Connect with us

JAKAR MAGORI

An Gurfanar Da Soja A Gaban Kotu Bisa Laifin Satar Naira 93,000

Published

on

A ranar Laraba ce, a ka gurfanar da wani soja mai suna Samuel Hassan dan shekara 37 da haifuwa, a gaban kotun garin Jos, bisa tuhumar sa laifin satar kudi har naira 93,000, daga asusun makwabcinsa. Alkali mai shari’a Roseline Baraje, ta samu Hassan da laifin da a ke tuhumar sa da shi na tada hankalin al’umma, cuta, sata da kuma almubazzaranci.  Baraje ta bai wa wanda a ke tuhuma zabe a kan ya biya tarar kudi na naira 40,000. Sannan kuma ta umurci wanda a ke tuhuma da ya mayar wa mai dukiya kudinsa na naira 93,000. Baraje bayyana cewa, hukuncin zai zama darasi ga duk wadanda a ke aikata irin wannan laifi.

Tun da farko dai, lauya mai gabatar da kara, Monday Dabit, ya bayya wa kotu cewa, an kai rahotun lamarin ne ga ofishin ‘yan sandar Angwan Mission Tundunwada da ke garin Jos, ta hannun Misis Helen Geoffry. Dabit ya kara da cewa, wanda ta kai korafi da yarda da wanda a ke tuhuma, inda ta ba shi katin cire kudita a cikin watan Mayu, ya yi amfani da wannan dama, sannan ya cire mata kudi daga cikin asusunta har naira 93,000, ba tare da sanin ta ba.  Ya ce, lokacin da ‘yan sanda su ka gudanar da bincike, sun gano katin cire kudn daga hannun wanda a ke tuhuma. Ya cigaba da cewa, wannan laifin dai ya saba wa sashe na 297, 307, 272 da kuma 294 na dokar fanal kot.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: