Connect with us

KASUWANCI

Kamfanin Dangote Zai Yi Hadaka Da Gwamnatin Neja Don Habaka Kasuwar Sikari

Published

on

Don kara habaka sarrafa kasuwancin  Sikari a Nijeriya da rage zaman kashe wando, kamfanin Dangote zai yi  hadin gwaiwa da gwamnatin jihar Neja.

Kamfanin na Dangote ya shiga yarjejeniya ce  don kafa kamfanin Sikari na naira miliyan dari da sittin da shida a jihar.

A jawabin sa lokacin rattaba hannun yarjejeniyar da ya gudana a Minna, Babban birnin jihar, Shugaban Kamfanin rikunonin Dangote Aliko

Dangote ya bayyana cewa, in an kammala kamfanin, zai samar da ayyukan yi sama da dubu sha biyar ga ‘yan jihar da kuma kara farfado da tattalin arzikin jihar.

Dangode yaci gaba da cewa, aikin na dalar  miliyan dari hudu da hamsin, za a gudanar dashi   ne yadda zai samar da kada-da ta Sikari dubu sha shidya.

Shugaban ya ce, kamfanin wanda a yanzu yake gudanar da shirin noman shikafa,  a jihohi da ban-da-ban dake kasar nan, shi kadai ne ke  sarrafa Sikari a Afirka dake jihar Legas da kuma gona Rake dake a jihar Adamawa.

Ya ce, kamfanin ya yanke shawarar zuba jarin ne, don samar da ayyuka ga ‘yan kasar, musaman yan jihar ta Neja. Ya kuma jinjinawa gwamnan jihar, Alh. Abubakar Sani Bello a bisa hangen nesar da yayi na janyo masu zuba jari a jihar.

A na shi jawabin, Gwamna Bello ya yi nuni da cewa, aikin zai kara haba harkar noma a jihar da kuma kasa baki daya, inda ya kuma bayyana farin cikin ganin cewa an gudanar da yarjejenyar ce, lokacin mulkin din sa.

Ya danganta kamfanin na Dangote, matsayin Kamfanin dake taimakawa wajen farfado da tattalin arzkin kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: