Connect with us

LABARAI

Obasanjo Ne Matsalar Nijeriya – Oba Na Legas

Published

on

Taro ne babba wanda ya tara manyan baki daga ciki da wajen Nijeriya, domin karrama jan gwarzo, Tsohon Gwamna, fitaccen dan jarida, ginshikin siyasa.

Sai dai kuma lokaci ne na fadin gaskiya jiya a Legas, inda shugabannin siyasa, manyan jami’an gwamnati, Sarakunan Gargajiya da manema labarai gami da ‘yan’uwa da abokanan arzikin daya daga cikin shugabannin Jam’iyyar APC, Aremo Olusegun Osoba, ya yi bikin cikarsa shekaru 80 da haihuwa gami da kaddamar da littafinsa mai suna, “Battlelines: Adventures in Journalism and Politics.”

A wajen bikin wanda tsohon shugaban gwamnatin mulkin Soja, Janar Abdussalam Abubakar, da jagoran APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Ambassada Bababgana Kingjibe, duk suka shugabanci taron,  sun kuma yi kira da a sami hadin kai, suka kuma bukaci masu kada gangar rarraba da su guji hakan.

Sai dai, a tsage gaskiya irin na shi, Eleko na Legas, Oba Rilwan Akiolu, ya dan tayar da kura, inda ya kwatanta tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, da cewa, shi ne matsalar Nijeriya.

Basaraken, wanda ya sake kawo rikicin da aka yi ta yi a tsakanin gwamnonin jam’iyyar AD da Obasanjo din, wanda a lokacin yake neman zango na biyu a karkashin tutar jam’iyyar PDP, ya ce, ya gargadi Tinubu da kar ya kuskura ya hada kai da tsohonn Sojan ko ta wace hanya.

“Na ba Tinubu shawara da kada ya hada kai da Obasanjo sam. Na ce, kar ka taba baiwa Soja amanna. Babbar matsalar da muke da ita a Nijeriya, ita ce Obasanjo,”

Ba mu dai iya samun tsohon shugaban kasan ba, ballantana mu ji ta bakinsa tun a jiya din.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: