Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Hulda Tsakanin Sin Da Turai Za Ta Kara Samun Ci Gaba Bayan Sabbin Shugabannin EU Sun Fara Aiki

Published

on

A ran 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wata sako ga firayin ministan kasar Belgium Charles Michel, domin taya shi murnar hawa kujerar shugaban majalisar kasashen Turai, inda Xi ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan kasashen Turai da su kara taka rawa a cikin harkokin kasa da kasa, kuma tana son ciyar da huldar dake tsakaninta da kasashen Turai gaba yadda ya kamata, musamman ma a fannonin shimfida zaman lafiya da samun ci gaba, da yin kwaskwarima da wayewar kai. Sakon da shugaba Xi ya aika ya nuna cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan hadin kai dake tsakaninta da kasashen Turai.
An yi hasashen cewa, sassan biyu wato Sin da Turai, za su ciyar da huldar dake tsakaninsu gaba cikin lumana, saboda sassan biyu suna mallakar moriya iri guda.
A farkon shekarar da muke ciki, bi da bi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da firayin ministan kasar Li Keqiang, sun kai ziyara kasashen Turai, har ma sun bude wani sabon shafi yayin da ake kokarin raya huldar dake tsakanin sassan biyu.
A yayin shawarwarin da shugabannin kasar Sin da kungiyar EU suka yi karo na 21 a watan Afrilun bana, bangarorin 2 sun sake nanata kara azama kan samun sabon ci gaba, wajen raya huldar abokantaka da ke tsakaninsu ta fuskar zaman lafiya, da ci gaba, da yin gyare-gyare da wayin kai, tare da tsara ajandar ayyukan hadin gwiwa bayan shekarar 2020 cikin hadin gwiwa. Don haka sauyewar shugabannin kungiyar ta EU ba za ta kawo illa ga manufar yin hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kungiyar EU ba, a’a, ana sa ran kara sabon karfi kan hadin kan bangarorin 2.
Alal misali, kasar Sin da kungiyar EU suna da bukatun bai daya wajen kiyaye zaman lafiya. A matsayinsu na muhimman sassa 2 na duniya, suna tsayawa kan tabbatar da tsarin kasa da kasa, inda aka mayar da MDD a gaban komai, yayin da ake kara fuskantar ra’ayin nuna bangaranci da danniya.
Bangarorin biyu na goyon-bayan daidaita sabani, da rikici a yankin ta hanyar yin shawarwari, a kokarin tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa, da kuma dauwamammen ci gaba a duniya baki daya. A halin yanzu, matsalar nukiliyar Iran na dada tsananta, har ma kasar Sin na kara yin mu’amala da tuntuba tare da kasashe masu ruwa da tsaki a nahiyar Turai, ciki har da Birtaniya, da Faransa, da Jamus, don daidaita matsalar yadda ya kamata.
Har wa yau, Sin da Turai na cin moriyar juna a fannonin da suka shafi ci gaba da gyare-gyare. Kungiyar tarayyar Turai wato EU, ta zama aminiyar cinikayya mafi girma ta kasar Sin a jerin shekaru 15, kana ita kasar Sin ta zama abokiyar cinikayya mafi girma ta biyu ta EU. A yayin da kasar Amurka ke kara rura wutar takaddamar ciniki a duk duniya, ya zama tilas Sin da Turai su zama tsintsiya madaurinki daya, don kare tsarin kasancewar bangarori daban-daban, da tsarin gudanar da ciniki cikin ‘yanci bisa doka da oda.
Sin da EU sun amince da sa kaimi wajen hada kan shawarar Sin ta “Ziri daya da hanya daya” da dabarar EU ta hada kai tsakanin Turai da Asiya, kana a yanzu haka bangarorin biyu suna kokarin gaggauta shawarwari a tsakaninsu game da yarjejeniyar zuba jari, da nufin cimma yarjejeniya mai babban matsayi kafin shekarar 2020.

Baya ga haka, bangarorin biyu sun cimma muhimmin ra’ayin bai daya a fannonin yin kirkire-kirkire ta fuskar kimiyya da fasaha, sayo kayayyaki da gwamnati ke yi, da kuma cinikayyar kayayyakin aikin gona da dai sauransu, kuma sun bayyana fatansu na kara tattauna batun yin kwaskwarima ga kungiyar WTO. A gun taron koli na G20 da aka shirya a birnin Osaka na kasar Japan, shugaban kasar Sin ya sanar da muhimman matakai guda biyar, na gaggauta bude kofa ga kasashen ketare. An yi hasashen cewa, kokarin da kasar Sin ke yi a fannonin takaita sassan da baki ba za su zuba jari ba, da kara kyautata muhallin gudanar da cinikayya, da kuma kara karfin kiyaye ikon mallakar fasaha, zai samar da dama mai kyau ga kamfanonnin kasashen Turai a nan gaba.
Ga kungiyar EU, ya kamata a daidaita huldar hadin gwiwa da kuma yin takara tare da kasar Sin yadda ya kamata, da warware matsalolinsu don samar da yanayi maras nuna bambanci ga kamfanonin Sin wajen zuba jari, da gudanar da ayyukansu.
A fannin yin shawarwarin al’adu, an ci gaba da raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kungiyar EU. A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a kasashen Turai a watan Maris na bana, an cimma wasu nasarori kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Italiya, da Faransa, da Monaco a fannonin al’adu, da wasanni, da bada ilmi, da yawon shakatawa da sauransu, mu’amalarsu da aka zurfafa da juna za ta taimakawa raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kungiyar EU bisa bukatun jama’arsu.

A halin yanzu, ana fuskantar babban canji a duniya, an kara samun moriya iri daya a tsakanin Sin da kungiyar EU. Sin tana fatan za a yi kokari tare da sabbin shugabannin kungiyar EU, wajen inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu a cikin shekaru 5 masu zuwa. Inganta hadin gwiwarsu ya dace da moriyar bangarorin biyu, kana zai taimakawa wajen samun zaman lafiya da wadata a duniya baki daya. (Masu Fassarawa: Jamila, Tasallah, Murtala, Bilkisu, Zainab daga CRI Hausa)
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: