Connect with us

MAKALAR YAU

Kokarin Hana Bara: Mu Ma Almajirai Ne..!(3)

Published

on

Kamar yadda na yi alkawari zan cigaba da wannan rubutu nawa gashi cikin ikon Allah zan kawo kashi na karshe akan wannan mukala tawa akan batun almajiranci wanda shugaba Buhari ya ce yana da alaka da ta’adanci saboda kawai ya raina ‘yan arewa.

Alamu na nuni da cewa wanna maganar tana neman kama gabanta kila ya ji wuta domin kuwa ba abu ne mai sauki ba ace an wayi gari wannan mutumin ya yi nasarar hana almajiranci saboda ko ba komi zai haifarwa da yankin arewa karancin mahaddata alkur’ani musamman yanzu da suka yi karanci.

An samu wani sabon yanayi da idan shugaba Muhammadu Buhari ya kudiri aniyar yin wani abu na cutar da al’umma idan suka dage suka nuna tirjiya yana canza ra’ayi akwai misalin haka akan batun samar da rugage a yankin kudu mun ga yadda suka ta so masa kamar su cinye shi, sai gashi ya koma daga baya ya yi lakwas.

To, wannan batun na maganar hana almajiranci ya zama wajibi wadanda abin ya shafa kai tsaye su nuna jan ido da rashin amincewarmu tunda mun ga ‘yan kudu sun tsaga sun ga jini.

Idan muka kara komawa baya muka yi tunani zamu ga cewa a karkashin shugaba Muhammadu Buhari babu wani abu da zai amfani wannan yanki na arewa kullin abubuwa da suke faruwa babu dadin ji indai akan wannan gwamnati ne, amma kuma babar matsala shi ne baka da ikon yin magana.

Ganin yadda wannan magana ke kokarin bin shanun sarki ya sa nima zan ajiye alkalamina hakan nan sai kuma ya kara bullowa da ‘yan arewa wata sabuwar fitinar bayan gama sauraran manya sai mu cigaba daga inda muka tsaya.

Amma abinda muke cewa har kullin shi ne, duk lokacin da kake kokarin ka raba mutun da abinda yake yi to akwai hanyoyi masu sauki wajan hana shi ko kuma kawo mashi mafita wanda cikin kankanin lokaci zai yarda ya kuma karbi abinda ka zo mashi da shi.

Idan ba a manta ba kwanan nan an zo da wata sabuwar doka ta hana yawo ko amfani da mashina a wasu yankuna da suke fama da masu tada kayar bayan, wanda kafin a sanya wannan doka akwai abubuwan da ya kamata ayi la’akari da su wanda daga karshe za a iya samun abinda ake so cikin sauki ba tare da wata matsala ba, amma sai ba ayi haka ba.

Dokar ta ce kawai a daina amfani da mashin saboda da sune masu garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa suke amfani, da sune ake kai hare-haran wuce gona da iri, da su ne, ake yin fashi da Makami.

Abin cewa anan, idan har jama’a da suke wannan yanki suka daina amfani da wadannan abubuwan hawa, menene makomarsu madamar suna zaune a wannan wurare ba su dawo cikin gari ba da sunan gudun hijira? Me gwamnati ta tanadar ma su wanda zai maye gurbi abinda suke da shi ada.

To, haka batun yake kan batun hana almajiranci, kamar yadda na sha fada, kuma sauran al’umma kulin suna kara fadakarwa cewa bara ba abune mai kyau ba, kuma kowa ya san haka ya kuma yarda, to amma saboda yanayi da muka samu kanmu wanda har gobe ana zargin gwamnati ta taka muhimmiyar rawa wajan haifar da wannan yanayi.

Alal hakika, yana da wahalar gaske a wayi gari an daina bara, to balantana almajiranci wanda akwai matukar mahimmaci cikin wannan sha’ani, wanda kuma babu wanda bai amfane shi ba.

Gwamnatoci a yankin arewa da suka gabata, sun kula cewa akwai wannan baban kalubale na bara da kuma shi kanshi almajirancin saboda haka a matakin jiha suka yi wani sabon tunani na cewa ya kamata su duba wannan lamari da idon basira maimakon su watsar da shi ko kuma su ce sun hana.

A bisa wannan tunani na su, a karshe sun yanke shawara cewa dole a jawo almajirai a jiki domin suma mutane kamar kowa, ‘yan kasa ne kamar kowa, suna da hakki akan gwamnati ya kamata suma a duba bukatunsu domin yin wani abu da zai rage wannan dabi’a da kuma matsala ta bara.

Sun fito da tsare-tsare da gwamnati da zata taimaka wajan ganin cewa almajirai da almajiranci sun samu gata a gwamnatance ba wai a tsangwame su ba, har wani ya yi barazanar cewa zai hana wannnan bara baki daya bayan a baya bai yi wani tunani na cewa ta ya ya zai taimakama masu ba kafin ya ce ya hana.

Gaskiyar magana abin yana da matukar daure kai, mune ‘yan arewa, mune ke zaune a arewa, mune ke tare da almajirai, kai karewa da karau ni kaina nan almajiranci aka kawoni gashi kuma cikin ikon Allah na samu sa’a da nasara a rayuwa ina kara yi wa Allah godiya bisa wannan ni’imar da ya yi mani a matsayina na almajiri.

Duk da haka gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana da sauran dama domin duk bayanin yadda gwamatocin baya suka tafiyar da sha’anin almajirai suna nan idan yana bukata zai nema ya kakafe ya duba ya yi gyara ya taimakawa wannan bangare idan yana da rabo gobe kiyama.

Domin abin yana da matukar kunya ace tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yarda ya taimaki wannan bangare ta hanyar gina manyan makarantu a arewacin kasar nan domin dai kawai a wayi garin an rage kaifin wannan dabi’a a arewa amma sai ga wani wanda duk bayanai sun tabbatar da almajiranci ya kawo kakanninsa Najeriya ya ce bayan san almajirai su ke kawo matsalar tsaro yankin arewa

Har gobe ana bara a jihar Legas da kuma yankin kudu akwai almajirai masu bara da kuma masu karatu, duk yadda Buhari ya kai tsananin kiyayya ga almajirai bai kai Yarabawa ba, amma sun bar su tama, suna can suna gudanar da sha’aninsu, ba su taba shirya masu shifcin gizo ba don su ci mutuncinsu ba, sai dai idan wata rigima ta kaure su huce akan su.

To alamun da shugaba Buhari yake nuna game da harkar almajiranci a yankin arewa in banda ‘yan kudu da yanzu suka taka masa burki game da maganar kafa ruga wanda suka ce ba sa so, ba su kamar muna so, da yanzu ya dauki wani mummunar mataki game da wannan batu da yake da dadaddan tarihi a kasar Hausa.

Kuma kar mu manta a wannan duniyar  Buhari ya iske bara da almajiranci, haka kuma Insha’Allahu anan zai barta, sai dai idan zai zo da wani tsari da zai taikamawa jama’a rayuwa ta yi sauki a garesu wannan barar ta saukaka, muddun bai yi haka ba, to sai mu ce dama ya jaraba haka ne domin ya ji idan akwai laushi ya fasa in kuma babu shikenan, an aiki Bawa garinsu.

Mai karatu anan zai dakata da wannan mukala tawa mai take Hana Bara: Mu ma almajirai ne, saboda idan aka duba kamar yadda na ce ba a dade ba, su Buhari suka zo barar kuri’a wajan jama’a amma yanzu sun koma gefe guda suna yaki da bara, saboda haka  a irin wannan yanayin babu wanda zai iya kaucewa bara sai dai a ce ya danganta da wani irin hali ya shiga na neman taimako. Allah Ya shiga tsakaninmu da ma su san hana bara da almajitanci. Amin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!