Connect with us

LABARAI

Majalisa Ga Gwamnati: A Saki Al-Zakzaky Da Gaggawa

Published

on

Membobin Majalisar wakilan Nijeriya sun bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin jagoran ‘yan uwa Musulmi, wato Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda gwamnatin take tsare da shi kusan tsawon shekaru hudu.

‘Yan Majalisar sun ce rashin sakin malamin zai iya haifar da tashin hankalin da zai iya fin na Boko Haram muni, don haka abinda ya fi shine gwamnatin ta gaggauta sakin Shehin malamin kamar yadda kotun tarayya ta umarta.

Shugaban marasa rinjaye Ndudi Elumelu ne ya fara ayyana wannan kudirin, inda sauran ‘yan majalisar suka goyi bayan kudirin, a cewarsu cigaba da tsare Shehin malamin zai haifar da mugun tashin hankali a kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!