Connect with us

RAHOTANNI

Har Daga Abuja Matata Ta Gayyato Saurayi Su Ka Kama Otel – Hussain

Published

on

Magidancin da Matarsa ta kusa hallaka shi da wuka a kwanakin baya da suka wuce, Sa’id Hussain, ya samu lafiya ya kuma zayyana wa duniya abin da ya shiga tsakaninsa da matar mai suna Fatima Musa (Hanan), tun daga kan zare har abawa.

Idan ba a manta ba dai, wannan al’amari ya faru ne ranar 22 ga Yunin wannan shekara cikin tsakar dare da misalin karfe 1:30, a Unguwar Mai Kalwa, Na’ibawa, cikin Karamar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano. Kazalika, bayan faruwar wannan ta’addanci da Hanan ta aikata ne, ba tare da wani bata lokaci Jami’an tsaro suka yi awon gaba da ita.

Adaidai lokacin da wadannan Jami’an tsaro ke tuhumar Fatima bisa wannan mummunan aika-aika da ta yi ne kuma, kwatsam, sai aka fara ganin hotunan bidiyonta suna yawo a kafafen sada zumunta, ‘yar’uwanta na tuhumar Maigidan nata Hussin da cin zarafinta ta hanyar yi mata dan banzan duka, wanda a cewar tasu wajen kokarin kwatar kanta ne, hart a caka masa wannan wuka da yanzu ake zargin ta da aikatawa.

Har ila yau, a wani taron mane ma labarai da Hussain din ya yi, ya bayyana Matar tasa (Hanan) a matsayin cikakkiyar mai laifi, wadda kuma ta yi masa kage dangane da dukan ta da ta bayyana wa duniya cewa yana yi. Musamman a ranar da ta aikata wannan aika-aika, ta kuma ce wai ta kwaci kanta daga wurinsa ne.

“Akwai wani lokaci da na iske Matata Hanan tana rawa a falona sanye da kaya masu nuna tsaraici, tana kuma dauka a bidiyo za ta tura wa saurayinta. Ganin haka ne, ya sa na yi wuf na sanar da Mahaifita wannan abu da ke faru, nan take ta fara da tambaya ta cewa ko na sanar da yayar Matar tawa da Kakarta kafin na sanar da ita, sannan ta roke Allah da Annabi ka da na sake na fada wasu su ji don gudun ka da na bata wa danginsu suna a idon duniya.

Haka nan, akwai lokacin da na taba kalubalantar wani daga cikin samarin nata da suke yin waya sannan ta ke kuma tura musu da irin wadannan bidiyo da kuma murya da hanyar tura sako cewa, shin bai san cewa ita matar aure ba ce? Sai ya ce wallahi shi bai taba sanin cewa tana da aure ba”, in ji shi.

“Irin Wadannan sakonni da ke dauke da muryarta da take tura wa samarinta, wannan shi ne na 30 da na kama ta da shi, na kunna na ji irin hirarrakin da take yi da wannan saurayi nata a wayar tarho.

Kazalika, ina da cikakkiyar shaida ta yadda Matata ta gayyaci wani saurayi nata daga Abuja, ya zo sauka dauki dauki tare da ita a wani Otel da ke Unguwar Bompai, wanda dai kawai ba na son kama suna. Amma dai wannan abu ya faru ne, a 26 ga watan Afrilun 2016, ba tare da la’akarin cewa ita matar aure ba ce. Tana cikin wannan Otel daga misalin karfe 10:13 na safe har zuwa 12: 16 na rana, ina nan da wadannan bayanai, don kuwa na’urar CCTB ta wannan Otel ta nadi kafatanin wadanan bayanai da na ke fada a hali yanzu”, a cewar tasa.

Hussain ya ci gaba da cewa, a ranar wannan Juma’a dai da wannan abu ya faru, na kama Hanan tana shan wasu kwayoyi a gidana tare da Shisha ta hada shi da wani sinadarin kayan maye. Sannan a ranar Azimin karshe, ta zuba min guba a abincina, ta hanyar kada wa a cikin kwai kafin ta soya, wannan ma ina da cikkakiyar shaida a kai. A lokacin da abubuwa suka yi tsamari ne, muka nemi Dakta Bashir, Limamin Masallacin Alfurkan, ya shiga tsakani ya kuma ba mu shawarwari don gyaruwar al’amuran.

“A lokacin da muka je ganin Dakta Bashir tare da Matar tawa, Mahaifiyar da yayanta dukkanin su a cikin motata na dauke su muka tafi tare. A gabansu ne kuma na zayyana wa Dakta Bashir irin miyagun halayenta musamman a bangaren rashin kula da addini da kuma shaye-shaye ta kuma amsa ko kadan ba ta musa ba.

Amma Hanan, a wannan rana bayan mu dawo gida ne kuma ta aika min wannan aika-aika da wuka bayan na kwace wayarta wadda take tura wa samari da hotuna da kuma bidiyonta na batsa. A lokacin da dauko wadannan wukake guda biyu daga dakin girki ta shigo daki, tuni da ma ni ina kwance a kan gado. Da ta shigo, sai ta zauna a gefen gado ta juna min baya kamar tana yin wani abu daban, a daidai wannan lokaci ne ta fara fito da wuka guda daya ta caka min a gefen cikina sannan ta jefar da ita bayanta.

Da na ga ta sake yin wuf ta dauko wata wukar za ta sake caka min, sai na yi maza na mike na kuma yi kokarin rike hannunta, garin haka ne na ji ciwo a kamar yadda kuke gani. Haka ta sake daga wukar za ta sake luma min, Allah Ya taimake ni na kauce na kuma yi kokarin danna wukar da ke hannunta cikin katifar da muke kai. Sannan na samu na mike tsaye na rike hannunta ina ta faman kokarin yadda za a yi na kwace wukar. Muna tsaka da wannan kokawa ne, ta ciji hannuna ta fadin cewa lallai na sakar mata wannan wuka”.

“A wannan dambarwa da muka dauki lokaci muna yi ne, na samu na hankade tat a fadi ta buge kai da gefen dirowa ta kuma fadi a kasan tayal wanda wannan ya yi sanadiyyar daujewarta a fuska da kuma kunburi. Don haka, maganar fada ko kokawa da ta ce mun yi a dakin girki, wannan ba gaskiya ba ne. Idan aka duba Jinina da ya zuba, za a ga daga iya cikin daki ne zuwa falonmu.

Har ila yau, ina kalubalantar danginta kaf, tun daga kan Mahaifiyarta har zuwa kan ‘yan’uwan Mahaifinta da cewa, su kawo kowace irin shaida da take nuna cewa ina dukan ‘yarsu a kowace rana ta Allah kamar yadda suke zargi. Sannan faifan bidiyon da suka rika yada wa, yana da dangataka ne da wadannan abubuwan da ke faruwa?” in ji shi.

“Haka zalika a wannan rana, Abokina Lawali ne tare da taimakon Allah ya samu ya ceto rayuwa ya yi gaggawar kai ni Asibiti. A daidai lokacin da yana tallafe da ni, fuskar da na gane baya ga tasa, ta Mahaifiyar Matata ce, inda nan take na kora mata kashedin cewa ka da ta sake ta taba ni, Abokina Ustaz shi ne shaida. Sannan na fada mata cewa, duk abin da Matata ke aikatawa na rashin dacewa da kuma kokarin ba ni guba da ta yin a ci na mutu, babu abin da ba ta sani ba amma ba ki dauki wani mataki a kai ba. Jin fadin haka da ta ji na yi, nan da nan sai ta nemi da na shiru da bakina, tana roko na da cewa don Allah ka da na tona wa ‘yarta asiri a idon duniya.

Kafin Surukar tawa ta bar Asibitin, sai ta nemi Abokina Ustaz ya nemi ‘yar tata ya kuma tattauna da ita cikin sirri don jin gaskiyar abin da ya faru. Tana kokarin kwatanta abin da ya faru da Zainab Sanda Saga, da kuma yadda danginta suka yi kokarin kubutar da ita ta hanyar lalata dukkanin wasu shaidu da za su tabbatar da cewa, ‘yarsu ce ke da laifi.

Saboda haka, irin wannan abu ya taba faruwa a Abuja, inda Matar da kashe Maigidanta. Shi yasa yanzu Surukata ta hada baki da ‘yarta don kokarin ruguza dukkanin wata shaida da nake da ita, sannan aka rika yada ni a shafukan sada zumunta ana bata ni ana kuma munanan maganganu a kaina”, in ji shi.

Har wa yau, Hussain ya yi ikrarin cewa, bai taba sanin haka halin Matarsa yake ba har sai bayan ya aure ta, har bayan auren ma bai yi saurin gano irin wadannan munanan halaye nata ba, sai bayan an dauki tsawo lokaci saboda babu ruwansa da harkar wayarta. Ko a ranar da za a daura aurensu, sai da Mahaifinta ya zaunar da ita ya fada mata cewa, wannan ce fa damarki ta karshe ta zabin miji, sannan ya sake tambayar ta cewa, in ce kuwa tana so na, ta amsa da eh.

Haka nan, ban taba ayyanawa a raina cewa, na sake ta ba, dalili kuwa a matsayin ka na Musulmi a koda yaushe kana sa ran gyaruwar al’amura, shi yasa a cikin watan Azimi na dage da yin addu’ar Allah Ya daidaita tsakaninmu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!