Connect with us

KIWON LAFIYA

A Afirka Nijeriya Ce Ta Farko A Matsalolin TB A Afrika Kuma Ta Shida A Duniya

Published

on

Kasar Nijeriya tana da yawan matsalolin TB A Afirka kuma ita ce ta shida shida a duniya, mataimakin darekta na tsarin kulawa da cutar Tarin fuka da kuma Kuturta ta kasa, Ahmad Muhammad shine wanda ya bayyana hakan.

Ya cigaba da bayanin cewar kasar Nijeriya tana daga cikin kasashen duniya bakwai wadanda suke cikin fuskantar kashi 64 na matsalolin Tarin fuka (TB) a duniya.

Da yake ganawa da manema labarai kafin a kai ga yin taron shekarar 2019, a Abuja ranar Talata. Mista Muhammad ya bayyana har yanzu ita cutar babbar matsala ce a duniya, wadda kuma hakan ba zai sa Nijeriya ta kasance kamar saniyar ware ba.

Shi dai taron na kasa akan cutar Tarin fuka na wannan shekara mai taken ‘Samar da wani babban hadin kai da kuma fahimtar juna saboda a kawo karshen Tarinfuka a Nijeriya, za ayi shine tsakanin ranakun 17 da kuma 18 ga watan Yuli na shekarar 2019.

Da yake shine wanda ya jagoranci babban jami’i kuma Shugaban cibiyar na kasar NTBLCP, Adebola Lawanson, Mista Muhammad ya bayyana cewar kasashen bakwai sune wadanda suke fuskantar matsalolin cutar kashi 64 a duniya gaba daya. Yayin da ita kuma kasar Indiya wadda kuma kamar ita ce jagora akan hakan, sauran kasashe da suka hada da Indonesiya, China, Philippines, Pakistan, Nijeriya da kuma Afirka ta Kudu suke   bin ta a baya.

“Kasar Nijeriya ita ce kasa ta farko a nahiyar Afirka wadda take fusknatar babbar matsala dangane da ita cutar ta Tarinfuka, ta kuma kasance kasa ta shida a duniya.  Gaba daya kasashen Nijeriya da kuma Indiya sune samar da kashi 48, mace – macen da ake yi sanadiyar cutar Tarinfuka a duniya, wannan kuma ya kasance daga  cikn wadanda basu dauke da cutar ta Kanjamau, sai kuma kashi 43 na yawan mace – macen  da aka yi a sanadiyar Tarin fuka, wannan kuma sai an samu Tarawa ko kuma hadawa nag aba dayan wadanda suka mutu a dalilin ko dai suna dauke da cutar ta Kanjamau ko kuma basu dauke da ita kamar dai yadda ya jaddada.

Ya kuma bayyana cewar ita cibiyar ko kuma Hukumar ta NTBLCP, tare da hadin gwiwar Hukumar lafiya ta duniya (WHO), da kuma wata kungiya ta kasar Amurka USAID, sai kuma wata gidauniya ta duniya (Global Fund) da kuma sauran kungiyoyi masu zaman kansu, saboda a kawo karshen shi Tarin na Fuka a kasar Nijeriya.

Mista Muhammad ya kara bayar da haske inda ya bayyana cewar shi taron na kasa, kamar wata dama ce, koma dai ace wata dama ce wadda za a samu yin wani hadi na mutane daban -daban, a al’amarin daya shafi shi Tarin fuka, za asamu wata dama ce, inda kowa zai bayar da tashi shawarar hanyoyin da za abi, wadanda kuma suna iya hadawa da wasu sababbin abubuwan karin cigaba, akan yadda za a samu damar kawo karshen matsalolin da ita cutar take samarwa.

Shima a tashi gudunmawar shugaban ita cibiyar ko kum na kokarin da ake yi, na a tsayar da yaduwar cutar Tarinfuka da kuma kawo karshenta, a kasar Nijeriya Lobett Lawson, ya bayyna cewar da akwai dalar Amurka kusan miliyan $312, wato su kudaden da za a kara, saboda a samu wata dama ta cimma kawo karshen ita cutar ta TB nan da shekara ta 2030.

Mista Lawson ya bayyana cewar da akwai bukatar akan ita gwamnati ta kara yawan kudaden da take ware ma shi koi ta cutar Tarinfuka, da kashi 76, wannan kuma sai idan Nijeriya har tana son, ta kawo karshen ita cutar nan da shekara ta 2030.

Ya kara nuna rashin jin dadin shi akan su kudaden da ake samu daga hannun gwamnati, da kuma masu taimakawa na kasa da kasa, kashi 24 ne kawai, inda kuma ake barin kashi 76 na sauran kudaden da ake bukata, ba tare da samun su ba.

Mr. Lawson ya kara jaddada cewar idan har ana bukatar cutar tarin fuka ta kasance tarihi, da akwai bukatar a samu damar yin amfani da wasu abubwan da aka san za su iya taimakawa, wajensamun karin taimakon kudade, musammaan daga kamfanoni da kuma sauran mutane masu arziki.

“Tarinfuka a halin da ake ciki yanzun shine ciwo wanda kuma yake samar da babbar matsala, wadda ta shafi lafiyar al’umma, yayin da kuma wasu sababbin nau’oin ita cutar da suka kai miliyan 8 zuwa 10, wadanda kuma suka kai kashi daya bisa uku na yawan al’ummar Nijeriya, abinda kuma ya kai kusan kashi 95 a kasashe masu tasowa.

“Idan kuma aka yi la’akari da yadda ita cutar ta Tarinfuka ta ja baya da kjusan kashi 1.5, abin a hankali ne zai iya karuwa, zuwa kusan kashi 10 a duniya na da zuwa shekara ta 2025, wannan kuma saboda a samu cimma shi burin gaci na kawo karshen ita cutar nan da shekara 2030.

“ Abinda muke bukatar yi ko kuma daukar mataki akan shi shine, al’amarin daya shafi rashin ingantaccen abinci na yara, wanda yake gina jiki, tunda dai yake kasar Nijeriya tana daga cikin kasashen da suke da babbar matsalar data shafi rashin ingantaccen abinci wanda yake gina jiki na kananan yara a nahiyar Afirka. Inda kuma Arewacin Nijeriya ne yake daukar babban kaso na shi al’amarin.

“Mun yi kokarin muga cewar yadda za ayi amfani da kudade da kuma ilimi akan shi al’amarin daya shafi harkar abinci, saboda mu dauki wani mataki akan shi al’amarin wajen taiamaka wa mata, sai mukla dauki wanda ya dace, wato abinda ya kamata aci da kuma lokacin da za aci shi, ta wannan hanya ce suka samu suna cin abinci wanda yake da nagarta.

“Zuwa yanzu dai an samu dama ta tuntubar mutane 93,000 tare da matan da suke daga Jigawa da kuma Zamfara, a kananan Hukumomi biyar inda ake basu Naira 4, 000, ko wanne wata, saboda a taimaka masu domin a taimaka masu su fice daga fatara.

“Mun kashe Naira biliyan 11 inda kuma Jarirai 85,000 da aka haifa suka amfana daga shi tsarin, a nan ma an samu kai wa da kuma haduwa da masu gidaje 630,105 kamar dai yadda ta bayyana.”

Ms Buda’r-Aliyu ta bayyana cewar shi tsarin ya samu cimma buri da dama, saboda an samu rage cutar kananan yara, a su wuraren. An kuma samu canji daga wurin mata, wanda abin kamar yadda ta ce yanzu an samu karuwar sosai, saboda ana zuwa wajen yin gwajin Ciki ko kuma Juna Biyu.

Shugaban tawaga kuma babban jami’i wanda yake bayar da shawara akan al’umuran da suka shafi cigaban zamantakewa da kuma shiga al’amari wajen samar da maslaha idan tashin hankali ya samu na UKaid, Aled Stebens, ya bayyana cewar shi sashen na cigaban kasa da kasa ko kuma  (DFID) yana farincikin kasancewa daga cikin shi tsarin.

Mista Stebens ya bayyana cewar shi tsarin wata dama ce wadda zata a koya da kuma yin maganin matsalolin da suka fi cima Nijeriya Tuwo a Kwarya.

Ya kuma jaddada cewar ana wani nazari akan shi tsarin, saboda kuwa a halin yanzu da akwai wasu gidaje da basu fama da matsalar rashin tsaro akan abinci, bugu da kari kuma suna da masaniya akan al’amarin daya shafi ilimin abinci, don haka ana iya gani nan take an samu cigaba da kuma raguwar matsalar da take shafar girman yara ko kuma Jarirai.

Ya bayyana cewar ita kungiyar tasu tana fattar samu dama da kuma yin aiki da wasu jihohi biyu, wato Kaduna da kuma Kano, bugu da kari kuma suna shirin bayar da nasu taimako akan tsari da kuma bayar da taimako na kariya ma kasar Nijeriya.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna jin dadin su lokacin da suka samu ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, inda suka nuna jin dadinsu akan shi tsarin da aka kawo masu, da kuma shi.

Jara Iliyasu wadda take daga Jigawa ta bayyana cewar tana amfani ne da 4, 000 wajen koyon dinki da kuma sayar da shinkafa.

Hakanan ma wadda ta amfana da shi tsarin daga jihar Zamfara wadad ake kira da suna Binta Suleiman, ta bayyana cewar tana da ‘ya’ya bakwai, amma kuma uku sun mutu, saboda bata san yadda zata kula dasu ba ta bangaren abincin daya kamata.

Mrs Suleiman ta dauki alkawarin cewar ita ma zata koya ma’ya’yanta irin abubuwan data koya idan ta koma gida.

Zainab Saminu wadda iat ma daga jihar Zamfara take ta nuna jin dadin ta, saboda kamar yadda ta ce an koya mata, ilimi akan lokacin daya kamata da kuma abinda yakamata a daba wadda kuma zai kasance cikin tsafta, hakan zai sa yara suma su kasance masu nagarta da kuma koshin lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: