Connect with us

LABARAI

Yadda Ta Rincabe Tsakanin ’Yan Sandan Najeriya Da ’Yan Shi’a A Abuja

Published

on

·Mun Cafke ‘Yan Shi’a 40, In Ji ‘Yan Sanda

·Sama Da Mutum Dari 100 Suka Kame Mana, In ji ‘Yan Shi’a

A jiya Talata ne ta sake rincabewa a tsakanin jami’an tsaro na rundunar ’yan sandan Najeriya da ‘yan uwa Musulami wadanda a ka fi saninsu da ‘Yan Shi’a a babban birnin tarayya Abuja, lamarin ya auku ne a yayin da su mabiya Shaikh Ibrahem Zakzaky su ke cigaba da zanga-zangar neman a sako mu su shugabansu da ya shafe sama da shekaru uku a tsare.

An samu aukuwar artabun da ya ci rayukan da jikkata mutane da dama ne a daidai kofar shiga majalisar kasa, lamarin da ya tursasa majalisar dage zamanta na jiyan zuwa rana ta gaba ba tare da shirin yin hakan ba.

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta shaida cewar a sakamakon hana ’Yan Shi’ar kutsa kai cikin majalisar kasa, sun harbi jami’an ’yan sanda guda biyu a kafa da jikkata wasu shida, inda su ka yi amfani da duwatsu wajen jifan jami’ansu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan a Abuja, DSP Anjuguri Manzah, a cikin wata kwafin sanarwar manema labarai da ya rabar, ya shaida cewar an samu matsalar ne a lokacin da masu zanga-zangar su ka yi yunkurin shiga cikin majalisar kasa, inda su kuma su ka hana su shiga.

Ya tabbatar da cewar an harbi jami’ansu biyu, sai dai babu bayanin kashe jami’an tsaro daga bangarensu.

A bisa haka ne, Manzah ya tabbatar da cewar sun cafke mabiya Shi’a guda 40 da su ka shiga zanga-zangar da ta janyo tashin hankali ga bangarorin biyu.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da mambar sashen dalibai na mabiya El-Zakzaky, Abdullahi Muhammad Musa ya fitar, ya shaida cewar, “jami’an tsaro sun yi amfani da harsasai masu rai su na bude wuta a kan mabiya Shaikh Zakzaky, sun kashe ma na mutane biyu masu suna Mahmud Umar Sakafa da kuma Ja’afa Mika’il.”

Musa a cikin sanarwar ya tabbatar da cewar ba za su taba daina kiran gwamnati ta saki jagoransu ba.

“Abun da mu ke fada a yanzu shi ne a bai wa malaminmu damar ganin likita domin jikinsa ya tsananta,” a cewar sanarwar.

A gefe guda kuwa, daya daga cikin ‘yan Shi’ar, Muhammad Ibrahim Gamawa, ya shaida cewar babu wani jami’in tsaron da su ka harba, ya shaida cewar karya jami’an tsaro su ka sharara mu su harbi, domin kautar da hankalin duniya daga tsananin rashin lafiyar da shugaban nasu ke fama da shi a inda ya ke tsare.

Ibrahim Gamawa ya ce ba su taba daukar makami ba tunda abin ya faru a Zariya. “Kawai mu na ganin wannan batun sun kawo ne kawai domin kautar da hankalin jama’a daga koke-koken da mu ke yi na cewa rayuwar Malam Zakzaky ta na cikin gayar hatsari. Don haka ne a ke neman kawo abu na daban, don kautar da hankalin al’umma zuwa wani abin daban. Abinda mu ke so shi ne a kai shi asibiti lami lafiya tun kafin abubuwa su lalace,” in ji shi.

Dangane da zargin sun harbi ‘yan sanda kuwa, ya ce, “Me ya sa sama da shekaru uku da ci ma na mutunci da kashe-kashen da a ka ma na da rushe-rushen da a ka yi ma na ba su sanya mun fito da makami ba sai yanzu? Wannan kawai tsarinsu ne su ka bayyana.”

Ya ce a kowani lokaci su na daukar matakai na hankali wajen kiran gwamnati ta sako mu su shugabansu. “Da’awar malaminmu da’awace ta hankali da basira, mun sha gaya mu su cewar duk wanda suka ganshi da malami tabbas ba daga cikinmu ya ke ba. Idan kuwa da za mu dauki bindiga ai ba bindiga guda daya za mu dauka ba, wannan dai kawai kokari na kawar da hankalin mutane daga tsananin yanayin da Malaminmu ke ciki,” a cewarshi.

Da ya ke bayyana dalilinsu na zuwa majalisar kasa a jiyan, Gamawa ya shaida cewar sun saba zuwa domin shigar da kokensu kamar yadda kowani dan kasa ke da ‘yancin yin hakan, ya na mai cewa, “a satin da ya gabata mun je majalisar; Hon. Ado Doguwa ya fito ya shaida ma na cewar a bayar da lambobin waya zai je ya yi magana a kan halin da jagoranmu ya ke ciki Shaikh Ibrahim Zakzaky. Ya ce ma na kila kafin mu isa ma zai kira ya shaida ma na yadda a ke ciki.

“Har zuwa yanzu bai kira ba. Don haka ne mu ka je majalisa domin mu yi tuni mu kuma ji dalilin da ya sanya bai kira ba, alhali ya yi alkawari.”

Da ya ke bayyana halin da su ka tsinci kansu a ciki kuwa, Ibrahim Gamawa ya shaida cewar jami’an tsaro sun kashe mu su ‘yan uwa biyu da jikkata sama da sha biyu gami da kame mafiya yawa daga cikinsu.

“Jami’an tsaro sun kashe ma na ‘yan uwa biyu da jikkata ma na ‘yan uwa da daman gaske hadi da kame sama da ‘yan uwanmu mutum dari,” a fadinshi.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya ya shaida cewar majalisar kasa dai ta dage zamanta na jiha Talata zuwa ranar Lababa ba tare da shirin yin hakan ba, inda Kakakin majalisar wakilai ta kasa Femi Gbajabiamila ya shaida cewar daukar matakin ya biyo bayan dalilan tsaro ne.

Kudirin dage zaman majalisar dai ya samu ne daga dan majalisar da ke wakiltar Kano, Ado Doguwa, wanda ya samu mara baya daga shugaban marasa rinjaye na majalisar Ndudi Elumelu da ke (PDP dada Delta).

‘Yan Shi’an dai sun mamaye majalisar kasar a daidai lokacin da ‘yan majalisun ke gudanar da zamansu a ranar Talatar.

LEADERSHIP A YAU ta shaida ce wasu wadanda abun ya faru a kan idonsu sun shaida cewar an kona motoci a harabar majalisar sai dai babu wani bangaren da aka daura wa alhakin hakan kawo yanzu.

Bayan hakan ne dai an kulle dukkanin wata mashiga da mafitar cikin majalisar a daidai lokacin da hatsaniyar ta yi kamari.

Su dai ‘yan Shi’ar sun jima suna gudanar da jerin gwano na kullum rana a cikin Abuja suna masu neman cewar dole ne gwamnati ta sake musu shugabansu Ibrahim Zakzaky da matarsa Zenatuddin tun da bayan rikicin da aka samu a shekarar 2015 da ya haifar da kashe rayuka da lalata muhallai da dama a birnin Zariya.

Wakilinmu ya shaido cewar ba wannan karon ba ne dai ake samun irin wannan matsalar, an sha samun matsala a yayin da masu zanga-zangar suka kekeshe kasa suka ce tilas ne a sako musu shugabansu.

A dai ‘yan kwanakin nan masu zanga-zangar sun sauya salon zanga-zangarsu da yawaita rubuce-rubucen neman a sake musu shugabansu da furta kalamai ga shugaban kasa biyo bayan abun da suka ce jikin jagoransu na tsananta.

Wani manazarcin yau da kullum Alhaji Yahaya Ibrahim Abuja, ya shaida cewar da bukatar gwamnati ta duba lamarin da idon basira domin kauce wa rikicin da za a gagara shawo kansa, “Yan shi’a suna da yawa sosai a kasar nan, amma kullum suna zuwa nan Abuja su yi zanga-zangarsu; to ya dace gwamnati ta zauna da mutanen nan a sasanta domin wannan fa abun na zuwa matukar kurewa, ana kara tunzura su mu kuma muna ganin abun kamar wasa, fatanmu gwamnati ta duba batun da ido biyu,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: