Connect with us

KASUWANCI

Gonar Teku Farm Za Ta Horar Da Matasa 2,000 Kiwon Kifi Da Rainon Itatuwa

Published

on

Shugaban  shahararriyar gonar nan wadda akafi sani da Teku International and Agro Allied Serbices dake a jihar Kaduna Alhaji Ibrahim Salisu ya sanar da cewa gonarsa zata baiwa mata, matasa da kuma wadanda suka kammalla makaranta basu da aikin yi har dubu biyu horo na musamman a kan  kiwon Kifi, renin yayan itatuwa da kuma yadda ake shukar furanni.

Ibrahim wanda ya sanar  sanar da hakan ne a hirarsa da Leadership Ayau a garin Kaduna ya ce, “Zamu basu horon ne  a kan dabarun noma na zamani da suka hada da, renon yayan itatuwa na zamani, renon furanni da kuma kiwon Kifi na musamman kyauta.”

A cewar Alhaji Ibrahim, “  a kwanan baya mun baiwa matasa, mata da kuma wadanda suka kammala makaranta amma basu samun aikin yi horo na musamman a kan kiwon kifi,  renon yayan itatuwa da furanni kyau, inda muka horas da dari biyu kyauta.”

Shugaban ya ci gaba da cewa, a kashi na biyun wanda shima kyauta ne zamu gudanar dashi zamu zabo wadanda za’a baiwa horon za’a zabo su ne daga kananan hukumomi ashirin da uku dake jihar bayan mun kaiwa shugabannin kanaan hukummin takardun neman izinin su turo sunayen wadanda za’a baiwa horon.”

Ya sanar da cewa, manufar ita ce yadda in an basu horon in sun koma yankunan da suna fito zasu zamo masu dogaro da kansu har suma su koyawa wasu da basu halarci horaswar ba.

Alhaji Ibrahim ya sanar da cewa, “Mun bayar da horon kashi na daya da kuma na biyun da muke shirin yi a cikin wannan shekarar ne domin munyi dubi akwai matasa, musamman da basu da aikin yi wasu kuma sun kammala makaranta amma suna zaman kashe wando.”

Ya yi nuni da cewa, wasu da suka suma koyo aikin noma a jami’a amma basu iya aikin aikace ba, suma  sun daga cikin wadanda gonar zata basu horon yadda zasu zamo kwararru sosai.

Shugaban ya kara da cewa, duk wanda yake da shawa’awa shiga horon a shirye muke mu bashi horon, inda ya ce, zamu rabar da fom kyauta ga wanda suke da sha’awar shiga horon.

Alhaji Ibrahim ya  yi nuni da cewa, lokaci yanzu ya chanza idan matakan gwamnati uku na kasar nan zasu bayar da wani tallafi na aikin noma ga masu shawa’awar shiga fanni sai sunga sun samu horo tukkun na.

A cewar shugaban, “Har yanzu mu a Arewacin kasar nan, an barmu a baya wajen yin aikin noma na zamani, kiwon kifi, renon yayan itatuwa da kuma renon furanni, inda ya ce, akwai bukatar mu rungumi fannonin uku na zamani, musamman don habaka tattalin arzikin yankin da kuma tattalin arzikin alumma baki daya dake yankin na Arewa.”

Alhaji Ibrahim ya ce a sshekara mai zuwa zamu kuma fadada horaswar a kan  kiwon dabbobi don habaka tattalin arziki.

A karshe shugaban ya ce, “ Zamu bayar da horon ne a gonar mu dake Bbbban titin Nmandi Azikwe daura da  Asibitin Ido dake a jihar Kaduna.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: