Connect with us

LABARAI

Duk Dan Sandan Da Ke Karbar Kudin Beli Kidnafa Ne – Kwamishinan ’Yan Sandan Legas

Published

on

A ranar Talata ce, Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas, Mista Zubairu Mu’azu, ya kaddamar da wani dakin tattara bayanai a sashen ‘yan sanda na CID da ke Panti, Yaba, inda ya yi gargadin cewa, duk dan sandan da yake karban kudi a hannun mutane kafin ya bayar da beli, ba shi da wata maraba da kidnafa (Masu garkuwa da mutane domin karban kudin fansa),  hukuma kuma ba za ta kyale shi ba matukar ya shiga hannu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya kawo rahoton da ke cewa, karban kudi kafin a bayar da belin, doka ta haramta hakan.

A wajen kaddamarwar na ranar Talatan, Kwamishinan ya yabawa kamfanin RoLAC for the initiatibe, ya yi nuni da cewa, tattara bayanai yana da matukar mahimmanci a binciken da ‘yan sanda suke yi.

Kwamishinan ya ce, tattara bayanai tushe ne na binciken ‘yan sanda.

Ya ce, na’urar tana da mahimmanci sosai a kan aikin ‘yan sandan, ya kuma baiwa ofishin jakadancin na Ingila tabbacin rundunar za ta yi amfani da kyautar da aka yi mata yanda ya dace.

Kwamishinan ‘yan sandan na Legas, ya gargadi jami’an rundunar na shi a kan su guji duk wani aikin da ya shafi karban cin hanci da rashawa, yana mai cewa duk wanda aka kama za a hukunta shi ba sani, ba sabo.

Ya kuma kara nanata janyo hankalinsu da su guji karban kudi kafin su bayar da beli.

“Mun sha nanata cewa, Beli kyauta ne, kuma hakan abin yake, ina ta kara nanata fadin duk dan sandan da ya karbi kudi da sunan bayar da beli ba shi da bambanci da kidnafa. Bambancin su kadai shi ne, kai kowa ma ya san inda ka boye wanda ka sacen.

Kwamishinan ya yabawa DCP Yetunde Longe, mai kula da sashen na CID  a kan namijin kokarinsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: