Connect with us

WASANNI

Bellerin Zai Dawo Buga Wasa A Watan Satumba

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Hector Bellerin zai dawo buga wasa daga doguwar jinyar da yayi wadda ta zaunar dashi tun daga farkon watan Janairun wannan shekarar da ake ciki.

Bellerin dai yaji ciwo ne a wasan da Arsenal ta buga da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea inda suka tashi Chelsea ta samu nasara daci 2-0 a ranar 19 ga watan Janairun daya gabata kuma anyi masa aikine a wani asibiti dake kasar Sipaniya.

Duk da cewa ciwon yanada hatsari kuma hakanne ma yasa akayi zaton bazai warke ba sai tsakiyar watan Okoba amma wasu rahotanni sun tabbatar da cewa yana samun sauki sosai kuma zai iya dawowa buga wasa a watan Satumba.

Kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana, Hector Bellerin yana fatan warkewa kuma ya fara buga wasa a ranar 22 ga watan Satumba, a ranar da kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa zata kai ziyara filin wasa na Emirates a gasar firimiyar bana.

Shima dan wasa Rob Holding wanda yaji dogon ciwo a wasan da Arsenal din ta buga da Manchester United a watan Disamba shima ana fatan zai dawo cigaba da daukar horo a karshen wanann watan da ake ciki.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai ta sauka a kasar Amurka domin fafata wasannin sada zumunta inda zata buga wasanni da kungiyoyin Bayern Munchen da Real Madrid da Fiorantina da kuma kungiyar kwallon kafa ta Colorado Rapids duka acikin wannan watan.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: