Connect with us

LABARAI

Shugabannin APC Sun Nemi A Taya Buhari Da Addu’a

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Galadima, ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da sauran ‘yan Nijeriya da su taya shugaban kasa Muhammadu Buhari da addu’a da sauran shugabanni domin samun nasarar mulkinsu.

Galadima ya yi wannan kiran ne a jiya Talata a garin Lafia a wani zama da ya gudana a tsakanin jagororin jam’iyyar na APC na yankin, inda suka tabbatar da cewa; ba da goyon baya ne da addu’o’i ne kawai zai sanya shugaban kasar ya kai ga nasara. Ya ce; akwai bukatar mabiya addinan Musulunci da na Kiristanci na jihar da ma Nijeriya baki daya da su dage da addu’a domin taimakon shugaban kasar don ya dauki kasarnan zuwa mataki na gaba da zai zamar mana da ci gaba.

A cewarsa kowanne shugaba a kowanne mataki yana da bukatar goyon bayan al’ummarsa da addu’o’i domin cimma nasara.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: