Connect with us

RIGAR 'YANCI

Badaru Ya Umarci Sarakuna Su Bai Wa ’Yan Hidimar Kasa Filin Noma A Jigawa

Published

on

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya umarci sarakuna da shugabannin kananan hukumomi da shugabannin al’umma da su tallafa wa masu yiwa kasa hidima da fili, domin gina lambun noma a wuraren da su ke aikin yiwa kasa hidima.

Gwamnan ya bada wannan umarni a wajen bikin yaye masu yiwa kasa hidima kashi na biyu na wannan shekara da su ka kammala karbar horo a sansanin masu yiwa kasa hidima da ke Fanisau.

Ya ce, jihar Jigawa tana da kasar noma da kiwo dan haka akwai bukatar su sanya shaawarsu wajen yin noma domin marawa kudirin gwamnati baya na yaki da yunwa da kuma rashin ayyukan yi.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini ya yabawa mahukuntan masu yiwa kasa hidima bisa yadda su ke kula da masu yiwa kasa hidima

Daga nan sai ya bayyana mutanen jihar Jigawa a matsayin masu karbar baki tare da yin kira ga masu yiwa kasa hidimar su yi kyakkyawan muamula da alumomin da suka tarar

A jawabinsa babban jamiin hukumar masu yiwa kasa hidima ta jiha Alhaji Ibrahim Abdul Muhammad yace masu yiwa kasa hidima 2,059 ne su ka kammala karbar horo na makonni uku kuma aka tura su wuraren da za su yi aikin yiwa kasa hidima na shekara guda’

Ya yabawa Gwamna Badaru Abubakar bisa yadda yake tallafawa ayyukan hukumar a kowane lokaci, inda ya hori masu yiwa kasa hidimar da su yi amfani da abubuwan da su ka koya a wuraren da aka tura su aiki tare da yin mu’amula da mutanen da su ka tarar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: