Connect with us

LABARAI

Zulum Zai Yi Kokari Fiye Da Ni, Cewar Tsohon Gwamnan Borno Shettima

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, magajinshi, Farfesa Babagana Umara Zulum, zai yi kokari sosai a matsayinsa na gwamnan jihar fiye da yadda shi kansa ya yi lokacin da ya ke rike da kujerar gwamnan jihar.

Sanata Shettima, wanda ke wakiltar tsakiyar Borno a zauren majalisar dattijan Nijeriya, ya bayyana cewa, shi bai yi mamaki dangane da kokarin da Zulum ke yi ba a daidai lokacin da ya ke cika kwanaki 35 da shiga ofis a matsayin gwamnan jihar Borno.

“Mutane su na mamaki, amma ko kadan ni ban yi mamakin namijin kokarin da Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi ba a cikin kwanaki 35 a matsayin gwamnan jihar Borno ba,” in ji Shettima.

Ya cigaba da cewa, “kuma na karanta bayanan yabon da jama’a da dama ke yi tare da lura da na yi da yadda wasu su ka cika da mamakin hazikancin Gwamna Zulum a cikin wadannan kwanaki 35 kadai.

“Haka kuma, wasu na mamakin yadda a cikin awani 24 Gwamnan ya kira taro da jami’an tsaro, ya gana da ’yan sintirin ‘Cibilian JTF’ da maharba tare da kara mu su kudaden alawus dinsu da kara yawan motocin aiki, kana da gudanar da taron musamman na ido-da-ido tsakaninsa da Shugaban kasa Buhari kan sha’anin tsaro a jihar Borno.”

Har wala yau kuma, ya kara da cewa, wasu mutane kuma su na mamaki kan yadda a cikin kwanaki 35, Gwamna Zulum ya ziyarci majalisun kananan hukumomi 20 a cikin 27 da a ke da su a jihar Borno, inda matsalar tsaro ta yi kamari, domin duba yanayin makarantu, asibitoci, hanyoyin mota, ruwan sha da sauran, don daukar matakan da su ka dace.

“Sannan kuma abinda ya jawo wasu jama’a ke mamakin Farfesa Babagana Zulum, shi ne ba su san hazikancinsa ba ne. Na dauki tsawon shekaru Ina lura da yadda ya ke tafiyar da lamuransa, kuma Ina da tabbaci in sha Allah, zai yi hobbasa wajen bunkasa jihar Borno fiye da kowane lokaci, kuma wannan shi ne babban muradina.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: