alhaji Abdullahi Gambon Hajiya ya ce, “ Mun yi hadakar ce don a bayar da horon ga matasan, mata da kuma zawaran yafda suma zasu rungumi aikin noma, musamman musammman na zamani.”

Alhaji Abudullahi Gambo ya ci gaba da cewa, “ Wannan ba shine karo na farko ba domin ko a kwanukan baya Gidauniyar mu ta gudanar da makamancin irin wannan horon a fannin kasuwanci kuma mafi yawanci matasa da mata zawara ne suma amfanai wasu ma har bashin gudanar kasuwanci an basu ta hayar  bankin masana’antu da kuma fannin aikin noma inda wadanda suna amfana suka samu tallafi daga bankin manoma.”

A cewar Alhaji Abudllahi Gambo, “ Mun yi hakan hakan ne don tallafawa kokarin da gwmnatin  Shugaban kasa Muhammadu Buhari take yi na yin yaki da talauci ta hanayar kasuwanci da kuma aikin noma.”

Shugaban Alhaji Abudullahi Gambo ya yi nuni da cewa baza mu gajiya ba zamu ci gaba da gudanar da irin wannan bitar, musamman ga matasa, mata da kuma zawara yadda suma zasu zamo masu dogaron da kansu da kuma ciyar da tattalin arzikin Arewancin kasar nan da kuma kasa baki daya.”

Ya yi kira ga wadanda suka amfana da horarwar dasu yi amfani da ita yadda zasu taimakwa kansu da kuma kasa baki daya.

Ita ma a nata jawabin a gurin tarin Mataimakiyar Shugaba a hukumar dake rabar da takin zamani ta jihar Kaduna( KADA) Uwargida  Yashim Chanwe taja hankalin mahalarta taron bitar dasu dinga yin la’akari da yanayin kasar noma kafin suyi shuka.

A cewar ta, “ Ina son ku sani cewa ya kamata manomi ya san wacce irin gona ce ya dace ya yi shuka don gudun kada ya ci karo da matsalar yanayin gona, inda ta yi nuni da cewa, ta hakan ne kawai manomi zai iya samun amfanin gona mai albarka kuma mai yawa.”

Shi ma a nasa jawabin a gurin taron, Alhaji Yusuf da akafi sani da mai fashin baki ya jinjinawa wadanda suka hada taron, inda ya ya ce, bitar zata taimakawa wadanda suma amfana matuka wajen rungumar aikin noma gadan-gadan.

Shi kuwa wani kamfanin ssyar da takin zamani Mista  Yemisi Adere Charles ya bayar ds tallagin takin zamani ga Gidauniyar ta GH.

Ya ce, ya yi hakan ne yadda za’a kara habaka aikin noma a jihar, musammannganin yadda Gidauniyar ta mayar da hankali wajen bauwa mata, matsa da kuma zawarawa horo a fannin aikin noma.

A karshe ya ce, “ Kamfanin zai kuma ci gaba da baiwa Gidauniyar tallafin kayan noma, musamman yadda zata samu sukunin bayar da horo a fannin aikin gona.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!